Ƙalubale Ga Makarantun Tsangaya

0
60

Kamar yadda tarihi ke maimaituwa kullum, cikin kowane al’amari mai kyau ba ka rasa baragurbi ko zare. Tsarin tsangaya ma bai tsira ba.

Tarihin musulunci da rayuwar sahabbai (Radiyallahu Anhuma) ya isa ishara, domin kuwa tun sahabbai (Radiyallahu Anhuma) ba su ƙare ba aka samu wasu mutane waɗanda ke da’awar Musulunci sun fito sun kishiyanci musulmi na ainahi. Irin waɗannan mutane sun haɗa da Khawarijawa da ‘yan Hururiyah da Murji’awa da Mu’utazilawa.

Aƙidun waɗannan mutane sun ci karo kai tsaye da aƙidun musulmi. Don haka dukkan musulmin da yake son ya wanzu cikin musulmin ƙwarai dole ya kauce wa aƙidu da ta’adun waɗannan mutane da muka ambata.

Makaranta cikin tsangaya su ma ba su kuɓuta daga irin waɗannan mutane da aƙidu ba. Da yawa mutane na kallon ma’abota tsangaya gaba ɗayansu a matsayin wani ɓangare na wani gungu na irin waɗansu jama’u da suka yi ƙaurin suna. Yin hakan rashin adalci ne ga nagartaccen tsarin mu na tsangaya.

Za mu ɗauki irin waɗannan gungu na makaranta masu waɗannan aƙidu domin mu ƙara nazari:-

1. ‘Yan Tatsine: Tatsine ko ‘yan Tatsine wasu mutane ne da ke da’awar su musulmi ne, masu karatun Alƙur’ani a yanayin irin na ma’abota tsangaya. ‘Yan tatsine sun samo asali ne ko sun ƙara fitowa fili a lokacin da wani mutum wai shi Muhammadu Marwa daga Marwa da ke ƙasar kamaru, ya tara gardawa masu neman karatun ƙur’ani ta hanyar sihiri da yaudara da yin da’awar annabtar ƙarya. Wanda daga ƙarshe ya haddasa rikicin da ya jawo asarar rayukan dubunnan mutane da dukiyoyi a birnin Kano.

Dukkan wanda ya rayu a birnin Kano ko a Najeriya ta Arewa a dai-dai wannan lokaci to kuwa ya san irin barazanar da Tatsine ta haifarwa al’ummar jihar Kano. Wannan al’amari ya jawo har yau ɗin nan akwai ɓurɓushin irin waɗannan ‘yan Tatsine masu aƙidun ƙin yarda da komai na Hadisi ko Tafsirin Musulunci daga bakin magabata, idan ba bisa irin fassarar son ransu ba.

In ba a manta ba gwamnatin wancan lokaci ta kafa wani kwamiti sakamakon wannan rikici na mai Tatsine a shekarar 1981 mai suna Kwamiti Kan Almajirai (Almajirai Committee 1987) ƙarƙashin jagorancin Malam Isa Waziri da Mambobi guda goma.

Ayyukan wannan kwamiti sun haɗa da:-

1. Duba yadda za a inganta tsarin karatun almajiranci duba ga abubuwan rashin daɗi da suka faru.
2. Nazari kan dokokin da za su kula da zirga-zirgar almajirai da shawarwarin yadda za a ɗabbaƙa su.
3. Aunawa da gano irin yadda tsarin almajirai ke haddasa gurɓatar ɗabi’un almajirai da sauransu.

Bayan kammala aikin wannan kwamiti, gwamnatin Guruf Kyaftin Muhammad Ndatsu Umaru ta fitar da matsayarta game da shawarar kwamitin wadda suka haɗa da:-

1. Yin doka kan zirga-zirgar almajirai.
2. Yi wa makarantun Alƙur’ani Rajista ta hanyar mai Unguwa ko Dagaci ko Hakimi.
3. Damar ƙwace izinin kafa makaranta ko zirga-zirgar malami da almajirai da sauransu.

Wannan ya sa mutane da yawa har zuwa yau ɗin nan suna kallon tsarin tsangaya a matsayin wani tsari da ke da haɗari kuma suna kallon almajirai da gardawa ko ma alarammominsu a matsayin masu alaƙa da tatsinanci.

