Da yake mun ga yadda ƙagaggun labaran Hausa na baka suka sauya fasali bayan haɗuwar Hausawa da baƙi, musamman Larabawa. A wannan ɓangaren kuma an kalli yadda waɗannan ƙagaggun labaran na gargajiya suka sauya fasali, suka koma a rubuce, ta yadda maimakon a kai da ake riƙe su, sai yanzu suka koma a rubuce, a zamanin zuwan Larabawa da Turawa.
Fasalin Ƙagaggun Labaran Hausa a Zamanin Larabawa
Ƙagaggun labaran Hausa sun sauya fasali ta wata hanyar daban bayan da Hausawa suka haɗu da Larabawa, ta inda a wannan karon aka mai da wasu daga cikin waɗannan ƙagaggun labaran a rubuce a maimakon a ka da suke adane. Daga binciken da aka yi an fahimci babu adabin gargajiyar Bahaushe da ake da shi a rubuce, sai lokacin da Hausawa suka haɗu da Larabawa, inda suka fara yin rubutun su cikin Ajami.
Masana da dama (dubi Magaji, 1982, Dokaji, 1978, Yahya, 1988, Gusau, 2008 da kuma Malumfashi, 2009) duk sun yarda da Musulunci ya shigo ƙasar Hausa da daɗewa, tun wajen ƙarni na goma sha ɗaya zuwa na goma sha uku. Su kuwa Magaji, 1982, da Abdullahi, 1997 sun ruwaito cewa, ‘a wajen ƙarni na 12 zuwa na goma sha uku, wato lokacin da sarkin Kano Naguji Ɗan Ɗariƙu (1194-1247) wasu Larabawa ‘yan kasuwa suka fara kawo Musulunci Kano.
Daga baya kuma zamanin sarkin Kano Aliyu Yaji (1349- 1385) wasu Wangarawa mutanen ƙasar Mali suka fara zuwa ƙasar Hausa don ƙarfafa addinin musulunci. Sun zo Kano tare da litattafan koyar da addinin Musulunci, kuma suka kafa makarantu da masallatai.
Tarihi ya nuna kafin zuwan addinin Musulunci ƙasar Hausa, Hausawa ba su da wata hanya tasu ta karatu ko rubutu. Adabin Hausa a lokacin na baka ne, ana kuma watsa shi ta baka, a kuma adana shi da kai. Saboda haka zuwan waɗannan malamai shi ne matakin farko na koyon karatu da rubutu a ƙasar Hausa.
To sai dai, duk da bayyanar waɗannan malaman da kuma samun cikakkiyar hanyar karatu da rubutu bayan watsuwar addinin Musulunci da kuma samar da sababbin masu ilmi cikin al`umma, wannan bai haifar da wani abun a-zo-a-gani ba game da samuwar adabin Hausa da ta shafi addinin Musulunci ba.
A wannan lokacin, duk faɗi-tashin da malamai da almajirai suka yi ta yi, ta tsaya ne a kan yadda mutane za su fahimci addinin Musulunci, da kuma yadda za su yi aiki da shi cikin al`amurransu na yau da kullum. Wannan ya sanya adabin Hausa bai samu wani canji ba, yana na dai a adane cikin ƙwaƙwalwar mutane, duk lokacin da ake buƙata sai a aiwatar da baki kuma a inda ya dace, kamar dai yadda Sulaiman, 2008 ya ruwaito daga Hisket (1975).
Sai daga baya ne malaman addini da sarakuna suka yi amfani da rubutun Ajami ƙwarai da gaske wajen aikawa da saƙonni zuwa ga ‘yan uwansu sarakuna da malamai. Malamai sun yi wallafe-wallafe da dama cikin ajami don watsa addinin Musulunci, wasu a tsarin waƙoƙi, wasu kuma maganganun azanci ne suka rubuce, wasu kuma fassara suka yi.
Wannan ya sanya yawa-yawan ayyukan adabin Hausawa, musamman waɗanda suka shafi ƙagaggun labarai na gargajiya da waɗanda aka tsinto daga Larabci suka shigo da sabuwar riga ta rubutun Ajami da Larabci ta yadda daga baya za ka ɗauka cewa tun can asali da wannan rigar aka haife su.
Wannan bayani an ciro shi ne daga rubutaccen kundi mai taken: ADABIN KASUWAR KANO: Nazari da Sharhi Game da Ƙagaggun Labaran Hausa (1984-2008) wanda Bashir Abu Sabe 07/211111002 (M.A Hausa Studies) USMANU ƊANFODIYO UNIVERSITY, SOKOTO, NIGERIA ya wallafa.
Domin karanta Gwamutsuwar Labaran Gargajiya Na Hausa Da Baƙin Al’adu danna nan
Edita@rumasau-kallamu