Zikiri shi ne ambaton Allah Ta’ala da kalmomin yabo da kirari da girmamawa da godiya; bisa ni’imominsa tare da nutsuwa da ƙasƙantar da kai da nuna gajiyawa; da ƙwadayin rahamarsa da neman tsari daga azabarsa.
Zikiri kalma ce mai faɗi wacce ta ƙunshi ambaton Allah da harshe da biyayya a gare shi da gaɓoɓi; da kuma sanya Allah Ta’ala a cikin zuciya ta hanyar tunani kan ni’imominsa da falalarsa ga bayinsa da ƙoƙararin fahimtar hukunce- hukuncen addininsa da ma’anonin littafinsa.
A kan haka za mu fahimci zikiri yana da nau’o’i daban-daban wanda ya ƙunshi karatun alƙur’ani, ibadu; zikiran safe da yamma, zikiran lokuta da halaye daban-daban, karatun ilimin addinin musulunci; da kuma dukkanin wani nau’i na zikiran harshe kamar hailala, salati ga Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasalam) Istigfari, Tasbihi, lahaula wala kuwwata illa billahi da sauransu.
Zikiri yana da falala mai ɗimbin yawa, ga kaɗan daga cikin irin waɗannan falala da darajoji:
1- Allah Ta’ala yana yabon masu zikiri a cikn mala’iku.
2- Allah Ta’ala Mala’ikunsa suna yin salati ga masu yin zikiri.
3- Allah yana gafarta zunuban masu zikiri
4- Mai yawan zikiri yana samun taimakon Allah.
5- Zikiri yana sanya nutsuwa da sanyin rai ga mai yinsa.
6- Zikiri yana raya zukata.
7- zikiri yana sanya mutum ya samu kariya da ga wasiwasin shaiɗanu.
8- Zikiri yana sanya a samu alkhairin duniya da lahira.
9- A cikin kowacce ibada akwai zikiri.
10- Allah yana sanya kwarjini da farin jini ga mai zikiri.
Domin karanta cikakken bayani a kan Yadda Falalar Zikiri Bayan Sallar Asuba Har Zuwa Ɓullowar Rana Ya Ke danna nan.
Domin karanta cikakken bayani a kan Yadda Falalar Zikirin Tashi Daga Majalisa Yake danna nan.
Wannan bayanin an ciro shi ne daga littafin Ingantattun Nafiloli Da Falalarsu; Wanda Usman Abubakar (Shehu Mansur Dala) ya wallafa shi; Domin karanta cikakken littafin danna nan.