Da zarar watan azumin ya kama, watan (Ramadan), ‘yan mata su ne masu ko suke gudanar da wannan wasa a ƙarƙashin tallafin ‘yan uwa da abokan arziƙi na danginsu da ma na dangin surukai, har ma da abokan ‘ya’yansu, da samarinsu da abokan samarin, da duk waɗanda suka sani suna da alaƙa da su.
Wannan alaƙa ta ‘yan uwantaka ko kuma ta zaman tare, a ɓangaren cinikayya ko kuma a zaman unguwa ɗaya, mutun ya kan bayar da tallafinsa na gudanar da wannan wasa da zarar watan ya kama na azumi daga dangi na kusa da na nesa.
Yadda ake karɓar wannan tallafi shi ne yarinya za ta yi wanka ta ɗaura atamfa kyakkyawa kamar ranar Sallah, a wannan lokaci tana bin gidajen danginta, tana zuwa gaishe su, inda za ta faɗa musu ta zo karɓar hatsin ƙunshi. Nan take idan wurin da za a yi wasa da dariya ne, sannan a ɗebo abin da ya samu a ba ta.
Waɗansu sukan bayar da gero, ko dawa ko maiwa ko shinkafa ko kaza ko zakara ko ɗan shila. Waɗansu na bayar da zabi waɗansu ƙwai waɗansu kuma sukan bayar da kuɗi da dai sauran abubuwan da mutum yake da halin da zai iya bayarwa. Idan ta haɗa waɗannan kayayyaki ta kammala karɓar tuwon ƙunshi na wannan shekara ke nan.
Abu na gaba, za ta tafi ta ɗauki ‘yar ƙunshi. Ita ‘yar ƙunshi yarinya ce ‘yar ƙarama za ta samu ko ‘yar yayarta ko ‘yar ƙanwarta ko kuma ‘yar uwar ɗakinta, ko kuma ‘yar abokiyar wasanta, ko kuma wata daga cikin dangi. Wannan yarinya ita ce ‘yar ƙunshinta, sai ta sanar da mahaifan yarinya, yarinyar wacce ba ta wuce shekara shida zuwa shekara tara ba (6-9).
Daga wannan lokaci su ma iyayen yarinya ta same su, domin kuwa su ma za su haɗa kayan abinci su ba uwar ɗakin ‘yarsu, daga wannan lokaci wannan yarinya da aka ɗauko wato (‘yar ƙunshi), shi ke nan duk wata ɗawainiyarta, ta koma kan uwar ɗakinta, (wato wannan budurwa).
Wankanta da shanta da cinta, waɗansu ma idan suna da hali har ma tufafinta duk sun koma kan uwar ɗakinta. Wannan nauyi ya ɗoru har lokacin da za a yi auren wannan budurwa. Wannan yarinya ita ce za ta zama ‘yar zaman ɗaki kafin kwana arba’in (40).
Za a saka tabarma ta kaba (turarriya) a yi mata ado mai kyau. Wannan tabarma za a ba wa ‘yar ƙunshi a ce mata ga tabarmarmu ta cin tuwon ƙunshi, saboda haka, wannan yarinya ita ce mai alhakin kula da ita, bayan an kammala waɗannan shirye-shirye. Ga waɗanda suke da hali suna yin sababbin ɗinkuna, waɗanda kuma ba su sami halin hakan ba, sukan sanya tufafinsu kyawawa.
Ita wannan yarinyar za a yi mata ƙunshi tare da uwar ɗakinta kafin lokaci ya rage kwana ɗaya ko biyu. A ranar da ake azumi na ashirin da shida (26), a wannan rana kowace budurwa komai girmanta, ba za ta yi azumi ba, saboda rana ce ta wannan wasa na ƙunshi.
Dangane da waɗancan kayayyakin abinci da kuɗaɗe waɗanda aka samu daga dangi da abokan arzuƙa. A ranar ashirin da shida (26) har zuwa ashirin da takwas ana girke-girke, na alfarma a duk gidan da budurwa take, idan an gama dafa abinci, su yara ƙanana-ƙanana suna shiga gida-gida suna cewa a ba su tuwon ƙunshi, kowanne da kwanonsa, za a karɓa a zuba musu.
