Ina farawa da sunan Allah mai rahma, kuma mai jinƙai, Wanda yake ara min iko da har dubun nan bayinsa suke karanta rubuce-rubucena a kafar sadarwa ta zamani.
Yakan ba ni iko ne ba wai don na isa ba, ko kuma na kai ba, sai domin ya nunawa al’umma ayarsa ta halittar ƙwaƙwalwa a kaina, mai fitar da abin da ake mamakin fitar sa, sarki ɗaya tilo wanda bashi da kishiya.
A karon farko wannan ne rubutuna da harshen Hausa a maimakon da can da nake yi da harshen Bature wato Ingilishi, na yi hakan ne domin iyayenmu mata su samu sauƙin fahimtar saƙon da nake son isarwa a kan ‘ya’yansu mata
Ina mai amfani da wannan dama, domin nusar da iyaye mata da su ƙara zage damtse a kan yadda suke, su saka ido a kan rayuwar ‘ya’yansu ta yau da gobe, abubuwa suna faruwa sosai wanda kuma wani lokacin ƙawayen ‘ya’yan ne sanadi.
Ciwon ‘ya mace na ‘ya mace ne, Kai a waye ya kamata ki kira ‘yarki, ku zauna daga ke sai ita, ki ci gaba da ba ta shawarwari a kan ta kiyaye mutuncinta da kuma mutuncin gidan da ta fito, saboda tarwatsewar tarbiyyarta daidai yake da taɓarɓarewar al’umma baki ɗaya, kamar yanda Annabi S.A.W ya faɗa a cikin hadisi “…Idan mace ɗaya ta lalace, to al’umma ce gaba ɗaya ta lalace”.
A matsayina na ɗalibi a Jami’ar Bayero ta Kano, a da can na ga yadda kowa yake tafiyar da rayuwarsa a kan tafarkin da iyayensa suka ɗora shi, kenan ya zamo babban nauyi ne, da Allah ya ɗora wa iyaye mata wanda ya kamata su jajirce domin ganin sun sauke wannan nauyi wanda ya rataya a wuyansu.
Akwai wani lokaci ba zan taɓa mantawa ba, ina zaune a makaranta wani bawan Allah wanda ba zan kama sunansa ba, ya zo ya same ni, ya ce, “Shi fa babu abin da ya tsana sama da ya ga ina rubutun fadakarwa a kan abubuwan dake faruwa a Jami’a”. Na kawo wannan magana ce ba wai don na ci masa mutunci ba sai dai domin na kafa hujja da cewar abubuwan dake faruwa a Jami’a sai an sa ido sosai kuma an dage da addu’a domin gudun da-na-sani)
Za ka ga yarinya ta taso daga gidan mutunci da kamala, amman a sanadin haɗuwa da ƙawa mai son abin duniya, za ka ga ta zubar da mutuncinta, wannan abin kunya ne kam, a maimakon kiyaye mutuncinta, saboda kunnen ƙashi sai kawai ta siyar da shi a kan farashi mai rahusa, sun manta da Suratul Maryam aya ta 86
Inda Allah (S.W.T) yake cewa “Kuma muna kora masu laifi zuwa jahannama, gargadawa {Wanasuqul majrimina ila jahannama wirda}”…Bayan wannan kuma akwai inda Allah S.W.T yake faɗa wa Annabi (S.A.W) a cikin Suratul Maryam Aya ta 83 cewar “Shin ba ka gani ba cewa mun saki shaiɗanu a kan kafirai suna susuta su ga masu zunubi, susutawa?
Ma’ana idan shaiɗanu sun ga mai wa’azin gaskiya, sai su dinga susuta mabiyansu domin su yi faɗa da mai wa’azin, domin kada su saurare shi, har su gane ɓatan su, Shaiɗan shi ne mai ɓatar da wani mutum ne ko aljan.
Shekara ɗaya da ta gabata, wani bawan Allah wanda ba zan kama sunan shi ba, ya zo har inda nake, ya zazzage ni, na tambaye shi ko mene ne dalilin zagina da ya yi? Kun san me yace min kuwa? Wai akwai wata yarinya wadda suka yi da ita cewar za su haɗu, su je yawon ashararanci tare, sai kawai ya ji ta kirasa a waya, ta ce masa “Ya hau WhatsApp”. Hawansa ke da wuya, sai kawai ta tura masa wani rubutuna da nake magana a kan hukuncin aikata zina, nan take ya kira ta a waya ya ce mata, “Na gani, sai akai yaya?” sai ta ce masa, “Sai mu daina aikata aikin haram”.
Ya ji haushin abin matuƙa a lokacin, amman cikin ikon Allah sai ban neme shi da rigima ba, na ba shi shawarwari a nutse, to yanzun haka dai bawan Allan nan shima, ya tuba ya daina abin da yake yi, Allah gafurur Raheem ne, ya kamata iyaye su zaunar da ‘ya’yansu mata, su tuba kafin su koma gare shi.
A game da rubuce-rubucen faɗakarwa, an sha zuwa har inda nake, an ci mun mutunci kawai, saboda faɗin gaskiya, amman ba na damuwa samsam idan na tuno da aya ta 84 a cikin dai Suratul Maryam: