Sau da yawa wasu sukan samu matsala da manunin kwamfutarnsu, wato “mouse”
To daga lokacin da mouse ɗinka ya daina, a lokacin da za ka yi amfani da shi, to sai ka mayar da keyboard ɗinka ya zama kana iya aiki biyu da shi, ya yi aikinsa na keyboard sannan ya yi kuma na mouse.
Yadda za a yi kuwa shi ne abi waɗanann matakan:
- Sai ka yi amfani da Alt+Shift na hannun hagu +number lock sannan a danna Enter Key.
- Sai a yi amfani da lambobi don gabatar da aikinka misali;
Danna lamba 5 Yana matsayin Click
Ko ka danna alamar + Yana matsayin Double click
Ko kuma ka danna alamar – Yana matsayin Right click
Domin karanta cikakken bayani a kan Yadda Za ka Lalata Wayarka Idan Ta Ɓata danna koren rubutun nan