Waiwaye Kan Tattalin Arzikin Hausawa Na Gargajiya

0
20

TUNA BAYA SHI NE ROKO: WAIWAYE KAN TATTALIN ARZIKIN HAUSAWA NA GARGAJIYA

DAGA

Kabiru Abdulkarim

Kabiruabdulkarim996@gmail.com  08034510967

Da

HauwaMuhammadMaikudi

hawwammaikudi@gmail.com  08098191994

School of Languages,

Kano State College of Education and Preliminary Studies.

Takardar da aka gabatar a Bikin Taron Ranar Hausa ta Duniya a Kwalejin Ilimi da Share Fagen Shiga Jami’a Ta Kanoa ranar Talata 26 ga Agusta, 2025.

 TSAKURE

Hausawa kan ce “Waiwaye adon tafiya”. Wannan takarda ta yi waiwaye ne a kan tattalin arziƙin Hausawa na gargajiya domin abin nan da Bahaushe ke cewa “Tuna baya shi ne roƙo”. An yi nazarin sana’o’in gargajiya na Hausa, saboda su ne ginshiƙan rayuwa da tattalin arziƙin yau da kullum na Hausawa (Garba 1991:1).

Takardar ta gano cewa watsi da aka yi da waɗannan sana’o’i  namu na gargajiya, shi ya jefa mu cikin wannan hali na ƙaƙa-ni-ka-yi da matsin tattalin arziki da muke fama da shi a halin yanzu. Sannan an kawo shawarwari da ake ganin za su iya taimakawa sosai wajen rage wannan raɗaɗi da ake ciki da kuma mawuyacin hali da matasannmu suka tsunduma kansu a ciki na shan miyagun ƙwayoyi da ƙwacen waya da kuma faɗan daba.

Gabatarwa

An shirya wannan takarda ne da nufin yin waiwaye kan tattalin arziƙin Hausawa na gargajiya, ba don komai ba sai don a waiwaya a kuma gyara halayyar da Hausawa suka ɗauka a halin yanzu na watsi da sana’o’inmu na gargajiya, muka koma bilayi da bilinbituwar neman arziƙi ta wasu hanyoyi da ba su dace da mu ba, sannan kuma suke wahalar da mu, har suka ke neman kai Hausawa ƙasa warwas.

Bahaushe a da ba shi da wani abin da ya sanya a gaba sai sana’a, wato neman na kansa. Amma a halin yanzu an bar sana’a an koma neman wasu hanyoyi da za a azurta kai da gaggawa, kuma arziƙin ya ƙi samuwa. An koma ba mu ga tsuntsu ba mu ga tarko. Bahaushe yana cewa “Sana’a Sa’a, kuma rashin sana’a Sata” (Mu’azu da Satatima 2013:61).

Daga nan za mu fahimci cewa lallai Hausawa na wannan zamani, musamman matasa an doshi hanyar rugujewar al’umma. Don haka,  ya zama wajibi a koma ga sana’o’inmu na gargajiya domin ita ce kaɗai hanya mai ɓillewa wadda kuma ba ta da tangarɗa.

Wannan tattalin arziƙi da muke magana a gargajiyance ya ƙunshi hanyoyin da Hausawa suka bi a dauri, suka zauna cikin ƙoshin lafiya da kwanciyar hankali da wanzuwar arziƙi, har ya kasance sun zama abin koyi da kuma ban sha’awa a idon duniya.

Hausawa dai su ne al’ummar nan waɗanda harshen Hausa shi ne harshensu, kuma al’adunsu da ɗabi’unsu suka yi kama da na addinin Musulunci (Zarruq 1992:2). Gargajiya kuma tana nufin hanyoyin da aka saba bi na rayuwa. A nan gargajiyar Bahaushe ta kasu gida biyu: (a) kafin zuwan Musulunci da kuma (b) bayan zuwan Musulunci.