2. ‘Yan Ƙala-Ƙato: Wannan wani reshe ne na tatsinanci wanda mafi yawan mabiyansa ma’abota tsangaya ne. ‘Yan ƙala-ƙato mutane ne masu son yin bayani game da ma’anonin Alƙur’ani; bisa son zuciya da rashin ilimin fannonin musulunci da harshen Larabci. Ma’abota tsangaya kan ruɗu da bin ‘yan ƙala ƙato da riƙe aƙidunsu saboda:-

i- Rashin neman ilmin fiƙihu da sanin ilmin harshen larabci wanda sai da shi ne za a iya fahimtar saƙon Ubangiji maɗaukaki bisa sahihiyar ma’ana sanin kowa ne makaranta a tsarin tsangaya a arewacin najeriya suna da tawaya ta rashin neman ilmi fannonii fiƙihu don gyaran Sallah da fahimtar sauran mas’aloli.

Da yawa za ka ga gardi wanda ya rubuta alƙur’ani bai san hukuncin ƙabil da ba’adi ba hakan takan sa; wasu makaranta na ganin idan mahaddaci ya shiga fagen neman ilmin karatunsa ba zai yi inganci ba. Wannan matsala game da makaranta a tsangayun arewacin Najeriya ta zama ruwan dare. Saɓanin tsangayu a ƙasahen Gambiya da Senegal da Mali da Sudan; waɗanda ke da ɓangare guda na ɗaukar ilimai da sauran fannoni kamar su; Ahlari da Ishimawi a Fiƙhu da Alfiyya da Kaɗarun Nada a Nahwu da Lamiyya a ilmin Sarfu da Jawahir a fannin Balaga.

Wannan ya taimaka da gaske wajen samun mahaddata masu wayewa da gogewa a ilmi daban-daban a irin waɗannan ƙasashe ta yadda ba za a iya yaudararsu ko a ruɗe su ba.

ii. Da yawan makaranta musamman gardawa sun fi nuna ƙwaɗayinsu; wajen neman laƙani da asiri don samun shuhura tsakanin abokan hamayya da kuma samun jama’a. Wannan ya sa duk wanda ke da wani abu irin wannan to kuwa za su sallama masa; kuma duk wanda zai yi musu tsawa a kan wannan ba kasafai suke samun jituwa da shi ba. Don haka da yawa suke son laƙani ko da kuwa zai kai su ga fita daga Musulunci.

3. ‘Yan Magaru: ‘Yan Magaru wasu mutane ne da ake danganta su da ma’abota tsangaya. ‘Yan magaru sun shahara da tsafi da surkulle. Su ma aƙidunsu abin ƙyama ne kuma ba adalci ba ne a danganta duk wani matsafi da AIƙur’ani ba ko da kuwa ya haddace shi ko ya rubuta shi. A lokaci guda kuma ba adalci ba ne yi wa ma’abota tsangaya dukkaninsu kallon irin waɗannan mutane.

Duba da irin manyan Gwanayen Alƙur’ani kuma gwaraza a fagen fannonin ilmi irin su Gwani Hamad da Shehu Rabi’u Ɗantinki da makamantansu. Waɗanda ke kwaɗaitar da mahaddata kan su tsunduma cikin fannonin ilmi. Babu shakka an yanke hanzarin duk wani ɗan tsangaya, sai dai in son zuciya ne ya halaka shi.

Matashiya

Akwai wata ta’ada da ta yi gurbi a zukatan ma’abota tsangaya masu yawa; irin wannan ta’ada shi ne rashin gwama karatu da sana’a ko kasuwanci. Da yawa ma wasu malamai kan ce “in ka ga mahaddaci na sana’a ai karatu bai albarka ba”. Don haka za ka ga mahaddata Alƙur’ani sun fi son su yi tsibbu.

A wasu lokutan ma’ana kyarar su a wajen sauke Alƙur’ani a gidajen masu kuɗi. A gaskiya idan da makarantanmu za su yi ƙoƙarin koyi da magabata; da ba a bar su kullum a raɓe a soraye ana yi musu kallon raini ba. Alhali Ubangiji Maɗaukaki Ya ba su abin da bai ba wa kowa ba.

Ya kamata a samu alarammomi Teloli da Kafintoci da Ma’auna da ‘Yan kasuwa da dai duk wata sana’a da ba za ta hana malam yin karatunsa ba. Labarin Malam Na Maiganji a Sashe Na Huɗu na wannan littafi ya ishe mu ishara.

Domin karanta cikakken bayani akan Hanyoyin Farfaɗo Da Tsangayun Alƙur’ani danna nan.

Domin karanta cikakken bayani akan Asalin Tsibbu A Tsangayun Alƙur’ani danna nan.

Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Tsarin Tsangayun Alƙur’ani A Arewacin Najeriya; Tarihin Su Da Zamantakewar Su Da Hanyoyin Raya Su; wanda Dr. Sunusi Iguda Ƙ/Nasarawa ya wallafa shi; domin karanta cikakken Littafin danna nan.

labarin da ya wuceRashin Kogon Al’aura Ga Mata (GYNAETRESIA)
Labarin na GabaAsalin Samuwar Goni