KAYAN HAƊI
- Tumbi
- Kitse
- Hanta
- Zuciya – huɗu
- Albasa
- Gishiri da sinadarin ɗanɗano
- Markaɗe
- Tafarnuwa
- Masoro
- Girfa
- Habbahan
Yadda za a haɗa
A sami tumbi da kitse da Hanta da zuciya da huhu da hanji, sai a sami ruwa a tafasa. A ɗauko hanjin, sai a sa wuƙa a kankare shi, sai ya yi haske sai a yayyanka ƙanana, a wanke hanjin sosai a tabbatar ya wanku a tsane.
Sai a sa albasa, mai, gishiri, maggi za a ga ya yi ruwa, sai a sa markaɗe irin na farko, in ruwan ya yi kaɗan a ɗan ƙara a bar shi, ya yi ɗan kauri, sai a ɗauko tafarnuwa a daka da masoro a jefa girfa a ciki da habbahan. A juya in ta yi a sauke.