Zubar Jinin Haila Sosai Fiye Da Ƙima wato “Rushing” [Heavy Bleeding]

0
59

Kamar yadda in aka dafa dankali yake laushi tuɓus ta yadda ko yatsa kasa ka dirza ɓawonsa zaka ga ya saluɓe nan da nan,ko kuma saboda ma tsabar shan wuta zaka ga ya sassaluɓe ya fashe.

Toh ƙwatan-ƙwacin abinda ke faruwa kenan a cikin mahaifar ƴaƴa mata wato (uterus) a yayin haila,haka mayanin bangon mahaifarsu ke ɓamɓarowa tare da saluɓowa ya zubo kamar yadda maciji ke saɓa,wanda hakan ke haifar da fitar wannan jinin wanda ake kira jinin haila bayan salubowarsa.

Sannan hakan zai sa ku fahimci yadda period keda tsananin zafi, zogi da ciwo, domin in dankali yasha wuta ka daukesa a hannu kaima kasan me ka taɓa wajen azabar zafi,toh amma haka su mata jikinsu ke karɓar wannan zogin,shiyasa ba banza ba wasu ke murqususu,wasu ma basa iya mikewa sosai sak suyi tafiya saboda azaba yadda kowa agidan sai yasan lokacin hailar wance yayi,domin kowa da yanayin irin yadda jikinsa ke isar masa da saƙon zogi ko zafi.

Zanyi ƙarin haske ne akan zubar jini sosai fiye da ƙima dakan faru da wasu matan yayin haila.

A ƙa’idance bai kamata ace yayin haila mace ta fitar da jinin da yafi cikin sirinjin allura me lambar biyar (5ml syringe) ƙwaya 3 zuwa 4 ba a kullum. wato 15mls zuwa 20mls. Wannan normal ne.

Toh amma daga lokacin da jini ya zamto yana ƙwaranyowa wato rushing,wani lokacin harda duddunƙulallan jini wato clots toh da akwai damuwa.

Domin karanta bayani akan Vaginal Infection shiga nan

Alamomin Heavy Bleeding Yayin Haila

Ga alamomin dake nuna mace na zubar da jini fiye da Ƙima kuma akwai bukatar ɗaukar mataki domin babu lafiya:

  • Inya zamto duk bayan awa guda sai mace ta canza pad saboda jikewa da jini tsawon awoyin yini a jere.
  • Ko Pad daya kurum baiwa mace har sai ta haɗe pads biyu gu ɗaya sannan zata saka saboda yadda jinin ke ƙwaranyowa.
  • Ya zamto har da daddare sai kin tashi kin canza pads saboda jiƙa.
  • Jinin ya cigaba da zuba har fiye da sati guda.
  • Fitar da jini a duddunƙule manyan gudaji me yawa.
  • Jinin yasa bakya iya sakewa ki ayyukan yau da kullum saboda yadda yake fita.
  • Ko yawan kasala,nauyin munfashi kiji kamar iskar shaƙa na miki kaɗan saboda zubar jini.

Duk macen dake fuskantar alamomi bakwai ɗin can yayin haila to alamace dake nuna tana da HEAVY MENSTRUAL FLOW wanda ke bukatar aduba ai wani abu.

Wasu Daga Cikin Dalilan Dake Jawo Zubar Jinin Fiye Da Ƙima Sune:

Akwai lokacin da yakan zamto abu me wahala a iya gano dalilin da yasa mace ke zubar da jini sosai,toh amma akwai tarin ababen da binkice ya tabbatar suna jawo hakan.

(1) Rashin daidaiton sinadaran jima’i, girman nono,sha’awa,haila da goyon ciki wato ‘Istirojin da furojestaron”. Wanda a lafiyayyar haila ya dace ace wadannan sinadaran sunyi daidai da daidai wato 50/50 wanda hakan ne kesa a sami lafiyayyen mayanin mahaifa wato lining na uterus da kan kwaɓo yayin haila. Amma inya zamto babu daidai to musamman ace “Furojestaron” ya ɗara “Istirojin” wato ansami 70/30 ko 60/40 maimakon 50/50 toh hakan zaisa mayanin shimfidar cikin mahaifar a wannan wata tai kauri sosai,wanda kaurin nata shikesa saita dahu sosai kafin ta kwaɓo tabi jini ta fito,wanda hakan ke jawo aga jinin na fita fiye da ƙima domin da kyar jikin ya ɓamɓarota…. Hakan kan faru

Daga Cikin Abinda Ke Haddasa Rashin Wancan Daidai Ton Shine: 
  • Mace inta kasance me jiki ko ƙiba
  • Mace me ganin nononta na samar da ruwa duk da bata shayarwa koma kila budurwa ce
  • Mace me ‘PCOS’ wato yawan marurai jikin ƙwayayen haihuwa
  • Ciwon maƙoƙo,ciwon sugar,ko kuma idan ya zamto tana haila amma bata ovulation musamman ga matan dakan yi haila batare da wani ciwon mara ko wata damuwa sosai ba
  • Wanda rashin ovulation kansa  wani lokacin kwatsam Mace sai taga jini a tsakiyar wata alhalin tasan ba lokacin haila bane.
  • Magance yawan zubar jinin a wannan macen ya rataya ga magance matsalar macen bayan angano,walau ƙiba,pcos

Domin karanta bayani akan Pelvic Inflammatory Disease (PID) Danna nan

(2) Tsiron cikin Mahaifa na fayiburod (Fibroid); wanda kan fito jikin mahaifar mace wanda suke a tsakanin shekarun haihuwa wato shekaru 15 zuwa 50, musamman a matan da suka sami jinkirin haihuwa ko na aure,ko rashin daukar ciki akai-akai. Fibroid kansa zubar jini sosai ko jini yake zuwa a tsakiyar wata ya zamto lokacin da mace bata tsammanin haila kwatsam sai taga jini, ko ya rika daukewa yana dawowa,ko haila ta wuce kwanakinta.