  • Kafin zuwan Musulunci: A nan ana nufin duka abubuwan da Hausawa suka saba yi na rayuwa tun daga farkon samuwarsu , wato lokacin Maguzanci har zuwa lokacin da suka haɗu da Larabawa.
  • Bayan zuwan Musulunci: Addinin Musulunci ya zo ƙarsar Hausa a tsakiyar ƙarni na sha huɗu zamanin Sarkin Kano Aliyu Yaji (1349-80), (Maiyama 2008:40-41), kimanin shekaru 676 da suka gabata. Bayan zuwan Musulunci Hausawa sun karvi addinin hannu bi-biyu. Dukkanin wasu kyawawan halaye da ɗabi’u sai suka cigaba da su, amma duk wasu abubuwa da suka ci karo da koyarwa da tarbiyyar addinin Musulunci sai suka yi watsi da su. Dalilin daɗewar musuluncin a ƙasar Hausa, sai ya sanya su ma al’adun da aka samu daga Larabawa, sai suka zama gargajiyar Bahaushe.
  • Lokacin zuwan Turawa(zamani):Zuwan Turawa tare da mulkin mallaka shi ne ake kira zamani. Turawa sun karɓe ikon ƙasar Hausa a 1903. Don haka duk wani abu da ya samu bayan zuwan Turawa ƙasar Hausa, to shi ba gargajiyar Bahaushe ba ne ya zama na zamani ke nan.

Togaciya: Wannan takarda ta yi togaciya kan abubuwa kamar haka:

  • Akwai sana’o’i da dama da takardar ba ta dube su ko nazarce su ba, domin an tsara wasu Makarantu ko Kwalejoji  za su gabatar da su a wannan taro na ranar Hausa ta Duniya. Sana’o’in sun haɗa da Saƙa, Sassaƙa, Koli, Ƙira (babbaƙu), Dillanci da sauransu.
  • Akwai wasu sana’o’in da ko dai Hausawa na tababarsu cikin sahihancinsu kamar roƙo da raraka da tsibbu da makamantansu, takardar ba ta dube su ba. Haka sana’ar ƙunshi da wasu ke kallonta a gargajiyance kamar ba sana’a ba ce wato kwalliya ce, daga baya ne zamani ya ba ta gurbi ta zama cikakkiyar sana’a kuma mai gwaɓi.
  • Sana’o’in da takardar ta yi bayani, ana so ne a kafa hujja ko buga misali da su, ba wai su kaɗai ne suka fi sauran muhimmanci ba.
  • Wasu sana’o’in kuma an haƙura ba a kawo su ba saboda yanayin lokaci da gudun ka da abin ya yi yawa wai “shege da hauka”, misali Arkomi,da Asako,da Kiri,da Bugu,daAikatau wato Dakau,da Sirfau,da Niƙau da makamantansu.

SANA’A

Garba (1991:1) ya dubi sana’a da cewar ita ce ginshiƙin rayuwa da tattalin arziƙin yau da kullum na Hausawa tare kuma da ɗaya daga cikin muhimman manyan hanyoyin gano martabar mutum da ƙasaitarsa da matsayinsa cikin al’umma. Watau ban da noma wadda take ruwan dare, Hausawa suna kuma ƙara wa kansu wata sana’a wadda da rani ana samun abinci ta hanyarta, har ma ko da daminar akan taɓa wasu sana’o’i ƙari a kan noma.

Umar (1983) a cikin D/Iya (2006:1) ya bayyana sana’a da cewa; “wata hanya ce da ɗan Adam kan ta’allaƙa a kanta domin samin abin masarufi wadda ta shafi sha’anin kasuwanci, wato sha’ani na saye da sayarwa”. Ya ci gaba da cewa; “sana’o’in suna da babban matsayi a al’adun kowacce al’umma”. Ga Bahaushe su ne ƙashin bayan tattalin arziƙinsa.

