Yadda Tsayar Da Gemu Yake A Al’adar Fulani

0
58

A al’adar Fulani ana tsayar da gemu a lokacin da wanda za a sanya wa gemu ɗansa ko ‘yarsa ta yi aure har ta haihu. Idan kuma ba a haifa masa ɗa ko ‘ya da aka yi wa aure ya haihu ba, sai ya tsayar da gemu a lokacin da ɗa ko ‘yar tsaransa ya haihu. Ana tsayar da gemu a lokacin wani biki na aure ko haihuwa.

A mafi yawancin lokaci ana tara tsararrakin juna a haɗa su wuri ɗaya don a tsayar masu da gemu. Ana kuma la’akari da waɗanda aka yi wa kaciya a rana ɗaya, sai kuma a sake haɗa su don tsayar masu da gemu a rana ɗaya. Ana tsayar da gemun ne a wurin da ake yin bikin. Tun kafin zuwan ranar ake sanar da ‘yan’uwa da abokan arziki da kuma wanzamin gidan wanda shi ne zai sanya wa wannan mutum ko mutane gemu.

A ranar da za a sanya gemu bayan dukkan ‘yan’uwa da abokan arziki waɗanda aka gayyata sun taru, sai a kawo ƙwaryar madara a samo ganyen kalgo a naɗa gammo da shi a saka cikin wannan ƙwaryar madara. Daga nan sai wanda za a sanya wa gemu ya fito ya zauna a gaban dattawa. A al’adar Fulani an fi son wanzamin da zai sanya wa wani gemu,ya kasance wanda dukkan mahaifansa watau uwa da uba suke raye.

Idan kuwa wanzamin da yake yin wanzanci a wannan gida ya rasa ɗaya daga cikin mahaifansa, sai a sami wani daga cikin dangin wanda za a sanya wa gemu kuma wanda dukkan mahaifansa suke a raye ya fara sanya wa wannan mutum gemu. Yadda ake yi shi ne wannan wanda aka wakilta don ya fara sanya gemu zai shafa ruwan madara na cikin ƙwarya da sabulu, daga nan sai ya riƙa shafa bayan askar a wurin gashin haɓar wanda za a sanya wa gemu.

Daga nan sai ya mayar wa wanzamin da askarsa don ya ci gaba da yin aski da gyaran fuska wanda za a fito da gemu daga nan ya tsaya ba a ƙara aske shi. Idan za a sanya wa Fulani gemu ana aske saje da gashin baki da hana-ƙarya, shi kuma gemun ana kwakkwafe shi sosai ba a barin sa da faɗi sai dai siriri mai tsawo.

Bayan an gama sanya wa wannan mutum gemu idan akwai wani tsaransa wanda ya isa sanya gemu amma sai ya ƙi sanyawa, a al’adar Fulani sai a sami wani abokin wasansa ko wani dattijo ya mame shi ya ɗauko wannan gammo na ganyen kalgo wanda yake cikin madarar ya shafa masa a gemunsa.

Da zarar an shafa masa wannan ganye daga nan ya zama dole gare shi ya zauna a sanya masa gemu ko ya shirya ko bai shirya ba. Wannan dalili ne ya sa waɗanda suka san cewa sun isa sanya gemu amma saboda wasu dalilai nasu ba su sanya ba, ko an gayyace su zuwa wurin sanya gemu ba sa zuwa.

A lokacin da ake sanya gemu ‘yan’uwa da abokan arziki za su riƙa bayar da kari. Daga cikin abubuwan da ake bayarwa akwai kuɗi da dabbobi. Bayan an gama sanya gemun, sai a miƙa wa dattawa ƙwaryar madarar da aka yi amfani da ita wajen sanya gemu. Kowannensu zai sha wannan madara ya kuma shafa wa gemunsa gammon ganyen kalgon da yake cikin madarar.

Daga nan sai su yi masa huɗuba dangane da abubuwan da suka dace ya riƙa yi da waɗanda ba su dace ya riƙa yi ba. Bayan nan kuma sai dattawan su karkasa kuɗin da aka samu na kari zuwa kashi uku. Kashi na farko a raba wa wanzamin da ya sa gemun da maroƙa, kashi na biyu a ba malamai waɗanda za su yi addu’a, kashi na uku kuma ana sayen goro don a rarraba wa mutanen da suka tattaru a wurin sa gemun. Sauran abubuwan da aka samu kamar dabbobi ana bar wa wanda aka sanya wa gemu, daga nan sai malamai su yi addu’a.

