Yadda Manufar Rayuwarka Take

0
33

Manufar Rayuwarka
Wannan kusan zan iya cewa shi ne ma ya kamata ya zo a farko, amma na jinkirta shi ne saboda amsar da ka samu daga sanin kai wane ne ita za ta haska maka manufar rayuwarka. Kowa akwai abin da Allah ya halicce shi ya yi a wannan duniyar, wanda ya gano na sa da wuri kuma ya duƙufa a kai shi ne yake cimma nasarori da wuri.

Idan ka bibiye littafin nan tun daga farko, za ka gano wata gaskiya guda, babu irinka a duniya. Kafin a samu wani da ƙwayar halittarku ta zo ɗaya, shekarunku, iliminku, gogewarku, abokanku, iyayenku, makaranta da unguwarku duk ɗaya abu ne mai matuƙar wahala.

Kenan kai a matsayinka na wanda babu irinsa akwai abin da za ka yi da rayuwarka da ba lallai wani ya yi irinsa sak ba. Ba kowa ne yake iya gano manufar rayuwarsa ba ko da ya san kansa, amma aƙalla dai zai zama ya samu wata hanya da yake bi, tunda ya san shi wanene, zai gane ina ya kamata ya dosa.

A lokacin da yake kan hanyar ne kuma Ubangiji zai ta haskaka masa yana nuna masa abubuwa. Wani lokacin za ka yi ta yin wani abu ba ka ɗauke shi a bakin komai ba, sai
rayuwa ta yi nisa sai ka ga ashe wannan abin kamar an shirya ka ne don ka zama wani da shi a gaba. Wani lokacin kuma kwatsam wani abin zai faɗo rayuwarka, in ka ba shi lokacinka da tunaninka sai ka ga hanyar tana ta ƙara faɗaɗa.

Yana da kyau mai ƙoƙarin gano manufarsa ya amsa waɗannan tambayoyin. Ni wanene? Daga ina nake? Ina zan je ni? Yanzu a ina nake? Me nake yi yanzu don isa wurin? Lallai waɗannan tambayoyi matukar an dage da yinsu ba za a samu zaman lafiya ba sai an isa wurin. Kuma hakan ake buƙata.

Ita rayuwa duk lokacin da ta ga wani gurbi ba a cike shi da komai ba, sai ta cike wa mutum da wani abu da ba zai amfane shi ba. Kamar yadda basirar da aka ƙi yin komai da ita take nemawa mai ita abin yi, haka rayuwa take raba mana ayyuka ba tare da mun shirya musu ba. Kafin mu ankare kuma sun zame mana jiki sai mu ma ɗauka dama su ne ya kamata mu yi ta yi.

Abin dai da yafi muhimmanci shi ne mu ayyana wa kanmu wata hanya da muka ɗauka muke son bi, wannan zai sa komai na mu ya dinga tafiya a tsari, in ma hanyar ba mai ɓullewa ba ce ba mu da asara, za mu samu darussa da dama, kuma ta haka za mu lalubo mai ɓullewar. Kowa nan duniya da ka gani da gwaji ya kai in da ya kai, wanda yake tsoron faɗuwa ba ya taɓa zama gwani.

Duk lokacin da aka yi zancen manufa dai ya zama kana tuna cewa Allah ne ya halicce ka, kuma yace ka bauta masa, kuma yace in ka bauta masa zai maka sakamako da aljanna, kenan ya zama dole ya zama koma mene ne za ka yi kana kawo waɗannan abubuwan a farko.

Duk layin da ka ɗauka ka ga ba zai kai ga wannan ba daga ƙarshe, wannan ba layin kamawa ba ne, ka yi ƙoƙari ka watsar da shi ka nemi wani. Allah yana da kyauta, duk abin da za ka yi in ka yi da niyyar ya ba ka lada babu abin da zai hana ya baka lada sai in har ka saɓa masa ko ka saɓawa koyarwar manzonsa.

A taƙaice dai jin daɗin lahira ne yake zama kan gaba cikin tunanin mai manufa da kuma aiki yadda addini yace a yi, ko da kuwa a yanzun baƙar wahala yake sha, tunda ya san sakamakonsa yana can. Abubuwan da za su taimaki mutum a kan manufa sun haɗa da kyautatawa Allah zato.

Duk inda kake tsammaninsa a nan yake kamar yadda ya faɗa a hadisul Ƙudsi. Bayan wannan sai mutum ya so kansa, ka da ka raina kanka duk yadda kake, domin kana da wani abu da za ka iya bayarwa ba tare da ka ma sani ba. Daga nan sai tsaida hankali kan ƙananun abubuwa na kusa, kada ka shagaltu da tunanin manyan abubuwan da za ka yi, har hakan ya hana ka yin ƙanana.

Na sha shagaltuwa da tunanin manyan abubuwan da yakamata ace na yi ko ina yi, a haka lokacina zai tafi, ban yi ƙanana na kusa da ni ba, kuma babban ma ba yi zan yi ba. Yanzu da na fara ƙananan sai haske yake ta zuwa mini, nake samun matakala da za tai ni zuwa ga sauran.

Ba dole sai ka shahara da wani abu ba za ka ba da gudunmawa, amfanin manufa shi ne kawai ya zama an ƙaru da kai ko yaya ne. In dai ana ƙaruwa da mutum kuma hakan ya sa a gaba to ya riga da ya samu manufa, ko da ba a san shi a dandalin sada zumunta ba (in hakan ba ya cikin burinsa kenan).

A matsayinmu na bayi, waɗanda ba mu san ƙaddararmu ba, aiki shi ne na mu, zartarwa kuma na mamallakin ranar sakamako ne. Ganin damarsa ne ya cika mana burukanmu tun a nan, ganin damarsa ne kuma ya mana tanadi a can, ba a masa dole, ba a kuma kwanciya da sa ran shi zai yi, za mu yi, za mu jira zartarwarsa ba tare da ƙosawa ba, in bai ba mu ba sai mu sake gwada wani layin, wataƙila a can rabon yake.

Wanan bayanin an ciro shi ne daga littafi mai taken Ka San Kanka wanda AHMAD SANI ya wallafa.

Danna nan don karanta Yadda Za Ka Tambayi Kanka Da Kanka

Edita@rumasau-kallamu

labarin da ya wuceYadda Za Ka Tambayi Kanka Da Kanka
Labarin na GabaKammalawa Daga Cikin Littafin Ka San Kanka
wikiHausa
wikiHausa kundin ilimi (insakulofidiya) ce da ke ilimantar da jama'a yara da manya da maza da mata wajen samun ilimi a saukake, cikin harshen Hausa.