A nan sana’a ta zo da sigogin ma’ana, akwai zaɓaɓɓun lokuta da yanayi ke tabbatar da sana’a. Wannan ya yi dai dai da azancin da ke cewa lokacin abu a yi shi. Ma’ana kowace sana’a da lokacin yinta, wannan yana haska yadda Al’ummar Hausawa suke da abin yi rani da damina, dare da rana, mace da namiji, yaro da babba. Haka shi yake nuna ba sa zaman kashe wando  koyaushe akwai abin yi.

Rabe-raben Sana’a

Masana da dama sun yi ƙoƙarin bayyana ko tsara sana’o’in Hausawa bisa kashi-kashi dangane da ra’ayoyinsu da fahimtarsu.

Yahya da Ɗangambo (1986:173-174) sun tsara rabon sana’o’i zuwa gida uku. Sana’ar noma, da sana’ar sarrafa wani abu domin samar da wani abu. Misali ƙarfe-ƙira; zare – saƙa; fata – dukanci; sai sana’ar sarrafa jari da ƙwarewa, misali, kasuwanci, da gini, da tallau, da sauransu.

Haka kuma Yahya (1992:4) su ma a cikin littafin sun raba sana’o’i zuwa gida uku inda suka tsara sana’o’i na noma da kasuwanci da waɗanda suke dafe-dafe.

Ragowar rabe-raben sana’o’in na Hausawa, su ne rabo ta ɓangaren jinsi, ma’ana an raba sana’o’in a ɓangaren jinsi zuwa gida uku, jinsin maza da jinsin mata da kuma na tarayya. Abin nufi a nan shi ne, bisa ƙa’idojin al’adun Hausawa, ba kowacce sana’a kowa yake yi ba, a a kowace da mai yinta, waɗansu na mata ne, waɗansu na maza ne, waɗansu kuma kowane jinsi na iya aiwatar da su. Misali:

Na maza Na mata Na tarayya

Ƙira (babbaƙu) kitso saƙa

Dukanci sussuƙa ƙira (farfaro)

Jima dafe-dafe d.s dillanci

rini aikatau

wanzanci, da makamantansu.

Noma

Noma tushen arziki,

Noma na duƙe tsohon ciniki,

kowa ya zo duniya kai ya tarar.

A bisa tsarin gargajiya, noman nan shi ne tushen rayuwa, domin ta nan ne ake samar da abinci da kuma bunƙasar tattalin arzikin al’umma. Burin kowanne magidanci ne ya noma isassahen abincin da zai ci da iyalinsa tsawon shekara. Haka kuma dole ne akwai buƙatar a noma abin sayarwa irin su auduga da gyaɗa don samun ‘yan kuɗin biyan buƙatun rayuwa. Haka kuma sana’ar noma ta haifar da wasu sana’o’i musamman na abinci daban-daban.

Al’adar sana’ar noma ta yi wa rayuwar Bahaushe riga da wando, har ma da hula da takalmi. Bayan wadatuwa da abinci da abin masarufi, noman nan ya hana Bahaushe ragwanci da zaman kashe–wando. Ya tsare masa gabas da yamma ta fuskar cikar mutunci da kwarjini da cancanta ta kowace fuska. Don haka sana’ar  noma ta haifar da wasu sana’o’i irin su kiwo da saƙa da kaɗi da akasari sana’ar abinci da mata kan aiwatar daga cikin gida.

Fawa

Maza na Sarkin fawa,

Kuna yawa ana rage gona,

Fawa ko ta kwana ta fi tallan ƙosai,

Sarkin fawa rikici gado,

Kaɗauki bashi ka biya bashi,

Na Inna kashin shanu,

Hankaka mai da ɗan wani naka,

Bungare mai billen ‘yanci,

Na kulluru mayen ɗanye,

Maƙiyinki ya dama fura ya fasa.

Fawa sana’a ce ta yanka dabba a feɗe ta, a yanka ta gunduwa-gunduwa, tsoka-tsoka domin sayarwa ta yadda za a iya amfani da naman yadda ake sonsa. Ana iya sayar da shi a ɗanyensa, ko a gasa, wato tsire ko balangu ko kilishi da makamantansu.

