Ɗabi’ar Lokaci Saurin Wucewa
Ɗabi’ar lokaci ita ce saurin wucewa. Lokaci yana wucewa kamar walƙiya. Amman fa mutum ba ya ganewa, sai bayan ya riga ya wuce, ko kuma sanda ya zo mutuwa.
An ce mala’ikan mutuwa ya tambayi Annabi Nuhu (A.S) a lokaci da zai ɗau ransa “Ya Annabin da ya fi duk sauran Annabawa tsawon rai, ya ka sami duniya? Sai ya ce “kamar gida ne mai ƙofa biyu , na shiga ta ɗaya na fita ta ɗayar.
Idan Lokaci Ya Wuce Baya Dawowa:
Hasnul Basiri yana cewa, a kullum yini kan ce: “Ya kai ɗan Adam, ni sabuwar halitta ce, kuma mai yin sheda ce ga ayyukanka. Ka yi ƙoƙari ka ribace ni (ka yi amfani da ni) ba fa zan dawo ba har ranar ƙiyama”
Rashin Amfanar Lokaci Yana Gadar Da Ɓacin Rai Da Nadama:
Da yawa mutane da suka lalata kuruciyarsu da saɓon Allah Maɗaukaki suke nadama a lokacin da tsufa ya kama su. Babbar nadama kuwa sai ranar Alƙiyama in masu saɓo suka ga makomarsu.
Kowane Lokaci Na Da Aikinsa, Haka Kowane Aiki Na Da Lokacinsa:
Ya kamata musulmi ya san irin abubuwan da ake nema daga gare shi, a kowane minti ko awa ko safiya ko yammaci ko dare ko asubahi. Imma dai aikin zuciya ne ko na harshe ko gaɓɓoɓi. Don haka sai ya ƙirƙiri lokacin, ya yi ƙoƙarin cimma wannan aiki a lokacin. Wannan na nuna musulmi ba zai tattare ayyukan da yake so a lokacin da ya so ba, kamar yadda mai zuwa aiki masana’anta ko ofis ba zai je tsakar dare ba.
Koyarwar Annabi (Sallallahu alaihi wassallam) ta nuna mana kowane lokaci na da aikin da ya keɓance shi, kamar yadda Ubangiji Maɗaukaki ke cewa game da sallah “Lallai sallah ta kasance a kan mumini farilla mai kayyadajjen lokaci”. Nisa’i 103.
Game da aikin hajji kuwa Ubangiji Maɗaukaki na cewa: ‘Hajji watanni ne sanannu” suratul-Baqara-197.
Game da azumi Ubangiji Maɗaukaki na cewa: “To wanda ya halarta daga gare ku a watan, sai ya azumce shi”. Suratul-Baƙara-185.
Waɗannan ayoyi na nuna cewa kowanne aiki na da lokacinsa haka kowanne lokaci na da aikinsa.
Ya zama wajibi matasanmu da iyaye ko masu kula da yara su nusar da su amfanin yin aiki a lokacinsa. Kar ɗan firamare ya yi wasa da shekarunsa na karatu guda shida in kuwa ya yi wasa zai shiga shekaru ukun da ya kamata a ce yana ƙaramar sakandare. Yin sakaci da wannan lokaci zai iya zarcewa ya zuwa rayuwar karatunsa a jami’a da sauran lokutan rayuwa masu muhimmanci.
Kamar yadda in matashi ya yi sakaci da haddar Al-ƙur’ani a shekaru ashirin ɗin farko. To al’amarin zai wuyata a gare shi. Haka mai saɓo ba shi da damar tuba, matuƙar ya kai gangara domin ba lokacin da zai masa amfani ba ne. Wannan na nuna cewa nadama ko da-na-sani ba zata yi amfani a lahira ba. Domin komai da lokacinsa.
Wannan na nuna cewa mutum ba zai wata ibada ba face a lokacinta. Musulmi mai koyi da Annabi (Sallallahu alaihi wassallam) ya kan yi komai a bigirensa. Ya yi karatun Alƙur’ani ya yi istigifari ya sada zumunci. Idan lokacin jihadi ya yi, ya fita in an dawo ya wuce kasuwa. Idan lokacin sallah ya yi, zikiri ba zai maye gurbin sallah ba, sai an aiwatar da ita a lokacinta.
Ƙofofin tuba a buɗe suke, amma mutane sun kasa shiga, har sai an rufesu suna wasa da lokacin rayuwarsu, har sai tsufa ya kama su saboda rafkana. Rafkana ke sa mutum ya farka tsakar dare, amma ba zai iya tashi ya yi sallah ko da raka’a biyu ba. Rafkana ce ke jawo wa mutane su ci gaba da hira ana ta kiran sallah har sai lokaci ya yi nisa, ko ma ya wuce ba tare da sun yi sallar ba.
Kallon Bidiyo Da Talabijin Ko Tauraron Ɗan Adam
Babu shakka an jarrabi mafi yawan al’ummar musulmi da bala’in kallon fina-finai a bidiyo da talabijin. A inda mata da yara har masu gidaje ke cinye awowi don yin kallon fina-finai da shari’a ba ta yarda da su ba. Bincike ya nuna cewa hatta a ƙasashen Turai, an gano illoli ɗaruruwa waɗanda kallon ke haddasawa ga tarbiyar ‘ya’ya da sabbaba miyagun laifuka da yaɗuwarsu tsakanin al’umma. Baya ga irin lokacin da mutane ke asara a gaban akwatinan talabijin, suna ɗibgar zunubi ba tare da amfanar komai ba. Irin wancan bincike ya nuna cewa:
Fina-finai sama da 11000 ne ke nuna kisan kai ga ƙananan yara ƙasa da shekaru 15 a kowacce shekara a Amurka.
Domin karanta cikakken bayani a kan abubuwan da ke jawo asarar lokaci a rayuwar ɗan adam danna koren rubutun nan
Wannan bayanin an ciro shi ne daga littafin lokaci a rayuwar musulmi tsakanin riba da asara wanda Sunusi Iguda Ƙofar Nasarawa ya wallafa shi domin karanta cikakken wannan littafin danna wannan koren rubutun.