Abubuwan haɗawa
- Fulawa kofi huɗu (4 cups)
- Kwai 15 (ya danganta da irin girmansu)
- Butter 2 (simas leda 2)
- Baking powder ƙaramin cokali huɗu (4tsp)
- Filebo ƙaramin cokali uku
- kwakwa (na yi amfani da na kwali ɗan ƙanti)
- Suga kofi biyu (ko kofi biyu da rabi)
Yadda ake haɗawa
1. Da farko, ki tankaɗe fulawarki tare da baking powder, sai ki ajiye a gefe.
2. Ki sami mixer machine, ki sa butterki a cikin wannan kwanon mixer, (ko ki sami wani kwano daban, idan da hand mixer za ki yi).
3. Ki yi ta motsa shi na ɗan wani lokaci.
4. Sannan ki kawo suga ki sa a ciki, ki yi ta motsa shi har sai suganki ya narke a ciki (ba kya jin gudajin sugar a cikin butter).
5. Sai kuma ki ɗauko ƙwai ki fasa, ki yi ta motsa shi (Ƙwan ana so ana sa shi ne ɗaya bayan ɗaya, kuma ana motsa shi bayan kowane sa ƙwai da aka yi) har ki gama da ƙwanki.
6. Sai ki ɗauko vanilla filebo ki sa ki motsa.
7. Ki ɗauko fulawarki da kika tankaɗe tare da baking powder (za ki iya raba filawar gida shida) ki rinƙa zubawa a hankali a cikin wannan haɗin butter, har ki gama da flour kina motsa shi.
8. Bayan kin gama zuba filawarki, sai ki ɗauko bushasshen kwakwa, ki zuba ciki ki motsa. Sai ki ɗauko abin gashin (nakan sa takardar gashi a cikin abin gashin kafin na zuba kwallin cake nawa).
9. Ki zuba haɗin kwalli ki a cikin kowace takardar gashi (ba a so a cika shi don kar ya zube a lokacin gashi. Sannan ki sa su rabi-rabi ko ya ɗan fi rabi da kaɗan don ya yi gashi mai kyau).
10. Sai ki sa a cikin magasa (preheated oven) ki gasa, har sai ya gasu. (ko idan kin sa tsinke ya fito ba tare da komai a jikin sa ba) sai ki cire ki bari yasha iska.
A ci daɗi lafiya.
Ku karanta Yadda Ake Haɗa Sinasir