Barkan mu da sake kasancewa a cikin shirinmu na GIRKE GIRKEN WikiHausa wanda muke koyar da ƙayatattun abincinmu na gida Najeriya da kuma na ƙetare, tare da bayani a kan lafiyarsu cikin harshen Hausa a saukake tare da ni Hafsat Shettimah.
A yau zamu koyar da yadda ake yin daƙuwa ku biyo ni a sannu domin mu koya tare……
Ko kun san daƙuwa abin marmari ce wadda ake sakawa a cikin garar amarya?
Abubuwan Buƙata
- Aya 1 cup
- Gyaɗa ½ cup
- Ƙaramin ½ chokalin barkono
- Ƙaramin ½ chokali citta
- ½ cup sugar ko zuma
- ½ ƙaramin chokalin gishiri
Yadda Ake Haɗawa:
- A tsince aya a wanke ta fita fes sai a shanya
- A gyara gyaɗa a soya ta, ta soyu da kyau
- A soya aya ta soyu sosai sai a kwashe a daka gyaɗa separately ita ayar haka
- A haɗe waje guda sai a zuba kayan ƙamshi
- A zuba zuma sai a turashi.
Domin koyon Yadda ake haɗa hallaka-kwabo danna nan