Waɗannan al’adu na tsayar da gemu a wurin al’ummar Fulani sun yi tasiri a kan yadda wasu Hausawa suke tsayar da gemu. Daga cikin ire-irensu akwai ta lokacin ajiye gemu da kuma wanzamin da zai tsayar da gemu ya kasance wanda dukkan mahaifansa suke raye. Haka kuma akwai wasu Hausawa waɗanda a lokacin da za a gyara masu gemu, sai su sanya a yi shi siriri kamar irin yadda ake yi wa Fulani.

Askin Jarirai Na Ranar Suna

Wani ɓangare na wanzanci wanda al’adun Fulani suka yi naso a cikinsa shi ne askinn jarirai na ranar suna. A al’adar Fulani ba a fito da jariri a ranar suna don yi masa aski, wai don tsoron kada mayu su cinye shi. Wannan dalili ya sa Fulani ke kiran wanzami kafin ranar suna ko bayan suna don ya yi aski ba tare wasu mutane sun ga wannan jariri ba. Wannan al’ada ta yi tasiri a wurin wasu Hausawa.

A yau akwai wasu Hausawa waɗanda suka yi koyi da wannan al’ada ta Fulani waɗanda ba sa fito da jariran da aka haifa masu a ranar suna don yi masu aski. A maimakon haka ana yin askin kafin ko bayan suna, wai don tsoron kar mayu su cinye wannan jariri.

Nason Al’adun Fulani Dangane da Kaciya

A wurin yin kaciya ma al’adun Fulani sun yi naso dangane da yadda ake yin ta da kuma wasu al’adu waɗanda suka jiɓance ta. Za a iya ganin haka ta yin la’akari da ranakun da Fulani suka keɓe don yi wa ‘ya’yansu kaciya. Waɗannan ranaku sun haɗa da Juma’a da Lahadi da Talata da Alhamis.

A al’adar Fulani ba a yi wa yaro kaciya sai shekarunsa na haihuwa sun kai tara zuwa goma sha biyu. A ranar da aka yi wa yaro kaciya da an gama, sai a daka garin gero a dama da nonon shanu a ba yaron da aka yi wa kaciyar ya sha. Haka kuma ana ba dukkan mutanen da suka zo wurin da aka yi kaciyar wannan gari su sha. Shi ma wanzamin da yaransa ana ba su wannan gari su sha. Dalilin shan garin shi ne don a sanyaya zuciyar wannan yaro da aka yi wa kaciya.

Waɗannan al’adu na Fulani dangane da ranakun da ake yin kaciya akwai wasu Hausawa a sassa daban-daban na ƙasar Hausa musamman waɗanda suke yin hulɗoɗi da Fulani suna yi wa ‘ya’yansu kaciya a waɗannan ranaku. Haka kuma akwai waɗanda saboda koyi da al’adun Fulani ba sa yi wa ‘ya’yansu kaciya, sai a lokacin da shekarunsu na haihuwa suka kai tara ko wuce nan.

Nason Al’adun Fulani A Kan Tsagar Hausawa

Tsaga musamman ta gado da ta kwalliya suna daga cikin al’adun Fulani waɗanda suka yi naso cikin wanzancin Hausawa. Ba kamar Hausawa ba waɗanda a mafi yawancin lokaci ‘yan mata ne kawai ake yi wa tsagar kwalliya, su Fulani ana yi wa ‘yan mata da samari, kuma idan za a yi tsagar ba a yin biki kamar yadda ake yi a lokacin da za a yi wa ‘yan matan Hausawa.

Akwai ire-iren tsagar gado da ta kwalliya na Fulani da dama waɗanda har a wannan zamani ana yi wa ‘yan mata da samarin Fulani ire-irensu,kuma samari da ‘yan matan Hausawa na kwaikwayon yin su. Ire-iren waɗannan tsaga sun haɗa da tsagar gado ta kalangu da fetali da kuma tsagar kwalliya ta ‘yar goshi da kibau da ‘yar baka.

