Yadda Neman Laƙani Da Asiri Ya Shiga Tsangayu

0
473

Kamar yadda ya gabata, makarantu a tsarin tsangaya sun shahara da neman laƙani ko wani sirri na Alƙur’ani don samun biyan buƙatun rayuwa.

Da yawa akan samu makarancin da ke ɗalibta wajen wani Alaramma, ba don ya koyi wani abu ba; sai don kawai wannan alaramman ya sanar da shi wani laƙani. Irin wannan shuhura a fagen sanin laƙanoni shi ne a mafi yawan lokaci yake fito da malami ko kuma ya samu wani kwarjini na musamman a wurin al’umma. Da zarar malami ya zama gwani a wannan ɓangare na laƙani; to fa jama’a za su yi ta taruwa zuwa gare shi.

To wannan yanayi cikin rayuwar makaranta, shi ya ƙara buɗe ƙofar kasuwar tsibbu a tsarin tsangaya. Don haka ma ake samun makarantar da ke sare sanda a fagen laƙani; har ake kiran su Malam Gobe-da-nisa ko Malam mai gani har hanji da sauransu. Asalin laƙani a wurin makaranta an fi yin sa ne don fahamin karatu da kuma maganin wasu cututtuka kamar yadda ya gabata.

Alƙur’ani dai magani ne na dukkan cuta, sawa’un cutar zuciya ko cutar jiki; Kuma amfani da ayoyin Alƙur’ani don magani sanannen al’amari ne tun zamanin Sahabbai (Radiyallahu Anhuma).

Mas’alar rubuta Alƙur’ani a sha kuwa sananniya ce a wurin malamai; kuma abu ne mai asali matuƙar ba a jirkita Alƙur’anin ba. Amfani da Alƙur’ani a matsayin maganin cututtukan jiki da samun biyan buƙata a Arewacin Najeriya yana da faɗi. Mutane kan nufi makaranta a tsangaya don neman dafa’i ko jalabi, neman kasuwa, maganin ciwon jiki; fahamin karatu, haihuwa, da raba aure, sammu farin jini, jifan wani da sauransu.

Irin waɗannan laƙanoni sun haɗa da Baru uwa-uba da Burdin Yasin da Ummi Musa da Darni; da kurat mai fika-fikai da Gursan da Tabbat Yada mai ƙwai, da kinzan waji da gwamalan da Zailun da sauran su.

A ɓangare guda kuwa, makaranta a tsarin tsangaya; musamman a Maiduguri sun shahara da ɗaukar mummunan mataki; ko ramuwar gayya kan duk wanda suka samu taƙaddama ko rashin fahimtar juna da shi. Masu irin waɗannan asirai kan sabbaba tawaya ko cutuwa ko ma mutuwar abokin hamayyarsu. Makaranta kan jefi junansu wadda zai iya kawo zubewar tilawar ɗan uwansu ko samun tasgaro a rayuwarsa. A arewacin Najeriya a kan ce an yi wa wane Yasin ma’ana an yi masa asiri. Anya kuwa surar ta Yasin ake karantawa babu wani kauce hanya?

Tsokaci

Yana da kyau mu ba wa mai karatu haske game da yadda laƙani yake, kuma yaya ake yin sa? Mene ne bambanci tsakanin amfani da Alƙur’ani ta fuska halattacciya da kuma wadda ta haramta?.

Domin karanta cikakken bayani a kan Haramtaccen Laƙani Ko Asiri danna nan.

Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Tsarin Tsangayun Alƙur’ani A Arewacin Najeriya; Tarihin Su Da Zamantakewar Su Da Hanyoyin Raya Su; wanda Dr. Sunusi Iguda Ƙ/Nasarawa ya wallafa shi; domin karanta cikakken Littafin danna nan.

labarin da ya wuceMatsayin Tsibbu Da ‘Yan Tsibbu A Wurin Shehu Usman Bn Fodiyo
Labarin na GabaHaramtaccen Laƙani Ko Asiri