Farauta

Gwarzon daji,

Mai tsare ƙauyuka,

Barde mai tsaron daji,

Wanda baya tsoron daji,

Masanin dabarun naman daji,

Kai ne mai kawo tsoron-tsoro.

Farauta ita ce sana”a

Su

Mai su uwar ɗaka.

Wanda ke kawo ɗanɗano ga abinci,

Mai ba wa duniya ƙanshin ƙanshi,

Ɗawisu na alheri,

Mai zuba wa rayuwa ɗanɗano.

Su sana’a ce ta kamun kifi, musamman ga waɗanda suke zaune a gefen ruwa. Sana’a ce da ake kama kifi don ci ko don sayarwa.

Jima

Romon Jaɓa,

Mai yi wa saurayi aure,

Mai sai wa saurayi wando,

Mai kula da lafiyar mutane

Jima hannun magani,

Ka sha baƙar wahala don farar fata,

Ka zama ma ji ɗaukar alhini.

Jima sana’a ce da ake tusarrufi da fata. Jima dai ita ce sana’ar sulluɓe fata don fitar da gashin da ke jikinta (Alhassan da wasu,1980:43) Jima tsohuwar sana’a ce a ƙasar Hausa da har yau take cin ganiyarta. Kamar yadda Alhaji Sule Garo, shugaban masu Masana’antun jima na zamani, ya faɗa a wata hira da aka yi da shi (a Radiyo France International,R.F.I.ranar Litinin,17 ga watan Augusta,2009 da misalin ƙarfe 3:17 na yamma), cewa ya yi duk da shigowar zamani, har yanzu sana’ar jima ta gargajiya tana da tasiri. Domin kamar yadda ya faɗa, su kamfanonin sarrafa fatar sun fi buƙatar waɗanda aka jeme su a gargajiyance don haka ma sukan yi masu ƙima ta musamman wajen saya (Ɓatagarawa 2013: 328).

Rini

Baban dubu mai kamu,

Kowane ganye ya ruɓe ya lalace,

Amma ban da kai na Sarkin Marina,

Katsi katse tsiya,

Toka takore tsiya na Makaman Marina,

Kowa ya bar ka gidansa a sha lami.

Rini kuwa sana’a ce ta gargajiya da ta shafi canza launin tufa ko zare daga fari ya koma wata kala daban. Wajen rini ana amfani da abubuwa irin su muciya da kwatarniya da guga da itace da baba da katsi da shuni da tukunyar baba da ruwa da sauransu

Rini, sana’a ce ta gargajiya da a waɗansu wurare a ƙasar Hausa, har yanzu ana ado da ita. Duk da cewa an sami hanyoyi da dama na zamani inda ake amfani da launuka iri daban–daban, amma duk da haka har yanzu ana ba wa sana’ar ƙima  daraja ta musamman.

Wanzanci

Kala-kala magani gizo Ɗan Wanzam,

Aska na cikin kube tana cin gashi,

Ka ci gashi ka sha jini na Magaji Aska,

Kai wa Sarki rotse ka tashi da martaba.

Wanzanci sana’a ce da ake yin amfani da aska da ƙaho da tankolo da ƙugiya wajen aiwatar da ita. Masu wannan sana’a wato wanzamai suna tallafa wa rayuwar al’umma ta fuskar aiwatar da abubuwa kamar aski da ƙaho da kaciya (shayi ko kugunu) da tsagar anfill da shasshawa da cire beli ko hakin wuya da makamantansu.

Ɗinki

Ɗinki sana’a ce da ake amfani da zare a samar da sutura ingantacciya, yalwatacciya kuma kyakkyawa. Ɗinki hikima ce ta yin amfani da sililin zare, tare da allura a riƙa haɗa geffan kyallayen yadudduka a samar da tufafi ga maza da mata. Ɗinki ya rabu gida biyu wato ɗinkin tufafi da kuma ɗinkin huluna.

Ƙira

Huntu ubangijin mai riga.