Tsagar Gado

A lokacin da Fulani Dallazawa masu jihadi suka ci Katsina da yaƙi suka kafa mulkin Fulani a wannan masarauta, wasu Hausawan ƙasar Katsina sun riƙa kwaikwayon al’adunsu musamman waɗanda suka shafi tsaga. Asalin tsagar gado ta Katsinawa ita ce bille ko tsagar Katsinanci (Sallau, 2000:62, 78).

Su kuma Fulani Dallazawa tsagarsu ta gado ita ce kalangu (Sallau, 2000:90). Saboda kusanci da waɗannan Fulani, sai wasu Katsinawa waɗanda asalinsu Hausawa ne suka daina yi wa ‘ya’yansu tsagar gado ta billen Katsinanci, sai suka maye gurbinta da tsagar kalangu irin ta Fulani Dallazawa.

Wannan dalili ne ya sa a yanzu a ƙasar Katsina akwai Katsinawa waɗanda Hausawa ne gaba da baya waɗanda suke yi wa ‘ya’yansu maza da mata tsagar kalangu a matsayin tsagar gado.

Irin wannan al’amari ya faru ga wasu Hausawan a ƙasar Katsina a lokacin mulkin Fulani Sulluɓawa waɗanda su tsagarsu ta gado ita ce fetali a hannun hagu (Magaji, 2002:23). A nan ma an sami wasu Hausawa waɗanda suka maye gurbin tsagarsu ta gado ta billen Katsinanci zuwa tsagar fetalin hannun hagu irin na Fulani Sulluɓawa. Haka kuma tsagar gadon mahauta ita ce tsagar fetali a hannun dama (Sallau, 2000:77). Su ma a wannan zamani, sai suka bar yin irin wannan tsaga a hannun dama suka mayar da ita a hannun hagu irin ta Fulani Sulluɓawa.

Dukkan waɗannan nau’o’in tsagar gado na Fulani har a wannan zamani akwai wasu daga cikin mutanen ƙasar Katsina da ke yi wa ‘ya’yansu ire-irensu a matsayin tsagarsu ta gado. Hasali ma akwai waɗanda suke haɗa duka biyun wato tsagar kalangu ta Dallazawa da fetalin hannun hagu ta sulluɓawa.

Tsagar ‘Yar Goshi

Irin wannan tsaga ana yin ta a goshi, amma ita ko kusa ba ta yi kama da irin tsagar ‘yar goshi wadda ake yi wa Hausawa ba. Siffar wannan tsaga ta yi kama da kofin da ake sanyawa don cin wata gasa.

Tsagar Kalangu

Ita ma tsagar kalangu irin ta Fulani tana da bambanci da irin wadda ake yi wa Hausawa. Tsagar kalangu irin ta Fulani ana yin ta ƙanana kuma sirara ba kamar irin ta Hausawa ba wadda ake yi da girma. ’Yan mata da samarin Fulani ba a yi masu kalangu biyu-biyu kamar yadda ake yi wa ‘yan matan Hausawa, su ɗaya-ɗaya ake yi masu.

Tsagar Kibau

Ana yin irin wannan tsaga kamar siffar kibiya, daga nan ne ta sami wannan suna. Ana yin ta ne a fuska bisa kundukuki daidai ƙarƙashin idanu wurin da ake yi wa ‘yan matan Hausawa tsagar kwaluluwa. Asalin wannan tsaga ‘yan mata da samarin Fulani ake wa, sakamakon cuɗanya tsakaninsu da Hausawa ya sa ‘yan matan Hausawa kwaikwayon yin irin wannan tsaga. 

Tsagar ‘Yar Baka

Wata tsagar kwalliya wadda ake yi wa ‘yan mata da samarin Fulani wadda kuma ta yi naso cikin al’adun wanzanci da na Hausawa, ita ce tsagar ‘yar baka. Irin wannan tsaga ba ta yi kamanni da irin wadda ake yi wa ‘yan matan Hausawa ba wadda ake yin ta caɓa-caɓa a kumatu. Irin wannan tsaga ana yin gororin tsaga uku-uku ne a kowane kunci kuma kowace ana yin ‘ya’yan tsaga uku-uku ne, amma da na sama da na ƙasa ana yin su a gicciye ne ta tsakiyar ce ake yi a tsaye.

