Yadda Illolin Wasu Daga Kayan Ado Da Na Kwalliya Suke

0
672

Abu ne mai kyau  mu zayyana kaɗan daga wasu kayan kwalliya na tufafi da shafawa da sauransu, waɗanda za su iya zama illa ga mace don necsancesu.

Saboda ta yi amfani da nau’in  kayan kwalliya da zasu biya mata buƙatarta ta ado ba ta kauce  ƙa’idojin Muhaliccinta ba , kuma ba tare da ta cuci kanta-da-kanta ba.

  • Matsatsatsun Kaya:
  Sanya matsatstsun kaya ga wasu mata ya zama rowan-dare gama duniya. Irin waɗannan mata sukan fifita kayan da za su matse jikin tamau! Yadda za a iya ganin ƙirar jiki
Mafi yawa daga bayanan kiwon lafiya da suka zo a wannan Babi, an tsamo su ne daga wani littafi mai saua “Zinatul Mar’a Bainal Dibbi Washshar’i” Na Muhammad Abul-Aziz  Al-Musuid, wanda gidan bugu littattafi na Sarki Fahad dake Saudi Arabia ya buga, a Watan Sha’aban, 1416 A.H.
Sosai, masana da yawa sun yi tsokaci akan irin waɗannan kaya, ta fuskokin ilimi daban- daban.
      A ɓangaren kiwon lafiya, a na ganin irin waɗannan ɗamammaun kaya suna tsananta matse jikin mace,  haka kuma yana azabtar da ita sosai, ta hanyar takurata, da rashin samun walwala, saboda haka yawan sanya irin waɗannan kayan zai sanya mace yanwan jin damuwa a ranta.
            Haka kuma matsewar da tufafi ke wa jiki zai takurawa tsarin zagayawar jini a jijiyoyinta, wannan kuma zai iya sabbaba mata cutar hauhawan jinni.
A wani faɗin ma, wasu masana cewa su ka yi;yawaita sanya matsatstsun kaya zai iya hanawa mace haihuwa, ko kuma yayi  sanadin samun tangarɗar haihuwar.
(2) Tufafi masu Bayyana Fatar jiki:
         Koƙari kwaikwayon kangararrun Turawa, ya sa wasu matan Musulumi, su na sanya  tufafi  masu bayyana wasu sassa na jiknsu, yadda za a iya ganinsa ƙarara, kamargadon baya ko faɗin ƙirji ko sha-raba, da dai sauransu.
             Sakamakon bincike ya tabbatar da bambanci tsakanin yanayin fatar maza da ta mata, a yiyin da mafiya yawan maza su ke ayyukan a waje kuma wasu sana’o’ insu sai sun kwaɓe kayansu  cikin  zafin rana , ko ruwan damina ko hunturun sanyi, amma su wanye lafiya, ikon Allah!Saboda namiji dama ɗan gaganiya ne da hada-hadar faratutowa iyali abin  masarufi,
amma mace wadda tafi kyau da killatuwa guri guda cikin aminci da mutunci, idan ta cika bayyanar da fatar jikinta ga zafin rana ko haskanta da sauran nau’o’ in yanayi mai tsanani, nan da na za ta gamu da illolin fata da na ƙashi baki ɗaya, sannan kuma yana ragewa mace ƙyallin ƙuruciya, sannan ya sanyata  ta yi saurin  tsufa.
(3) Takalmin Coge:
 Wani dogon takalmi ne mai tsinin dunduniya, ko mai faɗinta. Da yawan mata suna sanya shi don a ga tsawon su.Saya iri wannan takalmi ya na da haɗari ga laifyar mace, idan an lura za a ga takalmin yana da doguwar dunduniya sosai, sannan kuma goshinsa ya kifa ƙasa idan matce ta sanya shi, itama haka za ta kifa, don haka tafiya a gunta ba ƙararamin aiki ta ke zama ba.