Ƙira sana’a ce mai dangantaka da ma’adanai da tsirrai da dabbobi. Sana’a ce da ake sarrafa ƙarfe da itace don samar da ma’aikaci. Ita ma wannan sana’a a iya cewa tana daga cikin sana’o’in farko-farko ma’ana tun lokacin da ɗan Adam ya fara zama wuri ɗaya. Ƙira ta zama tamkar uwa ma ba da mama a wurin sauran sana’o’i domin maƙeri ne yake samar masu kayan aikin sana’ar su.

Sana’ar ƙira ta kasu gida biyu. wato maƙeran fari, da kuma maƙeran baƙi. Maƙeran fari su ne masu ƙera abubuwa dangin farin ƙarfe da azurfa da zinare da makamantansu. Su kuma maƙera baƙi su ne suke sarrafa  baƙin ƙarfe  dangin tama da tagulla.

Ta hanyar ƙira ake samar da abubuwan amfani (ma’aikaci) irin su wuƙaƙe da gatura da adduna da faretani, da kuma makamai irin su takubba da masu da da kibiyoyi da makamantansu. Ka ga wannan ba ƙaramin tasiri suke da shi ba ta fuskar tattalin arziki da kuma harkokin tsaro a gargajiyance.

Fatauci

Fatauci sana’a ce da ta danganci kasuwanci. Akan bar gari a tafi wani garin domin kai haja can, sannan kuma a sayo wata a kawo gida. Masu wannan sana’a ana kiransa fatake. Da wannan sana’a ta fatauci Hausawa suka shahara a idon duniya. Sukan ɗauki kaya (haja) kamar fata da gyaɗa da auduga su kai sauran sassa na kudancin ƙasar nan ko ƙasashen ƙetare su sayo wasu kayan da ba a samunsu a ƙasar Hausa.

Sukan ya-da zango a wasu garuruwa. Wanda a halin yanzu waɗannan wurare suka zama mallakin Hausawa a wajen ƙasar Hausa misali Zango ta Gwanja a ƙasar Ghana in da daga nan ne ake kawo goro zuwa ƙasar Hausa.

Gini

Gini sana’a ceta sarrafa abubuwa don samar da muhalli, daɗaɗɗiyar sana’a ce a ƙasar Hausa. Hasali ma dai a iya cewa ga al’ada kowa magini ne. Ma’ana ko da dai ba a nuna ƙwarewa ba to a ƙalla kowa yana iya sarrafa ƙasa, ko laka don yin gini. Waɗanda suka ƙware, sukan maishe ta sana’a, kuma su ake cewa magina. Magina sun kasu kashi biyu, akwai magina na ƙasa ko laka (siminti a zamanance) da suke sarrafa ƙasa don samar da muhalli.

A ɗaya ɓangaren kuma akwai magina na yumɓu, waɗanda suke sarrafa yumɓu su samar da abubuwa irin su tukwane da kasake da murahu (amare) da tuluna da asusu da butoci da mazubai iri daban-daban. Akwai ire-iren waɗannan magina masu tarin yawa a ƙasar Hausa, kuma sun taka muhimmiyar rawa wajen baza harshe da al’adun Hausawa a wurare daban-daban ciki da wajen ƙasar Hausa. Adamu (1978:34).

Matsayin Sana’a Wajen Bunƙasa Tattalin Arziƙin Hausawa:

Ma’anar Tattalin Arziki

Tattalin arziki shi ne yadda al’umma ke samar da abin da take buƙata da yadda take sarrafa shi, da amfani da albarkatun ƙasa domin samun ci gaba da walwala da biyan bukatunsu na yau da kullum.

Ibrahim (2010) ya bayyana ma’anar tattalin arziki da cewa: “Tattalin arziki shi ne tsarin da al’umma ke bi wajen samar da abin da take buƙata daga albarkatun da ke hannunta da kuma yadda take sarrafa su.”

Bunza (2002) ya bayyana cewa, “Tattalin arziki shi ne yadda al’umma ke tsara rayuwarta ta hanyar albarkatun da take da su, domin ci gaba, zaman lafiya da kuma walwala.”