Ana yin gororin wannan tsaga da ɗan tsawo kuma dukkan su suna ƙarewa a wutsiyar baki. Bayan an yi waɗannan layuka na tsaga ana haɗe su da ƙananan ‘ya’yan tsaga waɗanda su ma ana tsara su uku-uku ana kuma barin ɗan fili a tsakani. Ita ma irin wannan tsaga ‘yan matan Hausawa suna kwaikwayon yin ta.

Dukkan waɗannan nau’o’i na tsaga waɗanda aka yi bayani a kan su wanzaman Hausawa suna yi wa ‘yan mata da samarin Fulani ire-irensu.Wannan dalili ne ya ƙara jawo hankalin ‘yan matan Hausawa kwaikwayon yin ire-iren su.

Cire Belun-Wuya

Wani ɓangare na al’adun Fulani wanda ya yi tasiri a kan wanzanci shi ne wajen cire belun-wuya ko hakin-wuya. A al’adar Fulani a lokacin da aka cire belun-wuya, sai a ɗura wa jaririn da aka cire wa belun nonon shanu mai tsami. Dalilin da ya sa ake ba shi irin wannan nono shi ne don jaririn ya sami sauƙin ciwon da ya biyo bayan cire masa wannan belu. Haka kuma yana taimakawa wajen tsayar da jini daga wannan wuri da aka cire belun kuma wurin zai yi saurin warkewa.

Wannan al’ada ta Fulani ta yi tasiri sosai wurin wasu Hausawa don kuwa akwai waɗanda a duk lokacin da aka cire wa jaririn da aka haifa belun-wuya, sai su ɗura masa nonon shanu mai tsami kamar yadda Fulani suke yi don yin magungunan da aka yi bayani a kansu.

Goyon Ciki

Wani fanni na al’adun Fulani wanda ya yi naso cikin al’adun Hausawa har abin ya shafi sana’ar wanzanci, shi ne goyon ciki. A al’adar Fulani idan mace ta sami cikin fari ba ta haihuwa a ɗakinta. A lokacin da cikin ya kai wata shida, sai a mayar da ita gidan mahaifanta don ta haihu a ɗakin mahaifiyarta. A lokacin da ta haihu haƙƙin mutanen gidan da take aure ne su turo wanzamin gidansu don ya yi wa abin da aka haifa dukkan ayyukan wanzanci.

Kamar al’adar Hausawa su ma Fulani namiji ne yake da haƙƙin kiran wanzami ba mace ba. Wannan ne ya sa wanzamai zuwa gidajen da ba su ke yin wanzanci ba yin ayyukan wanzanci,don kuwa matar da ta haihu a wannan gida tana aure ne a gidan da suke yin ayyukan wanzanci (Sallau;2000: 9). A nan tasirin al’adun Fulani ya yi naso cikin al’adun Hausawa saboda a al’adar wanzanci wani wanzami ba ya zuwa gidan da wani yake yin aiki ya yi.

Nason Al’adun Fulani Kan Ladar Aikin Wanzanci

A lokacin da aka yi wani aikin wanzanci ga al’ummar Fulani wanda aka yi wa ko iyalansa suna bakin ƙoƙarinsu wajen kyautata wa wanzamin da ya yi wannan aiki. Misali, idan aka yi kaciya bayan kuɗi suna kuma ba da zakara ko kaza ko zabo da kuma damen dawa. Haka kuma idan aka yi suna a gidajensu, idan wanzami ya zo kafin ya yi askin jariri na suna ana ba shi abinci mai kyau wanda ya haɗa da dambu da madara a kuma zuba man shanu a ciki.

Ana kuma dama fura da nonon shanu mai kyau a kawo wa wanzamin ya sha. Bayan kuɗin aski da ƙwaryar aski suna kuma ba wanzamin kan dawo da nono don ya kai wa iyalinsa. Hausawa sun riƙa kwaikwayon yin irin wannan al’ada.