Yin scanning agano matsalar tare da magancesa ko aiki aciresa na jawo zubar jinin ya daidaita ya dena.

(3)  Tsiron cikin mahaifa na Folif (polyp) shima tsirone dakan yi kamar fibroid saidai shi bai cika ƙara girma ba,kuma yafi a matan da suka manyanta suke gab da daina haila,wannan kansa ko bayan dena haila mata suke ganin jini na diga musu lokaci lokaci wato spotting. shima magancesa ta hanyar ciresa kansa a rabu da matsalar.

(4)   Sai tsiron ƙurarraji a wajen mahaifa wato”Adenomayosis”sakamakon glands din tsokokin mahaifar dakan kumbura su zamo sunyi kurji,wannan na haddasa zubar jini sosai  kaga mace na zubar da jinin haila kamar anyanka wata dabbar,sosai tare da matsanancin ciwon mara,tare da birgima. Zuwa ga likitocin mata (Gynecologist) bayan gano matsalar tare da dorata akan magani shine mafita.

Karanta cikekken bayani akan Malaria In Pregnancy Danna nan 

(5)  Macen da aka sakamata IUD cikin mahaifa na tazarar iyali,wasu daga side effect din da sukan fuskanta shine zubar jini sosai yayin haila koma jinin ya riqa musu wasa musamman matan da aka sanyawa copper IUD me ƙunshe da estrogen da progesterone. 

Don haka magance wannan matsalar shine a canzawa mace IUD zuwa ga me progesterone kadai zalla banda estrogen,ko kuma a canza mata wata hanyar planning din zuwa implanon, allura,maganin sha ta baki ko wata hanyar daban,ana haka jinin zai dedeta.

(6)  Samun juna biyu a ɓangaren mahaifar da bai saba aje ɗa ba,wato maimakon can cikin uterus inda yake da zurfi da faɗi,amma sai ya zamto cikin gashi a cikin mahaifa amma daga farko-farkon bakin mahaifar ana wuce cervix”fulasanta firebiya”wannan kanja mace taga jini na zuba,shine ma wasu kanyi zargin ga mace nada ciki amma tana haila,abinda ba haka ya kamata ya faru ba.

Wannan saidai a zuba idanu ai hattara,a hana mace aikin karfi sosai domin cikin na iya samun matsala akoda yaushe ko ya jawo aikin gaggawa na CS domin a cire cikin.

Karanta Abubuwan Daya Dace A Sani Akan Allurar Artemether

(7)   Cutar kansar bakin mahaifa ko cikin mahaifa (cervical cancer) zubar jini sosai musamman bayan duk anyi magunguna amma abu ya cigaba hakan ka iya zama alamun dake nuna tsokokin bakin mahaifar mace sun fara rikiɗa zuwa kammanin ƙwayoyin kansa, musamman ganin jini ba tsammani ko yake fita sosai,shiyasa gashinan ake gwajin kyauta don haka zuwa aiwa mace gwajin musamman me auren data haura shekara 30, ko wacce ke gab ko ta dena haila,wacce dai aka riga aka saba saduwa da ita,ko wacce take da zargi me karfi akan mijinta manemin mata ne,banda ƴan mata matuƙar mace bata taɓa sanin namiji ba,domin kwai masu amsa sunan yan mata amma ko mai aure ba lallai takaisu sanin daɗin namiji ba irin wannan sune kan gaba cikin wanda ya dace suje ai musu cervical cancer screening da za’a buɗe asa spatula a dangwalo majinar bakin mahaifar su a tantance.

(8)   Hakazalika matsalar ka iya zamowa adalilin larurar zubar jini ta gado sakamakon sun gaji karancin sinadaran dake sanya jini tikkewa da sauran tsaida zubarsa,kamar su hemofiliya ko bonwilbiran,irin wannan larura ce ta gado baka iya rabasu da ita complete saidai ana iya basu magani da zai takaita fitarsa don ganin ba ashiga wahala ba.

(9)    Hakazalika yana iya kasancewa a dalilin wani magani da mace kan amfani dashi wanda shine ke sanya period na mata rushing,kamar maganin tazarar haihuwa nasha wato OCP, ko maganin katsa jini ga masu larurar kumburi ko ciwon zuciya da akan basu,ko shan magani irinsu aspirin,irin waɗannan dakatar dasu ko canza musu kalar magani shine mafita.

(10)   Matan dake da ciwon koda,ko ciwon hanta ko makoko wato “thyroid disease” suma sukan fuskanci wannan matsalar,don haka maida hankali wajen maganin matsalar shi zai taimaka su rabi da heavy bleeding din.

 Don haka kowacce matsala kunji abin da na faɗa matsayin hanyar magance ta,don haka zuwa ga kwararun likitoci medical doctors da kuma gynecologist likitocin mata shine zai taimaka agano tushen matsalar da kuma hanyar da za’a bi a magance,karki ce ai naje asibiti amma har yau, a’a ta yiwu ba babban asibiti kikaje ki kaga Gyne doctor ba. inma shi kika gani in babu canji ba laifi bane kije wani asibitin ki ƙara ganin wani gyne ko medical doctor din,ta yiwu a sami bambancin kwarewar aiki.

Domin karanta bayani akan Noristerat (Norist) Danna nan 

labarin da ya wuceMalaria In Pregnancy
Labarin na GabaIna Ba da Nono Amma Baya Isar Jaririna, Ko Kuwa Ba Maiƙo