 Bunƙasar Tattalin Arziƙin Hausawa

Tattalin arzikin Hausawa ya bunƙasa sakamakon waɗannan sana’o’i da suke gudanarwa. Babu shakka Hausawa sun tsaya tare da jajircewa da bin wasu hanyoyi da ƙarfafa wa juna domin ganin tattalin arzikinsu ya bunƙasa daga waɗannan sana’o’i.

Saboda irin jajircewar da suke yi a kan sana’o’insu har sai da ya zamo sun yi fice a fuskar noma ta inda suke noma, wannan ba ƙaramin bunƙasa tattalin arziƙinsu ya yi ba a wancan lokaci. Daga cikin hanyoyin da suka taimaka wajen bunƙasa wannan tattalin arziƙi sun haɗa da:

Yadda wasu sana’o’in suke haifar da wasu sana’o’in: Ta hanyar haifuwar wasu sana’o’in a dalilin wasu, tattalin arzikin Hausawa ya bunƙasa matuƙa. Hakan na faruwa ne sakamakon duk lokacin da aka fari wani abu na sana’a to babu shakka za a samu majuɓunta a kan abin da suke samarwa.

Wannan zai haifar da samun kuɗi ga masu wannan sana’a kai tsaye da ma sauran al’umma baki ɗaya. Misali Sana’ar noma, ta haifar da sa sana’o’i irin su kasuwanci, fatauci, ban gishiri na ba ka manda da nakamantansu.

  • Kiwo ya haifar da sana’ar fawa.
  • Fawa ta haifar da sana’ar jima.
  • Jima ta haifar da sana’ar dukanci.
  • Sana’ar kaɗi ta haifar da sana’ar saƙa da rini.
  • Saƙa ta haifar da sana’ar ɗinki.

Bayan wannan akwai Sana’o’in da yawa da suka haifar da wasu sana’o’in, hakan ba ƙaramin bunƙasa tattalin arziƙin Hausawa ya yi ba.

Samar da kayayyakin da suke na buƙatu a matakin farko: Yawa-yawan kayan da Sana’o’in suke samarwa, kaya ne da ake buƙatar su ko ma a ce suka zama dole a mallake su. Hakan ya sa da zarar an samar da su da an saye su (ga waɗanda ake ƙirƙira ko samarwa) Haka abun yake ga sana’o’i na hidima irin su aski, kitso da makamantansu. Ƙarin bayani a nan, a zamanin da Hausawa ba su fiya ɗora kansu a sana’o’i na jin daɗin rayuwa ba da suke haifar da almubazzaranci da rashin adani ba.

Hanyoyin Bunƙasa Tattalin Arziƙin Hausawa

Akwai hanyoyi da dama waɗanda suke taimaka wa Hausawa wajen bunƙasar tattalin arziƙi. Kaɗan daga ciki sun hada da:

Gado: A da mutane suna gadar sana’o’i da suke yi ne daga magabatansu (gida). Wannan ya sa da wuya ka samu wanda yake ba shi da sana’ar yi, don kuwa mutum tun yana ƙarami yake koyan sana’ar da ya gani ana yi a gidansu. Hakan kan sanya ƙwarewa da kishin sana’ar ga masu yin ta. A dalilin haka da wuya ka ga mai zaman banza a wancan lokaci. Wannan ya sa kowa yana da abin yi, kuma tattalin arziƙin al’umma ya daɗa bunƙasa.

Ban gishiri na ba ka manda: Wannan wani kasuwanci ne da ake yi ba da kuɗi ba. Ana yin sa ne ta hanyar musaya na abubuwan buƙata. Misali manomi zai iya ɗaukar hatsinsa ya kai wa mai fawa don ya ba shi nama. Ko ya ba wa wanzami don ya yi masa aski. Wannan shi ake kira da ban gishiri na ba ka manda . Haƙiƙa wannan ya taimaka wajen bunƙasa tattalin arziƙin Hausawa domin kuwa babu yadda za a yi kana da sana’ar ka ka rasa wani abu da kake buƙata ko da kuwa ba ka da kuɗin saye.