A lokacin ɗaurin auren budurwa akwai al’adar da Fulani suke kira da sunan walima wadda ake yanka sa ko saniya wanda ake rarraba naman dabbar da aka yanka kashi-kashi a ba kowa nasa rabon. Daga cikin waɗannan kashe-kashe akwai kushekara da ‘ya’yanta waɗanda su ne kason wanzamin da yake yin aikace-aikacen wanzanci a wannan gida.

Bayan kushekara kuma ana ba shi goro a lokacin da za a ɗaura aure. Dalilin da ya sa ake ba wanzami waɗannan abubuwa shi ne, wai don shi ne ya yi wa wannan budurwa wadda za a yi wa aure gyara a farjinta a lokacin tana jaririya. Saboda haka waɗannan abubuwa suna daga cikin ladar aikin da wanzamin ya yi.

Dukkan waɗannan al’adu na Fulani da aka kawo a bayani kan su, sun yi naso ne a kan wasu al’adun Hausawa waɗanda suka danganci sana’ar wanzanci da yadda ake yin ta. Haka kuma a mafi yawancin lokaci wanzaman Hausawa ne ke yi wa Fulanin da Hausawa.

Magungunan da Wanzamai Suka Samo Daga Wurin Fulani

Wanzamai sun sami magungunan cutar ciwon saɗɗore da kuma ciwon ɗankaɗafi daga wurin Fulani. Shi saɗɗore ciwo ne da yake kama mutum a ƙafa ko a hannu, sai ƙuraje su fito wa mutum caɓa-caɓa a wurin. Wannan ciwo yana da wuyar yin magani, don kuwa sai a yi magani ya warke, bayan wani lokaci kuma sai ya dawo. Maganin wannan ciwo da aka samo a wurin Fulani shi ne, sai a samo ɗan kuka wanda bai ƙosa ba, kuma wanda ya faɗo ƙasa da kansa, watau ba wani ya hau ya ciro shi ba.

Idan an same shi, sai a ƙona shi, bayan ya huce sai a sami citta mai ‘ya’ya a haɗa su da jar kanwa a daka ya yi gari sosai. Daga nan sai a sami wani ɗan ƙoƙo ko kwano a zuba maganin ciki, a haɗa da man shanu ɗanye a cakuɗe su. A kullum sai a sami ruwa mai ɗumi a riƙa wanke wurin da ciwon yake a riƙa shafa wannan maganin. A duk lokacin da za a shafa maganin, sai an wanke wurin da ciwon yake da ruwan ɗumi. Za a yi ta yin haka har sai wurin ya warke (Hira da AAB, a Daɗin-Kowa Jihar Gombe, a ranar 23/4/2006).

Karanta Magungunan Gargajiya Na Wanzamai

Wannan bayani an ciro shi ne daga kundin bincike mai taken: SANA’AR WANZANCI DA SAUYE-SAUYEN ZAMANI JIYA DA YAU wanda BASHIR ALIYU SAFANA SALLAU WANDA AKA GABATAR A TSANGAYAR FASAHA DA ADDININ MUSULUNCI SASHEN KOYAR DA HARSUNAN NIJERIYA JAMI’AR BAYERO, KANO, DOMIN CIKA WANI ƁANGARE NA SAMUN DIGIRI NA UKU (Ph.D) A FANNIN HAUSA

MAYU 2009/JUMADA ULA 1430

Edita@rumasau-kallamu

labarin da ya wuceShayar Da Jariri Nonon Uwa Zalla (EXCLUSIVE BREASTFEEDING)
Labarin na GabaNason Al’adun Baƙi Maƙwabta Na Kusa A Wanzancin Hausawa
Prof. Abdalla Uba Adamu
Farfesa Abdallah Uba Adamu, Gangaran ka fi gwani! Gogaggen masanin harkar ilimi; bajimin marubuci; fitaccen mai karantarwa a matakin ƙasa-da-ƙasa (International Visiting Lecturer), ayyukan da yake da gogayyar shekaru arbai’in cif a ciki (1979 – 2019). Dambu mai hawa biyu, shi ne farfesa biyu a ɗaya, abin nufi, farfesa a fannonin ilimi guda biyu; Fannin Ilimin Kimiyya (Science Education) da kuma fannin Sadarwar Al’adu da Kafafen Sadarwa (Media and Cultural Communication) daga Jami’ar Bayero ta Kano.