Sau da yawa maza sukan zame su faɗi sakamakon sanya takalmin, kuma yawan sanya shi yana sanadin sanrewar jijiyoyin ƙafarta, daga bisani sai a sami ƙafar matce ta yi tsauri kamar dutse.
        Haka nan wannan takalmin ya na gadarwa da ciwon baya, kamar yadda takalmin yana mayar da waɗanda suka sanya shi maƙaryata, domin wadda ta sa shi kamar tana cewa ni mai tsaho ce ko kuma ni doguwa ce, amma da zarar ta sauka daga takalman sai ungulu ta koma gidanta na tsamiya! Wani mashahurin masani a ƙasar Masar Al-Ustaz Anis Mansoor, ya faɗa  a cikin littafinsa mai sun “Fi Salunil Akkad Kanatlana Ayyam” cewa wani Kamfani dake sana’anta coge a Italiya yayi bayanin sirrin da yasa suke ƙera shi a irin siffar da ita.
Cewa idan mace ta hau kan coge to za ta kifa gaba kaɗan, to idan ta yi takun tafiya, sai ta danga ƙaƙarin, dawo da jikinta bayan a wannan lokacin ko’ina a jikinta sai ya dinga kaɗawa yaddaza ta fi jawo hankalin mazaje!
  • Tiyatar kwalliya:
Larura da rashin lafiya ke sanya mutane su kwanta a yi masu aiki a Asibiti, amma wasu matan tsananin son kwalliya ne yake kai su ayimusu aikin tiyata don ƙara musu kyau (a zaton su!).
Irin wannana aikin tiyata a kan yiwa mata ne (ko maza ma a wasu lokuta) ta hanyar rage wani abu ko ƙarashi a jikinsu, akan yi aiki a rage mata faɗin ƙirji, a rage mata girman nono, ko a jeme mata fatar jiki, ko a tsaga mata wuahhirya, duka irin waɗannan ayyauka su na da haɗari ga lafiya da rayuwar mutan.
, yana da kyau a dubi irin wahalar da mashahurin hatsabibin mawaƙin nan ɗan ƙasa Amurka Michel jackso yake sha sakamakon irin waɗannan ayyuka da ka yi masa, baya ga ɓarnar dukiya da ya ke yi saboda tarairayar wannan jone-jone da aka yi a halittarsa ta asali.
      Haka kuma kowa ya san irin wannan aiki ne ya yi sanadin halakar mata Shugaban Ƙasar Nijeriya Stella Obasanjo Wadda  ta mutu a hannun ‘yan kwalliya dake wani Asibiti a Ƙasar Spain, a ƙoƙarinta na jeme fatarta ta koma kamar yarinya ‘yar bana-bakwai.
      Haka kuma irin wannan aiki na kwalliya, ya na da haɗari ga aƙidar Imani da Allah, domin a cikinsa akwai ƙoƙari canja halittar Allah, abin da ya ke haramun ne a Mu
(5) Kayan Shafe-Shafe:
Da a kwai kayan shafe-shafe iri-iri wanɗanda galibi su ke fatan, ta hanyar hana bushewa,da kuma ƙara mata taushi, da kyau, sannan a kwai wasu maye-mayen waɗanda musamman a na shafa su ne domin canjawa mace launin  fatar ta ɗungurungum, daga baƙa zuwa jawur.
2 Babu lafiya ga aikin d aaka yi saboda larura, kamar gaɓar roba ko haƙorin Asibiti.
 To,irin waɗannan kayan shafawa masu sanya launi, su ne suka fi haɗari da cutarwa ga lafiyar mutum, sannan kuma su na nuna halin rashin godiyar Allah. Kamar mace baƙa mai yin amfani da shi ta na nuna rashin gumsuwar ta da irin halittar da Allaha Ya yi mata, wananan kuwa rashin ladabi ne ga Ubangiji Maigirma da Daukaka.