Kiwo: Kiwo sana’a ce mai sirrin gaske ga al’ummar Hausawa. Ga mata har ma mazan a da ba a rasa su da yin kiwo. Idan biki ya taso ko haihuwa ko wata buƙata, mutum kan kama wata dabba tasa ya je ya sayar ya samu kuɗin biyan bukata nan take. Baya ga wannan, a lokacin da ake ciyar da dabbobi ciyawa akan zuba a ƙasa, to duk lokacin da dabbobin suka yi kashi, kashin kan haɗe da ragowar ciyawar da suka ci suka rage.

Idan sun ruɓe sai su ba da takin noma. Irin wannan taki ya fi ba da albarkar noma da lafiya ga abin da aka shuka a gonar da aka zuba shi. Wannan ba ƙaramin kawo bunƙasar tattalin arziki ya yi ba a zamanin da, musamman idan an kwatanta shi da zamanin yanzu da ake sayen taki da tsada.

Haɗin kai da tallafa wa juna: Yanayin yadda Hausawa suke aiwatar da sana’o’insu ya taimaka musu matuƙa wajen ƙara hada kawunansu. A sanadiyyar haka ya zamo akwai taimakon juna a duk lokacin da buƙatar hakan ta taso. Misali ko ba ka da jari za ka samu aron kayan aiki daga ‘yan’uwa ko abokan arziƙi don gudanar da sana’arka. Wannan shi ma ba ƙaramin taimaka musu ya yi ba wajen bunƙasa tattalin arziƙinsu.

Mafi yawan masu sana’oi’n nan, suna ba da taimakon magunguna a cikin sana’o’in nasu, wannan yana ƙara masu kuɗaɗen shiga, kuma ya ƙara bunƙasa tattalin arziƙinsu. Misali manoma ne ke bayar da maganin ciwon baya da maganin rana.

Haka kuma maƙera ne suke ba da maganin ƙunar wuta. Su kuma marina ana samun maganin lalurar fata kamar ƙyasbi da  ƙurajen bar- ni-da-mugu da katsi ga masu juna-biyu. Masunta suke bayar da maganin sanyi da ƙayar kifi. Mahauta suke bayar da maganin kaifi da kuma tsini da sauransu.

Shawarwari

  • Saka gasa a wajen samar da kayayyaki daga lokaci zuwa lokaci don bunƙasa sana’o’in kamar yadda Ƙungiyar Zauren Hausa Nijeriya ta ɗauki gaɓaren yi.
  • Hukumar ilimi ta sanya shi a manhajar makarantu domin sanya shi cikin manyan darussa koyarwa a matakai daban-daban na ilimi.
  • Masu riƙe da sarautun gargajiya lallai ne su zama sun yi kira da wayar wa da jama’a kai tare da cusa sha’awa don amfani da irin kayayyakin da sana’o’in na gargajiya suke samarwa.
  • Jama’ar gari su ma ba a bar su a baya ba, lallai ne sai sun dawo daga rakiyar da ba ta ƙarewa, wato sun yi riƙo  hannu bibiyu wajen rungumar kayayyakin da sana’o’in mu suke samarwa.
  • Ba da tallafi na kuɗi da kayan aiki ga masu sana’o’in da shawarwari da dabaru daga ƙwararru na masana iri daban-daban.
  • Hukumomi na gwamnati su dinga amfani a kayayyakin da ake samarwa ta fuskar sana’o’in Hausawa na gargajiya.

Kammalawa

Waiwaye a kan sana’o’in gargajiya na Hausawa ya nuna cewa jajircewa da tsayawa tsayin daka a kan wasu sirrika da taimakon juna su ne tushen tattalin arziki da ci gaban al’umma a wancan lokaci, kuma har yanzu suna da daraja wajen kare martabar al’adu da samar da ayyukan yi a cikin al’umma.

