Barkan mu da kasancewa a fannin girke-girkenmu na WikiHausa, za mu koyi yadda ake bread-egg toast. Tare da ni Hafsat Shettimah.
Abubuwan haɗawa:
- Bread (na alkama)
- Ƙwai
- Gishiri
- Pepper (yaji)
- Mai
Yadda ake haɗawa:
- Da farko Uwar gida za ki fasa ƙwanki, sai ki sa ɗan gishiri da yaji, sai ki kaɗa.
- Ki tsoma bread ɗin a cikin ƙwai, sannan ki ɗora pan ɗinki mara zurfi, sai ki shafa mai da tissue paper ba a so mai ya yi yawa. Idan ya yi, sai ki juya ɗayan gefen, haka za ki ta yi har ki gama.
- A sha da lemo ko shayi ko kuma a saka a lunch box ɗin yara na makaranta.
Domin koyan Yadda Ake Rainbow Cake Doughnut Sabon Salo danna koren rubutu nan