Da rana ta yi, za a tafi wani gida da aka ware ko dai gidan wata Amarya a unguwar ko kuma gidan wata mata wadda ta yi fice a wannan unguwa, inda ‘yanmatan suke wasanninsu tare hirarsu a gidan, sai su ce bana a gidan wance za a ci tuwon ƙunshi.
Idan an kammala dafa abinci kowacce ‘yar ƙunshi da aka ɗauko za a ɗora mata wannan tabarma a saka ta a tafi wancan gida da aka ambata a can za a ci tuwon ƙunshi. Kowacce budurwa a nan gidan za ta ɗauko abincinta ta ci. Kuma kowacce zata zo da sabuwar tabarma da aka saƙa ta musamman.
A wancan lokaci yara maza suna zagawa wurin waɗanda suka sani, suna cewa a ba su tuwon ƙunshi, kowanne da kwanonsa. A ɓangaren yarinyar ‘yar ƙunshi a ranar babu abin da za ta yi sai zama da kuma cin abinci wadda take so. Sannan a hannu guda kuma, ita wannan matar gida, ‘yanmata za su zuba abinci a kwano a kai mata.
Haka abubuwan za su ta tafiya tare da kai wa-da-komowa wasu zau tafi dandali wasu kuma bayan gari ya danganta inda suka ga dama har bayan sallar la’asar ana guje-guje da tsalle-tsalle da wasannin gargajiya iri-iri da gata da waƙoƙi da sauran wasanni har zuwa almuru ko kuma faɗuwar rana, sai kuma a dawo wannan gida, kowacce ta rage kuma ta ajiye abincinta haɗi da tabarma ta za a ɗauko sauran abincin a ƙarashe shi, daga nan an gama cin tuwon ƙunshi na ranar farko.
A rana ta biyu (2) wato ranar ashirin da bakwai (27) da kuma ranar ashirin da takwas (28), duk waɗannan wasannin iri ɗaya ne, sai kawai hidimar wata rana tana fin ta wata rana, a nan ake samun bambanci. To idan an yi wannan abinci na ranar ashirin da takwas ga wata (28), wato ranaku uku (3) ke nan ana gudanar da wannan wasa, to shi ke nan an kammala cin tuwon wasan ƙunshi.
Ita kuma ‘yar ƙunshi za a yi mata saye-saye daga gidan su uwar ɗakinta (wadda ta ɗauko ta), sannan ta ɗauke ta mayar da ita wurin iyayenta, shi ke nan wannan ‘yar ƙunshi ta yi uwar ɗaki, shi ke nan duk shekara ta zama ita ce ‘yar ƙunshinta ba wacce za ta ɗauki wannan yarinya sai ita.
Yayin da wannan budurwa ta kawo munzalin ayi mata aure, ita mahaifiyar ‘yar ƙunshi sai ta taka rawar gani a al’amarin auren, idan an yi auren ‘yar ƙunshin da ita za a tafi gidan mijin, sannan a canza mata suna ta koma ‘yar burganci”, ma’ana mai yi wa amarya aikace-aikacen gida, da ayyukan da amaryar nan za ta yi. Wannan ‘yar burganci ita ce mai yi mata hidima kamar share-share da wanke-wanke da duk wani aiki da amarya za ta yi. A nan gidan take kwana take tashi, har kwana arba’in.
Game da azumin da ba a yi ba wato suka sha ya tafi shi ke nan, sannan kuma sauran azumi guda biyu (2) ko ɗaya (1) ba kowace budurwa rama shi ba ko kuma take ƙara yinsa ba, da yawa ba sa ramawa, wasu kuma sukan ƙara har zuwa ashirin da tara ko talatin (30) ya danganta da yadda aka yi a wannan shekarar, ashirin da tara (29) ko talatin (30).
Wanan bayanin an ciro shi ne daga maƙala mai taken Nazarin Wasan Ƙunshi Jiya Da Yau A Ƙasar Gaya wadda Magaji Ahmad Gaya Ph.D Sashen koyar da Hausa Jami’ar Northwest, Kano ya wallafa.
Emai: magaya@nwu.edu.ng
0806600903
Danna nan don karanta Bukukuwa Da Wasanni Da Nishadi Na Bahaushe
Edita@rumasau-kallamu










