Mai yin sallah zai buɗe karatun Alƙur’ani da BismillAh aɓoye ba tare da mamu sun ji karatun BismillAh ba shine limami kuma sallah ce da ake bayyana karatu,a mazhabin malikiya kuma zai bayyana karatun BismillAh ne a fili,zai karanta fatiha sannan ya sake yin wata BismillAh kafin ya karanta surar gaba.
Zai tsaya ne ya ɗora hannun sa na dama akan hannun sa na hagu akan ƙirjin sa ko kasan ƙirjin sa saman cibiyar sa,ya ɗora idanun sa biyu a dai-dai inda yake sujuda kuma ya bar idanun sa abuɗe ba tare da lumshe su ko rufe su ba domin rage yawan tunani da zancen zuci a cikin sallah.zai karanta surah ko wani yanki na surah ko wasu ayoyi gwargwadon abinda Allah ya sanar da shi na Alƙur’ani yana tsaye.
Domin karanta cikakken bayani akan Mafifitan Aiyukan Mai Azumi danna nan.
Yana iya fasa karanta surah ko ya canza surah idan yaji ya kakare ko kuma ta ɗauke a cikin ƙwaƙwalwar sa ko ya rasa mai tuna masa ko bai rasa ba, yana iya karanta aya ɗaya koda ba mai tsayi bace, wajan karatu ya kula da haƙɗin mamu kar ya tsawwala musu wajan karanta surori masu tsayi ko yawa idan yana limanci idan shi kadai ne ya tsawaita yadda yaso
Domin karanta Halayen Da Ya Kamata Mai Azumi Ya Siffantu Da Su Danna nan