Manazarta

Adamu, M. (1978), The Hausa Factor In West African History. Zaria/Ibadan A.B.U. and Oxford,.

Alhassan H. da wasu, (1980), Zaman Hausawa, Littafi Na Ɗaya  Zaria. .I.E.P.,A.B.U.

Aliyu, U. (2015). Kasuwanci da Cigaban Al’umma. Zaria: Ahmadu Bello University Press.

Aminu, K. (2000). “Saka Sana’ar Sarrafa Auduga a Kasar Hausa: Tasirinta da Muhimmancinta.” Kundin Degree na Farko. Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero, Kano.

Asiru, A. (2017). Sana’ar Dinki Da Ci Gabanta. Zaria: Amadu Bello University Press Limited.

Bashir, I.S. (1990). “Take da Kirarin Sana’o’in Gargajiya: Nazarin Ma’anarsu da Muhimmancinsu ga Rayuwar Hausawa.” Kundin Digiri na Biyu. Jami’ar Bayero, Kano.

Batagarawa , S.A.(2013). Nason Wasu Al’adu a Kan Sana’o’in  Gargajiya na Hausawa Mazauna Lokoja. Takardar da aka gabatar a taron ƙarawa juna sani na kasa da kasa mai taken “Tavarvarewar Al’adun Hausawa a Yau” wanda Sashen Koyar da Harshunan Nijeriya  na Jami’ar Umaru Musa Yar’adua tare da hadin gwiwar Hukumar Adana Tarihi da Al’adu ta Jihar Katsina a ranakun 25-26 ga watan Yuni, 2013.

Dan’iya, M. A. (2006). Tasirin Kimiyya da Ƙere-ƙeren Zamani a kan Sana’o’in Hausawa na Gargajiya. Kano: Kabs Print Services Nigeria.

Garba, C. Y. (1991). Sana’o’in Gargajiya a Ƙasar Hausa. Ibadan: Spectrum Books Ltd.

Ibrahim, M. (2010). Tattalin Arzikin Hausawa. Kano: Benchmark Publishers.

Madabo, M.H. (1979). Ciniki da Sana’o’i a Kasar Hausa. Lagos: Nelson.

Madauci, I. da wasu (1968). Hausa Customs. Zaria: Northern Nigeria Publishing Company Ltd.

Maiyama, U.H. (2008): Sata A Zamantakewar Hausawa (Nazarin Waƙoƙin Barayi Na Muhammadu Gambo Fagada) Kundin Digiri Na Uku Da Aka Gabatar A sashen Nazrin Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato.

Mu’azu, A da Satatima,I.G. (2013). Kwaɗon Al’adun Hausawa da na Wasu Ƙabilu. Takardar da aka gabatar a taron ƙarawa juna sani na kasa da kasa mai taken “Tavarvarewar Al’adun Hausawa a Yau” wanda Sashen Koyar da Harshunan Nijeriya  na Jami’ar Umaru Musa Yar’adua tare da hadin gwiwar Hukumar Adana Tarihi da Al’adu ta Jihar Katsina a ranakun 25-26 ga watan Yuni, 2013.

Sani, A. (2003). Hanyoyin Rayuwa da Aikin Yi a Najeriya. Kaduna: Fisbas Media.

Smith, A. (1776). An Inquiry into the Nature and Causes of the Wealth of Nations. London: W. Strahan and T. Cadell.

Yahya,  I.Y. da Ɗangambo, A. (1986). Jagoran Nazarin Hausa. Zaria: Northern Nigeria Publishing Company Limited.

Yahya, I. Y. da wasu (1992). Darussan Hausa don Manyan Makarantun Sakandare. Ibadan: University Presss Plc.

Karanta Hanyoyin Zamantakewar Hausawa 

Edita@rumasau-kallamu

labarin da ya wuceFassarar Huɗubar Juma’a Rubutacciya Daga Masallaci Mai Alfarma 15th August 2025
Labarin na GabaSauran Waɗanda Suka Yi Shahada Tare Da Husaini (Radiyallahu Anhu)