Moi moi wadda muka fi sani da alala a Hausance ana yinta ne daga wake, alala ta kasance ɗaya daga cikin abincin gargajiya na bahaushe.
Abubuwan da ake buƙata
- Wake
- Taruhu da tattasai
- Albasa
- Maggi
- Tafarnuwa
- Manja
- Sausage
- Ƙwai
- Karas
Yadda ake haɗawa
- Da farko za ki wanke wake a surfa, sai a zuba taruhu da tattasai da albasa a niƙa shi ya yi laushi sosai.
- Sannan a zuba wannan haɗin a cikin bowl a sa manja, maggi, tafarnuwa, da curry, za a iya saka cray fish ma, a juya shi sosai komai ya haɗe.
- A saka mai kaɗan a kan kaskon, a sa sausage da karas a yi stir frying nasu, sai a sauke. A dafa ƙwai a ɓare shi a yanka slices. Shi ma a aje a gefe.
- Za a kunna oven 180° sai a ɗauko parchment paper a shimfiɗa ta a kan faranti na gashi, a zuba ƙullun a saka a oven.
- Bayan mintina 10 in ya fara yi, sai a sauko da shi a zuba fillings ko’ina, a mayar ya gama gasuwa.
- Idan ya yi, za a ji ƙamshin ya haɗe ko’ina a sa toothpick a duba.
- Don a tabbatar ya dahu, a sauke a naɗe kaman naɗin tabarma.
A ɗan bari ya huce sai ki yanka. A ci lafiya.
Domin sanin Yadda Ake Zobo Na Cucumba dannan nan.