    Haka kuma kayayyakin da a ke haɗa mayuka masu sauya launin, fata abubuwa ne na ƙyama da rashin imani, saboda haka ne man ya ke da ƙarni marar daɗi, kuma yawan shafa shi ya na jeme fatar mutum yadda (abin Allah ya kiyaya)idan wata larura ta samu wadda sai an yi ɗinki a gurin, to ɗinkin zai yi wahalar yiwuwa.
  (6)  Jan-Baki:
Jan-baki shi ne wani abu mai kamar alƙalmi wanda mata suke shafawa a leɓensu, sai yayi ja-jajir, ko shuɗi ko wani launin daban.
       Kasancewar jan-baki abu ne da a ke damɓara shi a leɓe, don haka yana hanawa fatar leɓe cikakkiyar iska. Saboda haka bayanwani lokaci sai leɓan ya danga yin ƙaiƙayi, da saɓa,da ɗaɗewa.
       Koda ya ke jan-baki ba shi da matsananciyar hatsari, amma ya fi kyau a rage shafa shi, kuma kada mace ta dinga sanya shi lokacin da za ta fita waje ko za ta gamu da mazajen da basu halatta ta bayyana adonta a gaban su ba , domin ya na matuƙar ƙawata ta, zama abin sha’awa ga maza.
  • Jan-Farce/Faratun Roba:
  Jan-Farace wani ruwa ne mai kama da fenti,wanda  a ke lafta shi a kan farce, don ya sanya masa kayau da birgewa. Yawanci launinsa ja ne, amma a na samun launukansa iri-iri.
       Shi  kuma farcen-roba, farce ne ɗan-kanti akan sanya shi don adoda kwalliya, ya kan zamo mai tsaho ne zaƙo-zaƙo a yatsun wanda ya sanya shi.
      Dukkannin su (jan-farce da farcen roba) suna da ill, shi dai jan-farce yana tarewa farce samun iska, ya kan sabbaba kakkaryewar farce da gautsinsa, kuma ya na hana ruwan alwala saduwa da farcen mutmu.
       Shi kuma farcen roba irin matsalarsa ɗaya da ta jan-farce, kuma ga shi ya kan cutar da wanda a ke maƙa masa abu, ko a ke karɓa daga shi ta hanyar kartarsa da dogwayan farautan su ke yi.
  • Kona Gashi:
Duk da ya ke wasu malamai sun yi rangwame a kan gyaran gashi na zamani, amma ya na da kyau a lura da wasu matsalolinsa, kamar haka:
  • Ya kan zamewa mace laura, ya zama dole a ci gaba da yinsa yadda in a ka daina sai ya jawo zubewar gashi.
  • Ya kan zama fitina, domin idan matce ta yi ƙunan gashi ya yi kyau, sai a dinga ƙoƙarin yadda za a yi ta fito da shi waje don a gani. Saboda haka, ya kamata Musulma ta keɓe maigidanta da wannan gyaran gashin. Kuma ta auna ta gani, shin ba zai cutar da ita ba?
Wannan bayanin anciro shi ne daga littafin “Sutura Da Kwalliyar Mata” Domin karanta cikakken littafin ko daukoshi  Danna nan
labarin da ya wuceYadda Ɗabi’un Annabi (S.A.W) Suke
Labarin na GabaYadda Musulmi Zai Ribaci Lokutansa Na Rayuwa
Dr. Aminu Isma'il Sagagi
An haifi Dr. Sagagi a Unguwar Sagagi cikin birnin Kano a 1968 Ya yi PhD a IUA Khartoum 2012 Ya yi aikin koyarwa a Makarantar Munazzama Kura. Ya yi koyarwa a Makarantar koyon Sharia ta Malam Aminu Kano. Ya taba rike Mukamin Mai ba wa Gwamna Shawara a kan Ilimi 2009-2011 A yanzu Malami ne a Sashin Nazarin Addinin Musulinci a Jami'ar Bayero.