Ga ta nan ga ta nan ku.
Wata barewa ce, sai ta rikiɗa, ta zama mace kyakkyawa. Sai ta ɗauki ɗan kwatashinta ta ɗora a ka ta tafi tsakiyar karofi ta ajiye.
Da ta ajiye, sai ta ce duk wanda ya jefa ‘yar tsakuwa ta buɗe kwatashin nan, shi ne mijinta. Sai wannan ya ɗauki tsakuwa ya jefa bai buɗe ba, wancan ya jefa tsakuwa bai buɗe ba.
Sai aka sami wani ya jefa ‘yar tsakuwa, Ya buɗe, sai ta ce ta sami miji, shi za ta aura.
Suka tafi garin ita yarinyar, wurin iyayenta za a ɗaura mata aure da wannan mutumin.
Sannan aka ɗaura musu aure ta zo ta tare gidan mijin. Kullum ranar girkinta sai a ce ta je ta ciro kuɓewa a gonar mijin ta yi miya.
Da ta je gonar sai ta yar da zanenta ta yi birgima a ƙasa ta zama barewa ta yi kiran ‘yan uwanta, ta yi waƙa ta ce:
Cinkalkal, cinkalkal kalaya,
Turmin ‘yan kale ya yi fure, ceɗiya.
Tudu na korar tudu, Marina.
Tudu na korar tudu da ƙaho.
Ban da ƙanƙan.
Sai ‘yan uwanta su zo su taru su ciccinye kuɓewa. Sa’annan in sun gama sai sun tafi gida.
Ita kuma sai ta yi birgima ta komo mutum ta ɗauki zanenta ta ɗaura. Sai ta koma gida ta dinga cewa; ‘Ni da gangan aka tura ni. Ga shi nan ban samo komai ba.’
To, ran nan sai mijinta ya bi ta gonar. Sai ya gan ta tana birgimar, sai ya ga ta rikiɗe ta zama barewa. Sai ya ga ta yi kiran ‘yan uwanta bareyi da waƙa. Bareyi suka taru a gonar jingim. Duk suka cinye kuɓewa. Suna cikin ci sai ya fasa su. Sai ya ga matarsa, ta gan shi.
Ya komo gida.
Sai ta ɗauko kuɓewar ta biyo shi. Ta tarar da shi a gida.
Ya ce, ‘Wace ce?’
Ta ce, ‘Ni ce’.
Ya ce, ‘Ina za ki?.
Ta ce, ‘Ɗaki za ni’.
Ya ce, ‘A a, koma daji’.
Sai ta ce ta ƙi. Sai ya biyo ta a guje ya kora ta daji.
Daga nan ba ta sake dawowa ba.
Shi ke nan. Ƙurunƙus.
Domin karanta Tatsuniyar Gizo da Giwa danna nan.
Edita; Rumasa’u M. Kallamu