Tatsuniyar Ɗankaɗafi

0
16

Ga ta nan ga ta nan ku.

Wata mata ce dai ba ta taɓa haihuwa ba, tun da ta ke. Sai ta ce, ‘Allah, ba ka ba ni ɗa ba, ka ba ni ko Ɗankaɗafi ne?’
Allah sai ya karɓi roƙonta, sai ta haifi ɗanta namiji.

Shi ke nan, yaro yana nan yana girma. Sai ran nan ta goya shi. Da ta gaji da goyo, sai ta ce da shi, ‘To, sauko ka kwanta Ɗan inna’.

Sai ya ce, ‘Mhm, mn, a baya’.
Ta kuma cewa, ‘Sauko a wanke maka ido.’
Ya ce, ‘Mhm, mn, a baya’.
Kome dai ta ce sai ya ce, ‘Mhm, mn, a baya’.

Sai ran nan ta ce, ‘Kai ni dai na gaji; Gun malami za ni ko yana da abin da zai yi mini in rabu da ɗan nan. Na gaji.’

Sai ta je wajen malami.
Malami ya ce, ‘Duk abin da aka gaya miki kya iya?’
Sai ta ce, ‘I, zan iya’.
Sannan ya ce, ‘To, sayo sa guda ki kawo mini’.
Sai ta sayo sa ta kai wa malami.
Sai ya ce, ‘biyu za a raba, ki ɗauki rabi, in ɗauki rabi’.

Ta ce, ‘To’,
Aka raba naman sa kashi biyu, Malami ya ɗauki rabi, ta ɗauki rabi.
Sai ya ce, ‘Ki soya wannan ki tafi da shi daji ki haɗa da majanyi da zane. in kin sauko yaron yana cin naman sai ki gudo ki baro shi can’.

Sai ta ce, ‘To’.

Taje gida ta soya nama. Sai ta tafi daji da shi. Ta ce, ‘Ɗan Inna, sauko ka ci nama’.
Sai ya ce, ‘Mn, a baya’.
Sai ta ce, ‘Ga naman naka nan sauko ka ci’.
Sai ya sauko. Da ya sauko yana cin naman, sai uwar ta waiga; ta waiga ba ta ga kowa ba; sai ta gudu ta bar shi da majanyi da zane.

Fatar bayanta har ta kwaye saboda goyo.
Shi ke nan sai ga kura, ita da ‘yan uwanta suna wasa. Sai ta ce, ‘Ɗan ƙanena, ɗan ƙanena, sam min ɗan naman in ci in goya ka.
Shi ke nan, ya ba ta.

Ta ɗauke shi ta goya shi suna wasa. Sai ta ce, ‘Sauko in huta’.
Sai ya ce, ‘Mn, a baya’.
Kome dai ta ce, sai ya ce, ‘Mn, a baya’.

Da ta yi ta yi ta cire shi daga bayanta ya ƙi; sai ta kira ‘yan uwanta su cire mata shi. Da suka zo garin cire shi sai fatar bayan kura ta ciro, ta ce, ‘Na gamu da jaraba’.
Sai suka gudu suka bar shi nan.

Can sai ga dodo ya zo ya ɗauke shi ya ɗora a bayan dokinsa, shi kuma yana gaba yana cewa:

Za ni za ni za ni,
Za ni za ni,
Za ni da namana,
Za ni da namana,
Za ni da kai sharɓa,
Ɗankaɗafi za ni da namana

Suna cikin tafiya a daji, sai Gizo ya ga dodo da yaro, sai ya sauke yaron, ya ajiye a ƙasa.
Shi kuma ya hau kan dokin dodo.
Dodo bai sani ba yana ta waƙa.

Shi ke nan sai ana ta tafiya da Gizo; sai kurciya ta ga Gizon a kan dokin dodo sun kusa da kogi, sai ta ce da Gizo; ‘Ku ne a yi muku rana, ku yi wa mutum dare.
Gizo ya ce, ‘A’a, ba zan miki ba’.

Shi ke nan, sai kurciya ta ɗauke Gizo a fiffikenta.
Da dodo ya je bakin kogi, sai ya waiga don ya ɗauko yaro ya cinye ya sha ruwa; sai ya ga ba kome. Baƙin ciki sai ya sa shi ya faɗa cikin ruwan nan, ya zama gawa.

Shi kuwa Ɗankaɗafi kura ta cinye shi a can dajin da aka ajiye shi.
Shi ke nan.

Ƙurunƙus.

Domin karanta Tatsuniyar Gizo Da Giwa danna nan.

Domin karanta Tatsuniyar Yarinya Da Dodanni danna nan.

Edita@rumasau-kallamu

labarin da ya wuceKiɗa Da Waƙoƙin Makaɗa Musa Ɗanƙwairo
Labarin na GabaYadda Falalar Zikiri Bayan Sallar Asuba Har Zuwa Ɓullowar Rana Ya Ke
wikiHausa
wikiHausa kundin ilimi (insakulofidiya) ce da ke ilimantar da jama'a yara da manya da maza da mata wajen samun ilimi a saukake, cikin harshen Hausa.