Addu’a Idan Mutum Zai Yi Tafiya

0
11

“Allaahu akbar, Allaahu akbar, Allaahu akbar, subhaanal lazii sakkara lanaa hazaa wama kunnaa lahu muƙriniina wa innaa ilaa rabbinaa lamunƙalibuuna, Allaahumma innaa nas’aluka fii safarinaa hazaa birra wat taƙ’waa, waminal amali maa tardhaa, Allaahumma antas saahibu fis safari, wal khaliifati fil ahli, Allaahumma innii a’uzu bika min wa’asaa’is safari, wa ka’aabatil manzari wa suu’il munƙalabi fil maali wal ahli”.

{Allah ne Mafi girma, Allah ne Mafi girma, Allah ne Mafi girma. Tsarki ya tabbata ga (Ubangiji) wanda ya hore mana wannan (abin hawa); ba mu kasance masu ikon sarrafa shi ba. Haƙiƙa mu masu komawa ne zuwa ga Ubangijinmu. Ya Allah! Muna roƙon ka nagarta da tsoron Allah a cikin wannan tafiya ta mu, da kuma aiki wanda kake yarda da shi. Ya Allah! Ka sauƙaƙe mana wannan tafiya ta mu, kuma ka naɗe mana nisanta. Ya Allah! Kai ne Ma’abocinmu a cikin wannan tafiya, kuma Halifanmu a cikin iyalanmu. Ya Allah! Ina neman tsari da kai daga wahalar tafiya, da abin gani mai sanya ɓacin rai, da kuma komawa mummuna ga iyali da dukiya}.

Idan ya dawo daga tafiyar tasa, sai ya faɗi wannan addu’a kuma ya ƙara da cewa:

“Aayibuuna taa’ibuuna aabiduuna li Rabbinaa haamiduuna”.

{Mu masu komowa ne, masu tuba, masu bauta, kuma masu godiya ne ga Ubangijinmu}.

Domin karanta cikakken bayani akan Yadda Ake Addu’ar Shiga Wata Karkara Ko Wani Gari danna nan.

Domin karanta cikakken bayani akan Sallar Kisfewar Rana Da Wata (Zazzaɓin Rana Da Wata) danna nan.

Edita; RMK

labarin da ya wuceCiwon Idon Jarirai
Labarin na GabaAddu’ar Tashi Daga Majalisi
wikiHausa
wikiHausa kundin ilimi (insakulofidiya) ce da ke ilimantar da jama'a yara da manya da maza da mata wajen samun ilimi a saukake, cikin harshen Hausa.