Domin shiga gasar mawaƙa wadda ƙungiyar gamayyar marubuta da yadda manazarta waƙoƙin Hausa ta ƙasa, ta saka a ƙarshen shekarar 2018 zuwa farkon 2019.
- Allah na roƘa cikin ɗa’a,
- A baitukan nan da babu ba’a,
- Allah na ɗaro daɗin sa’a,
- A baitukan nan da ba bidi’a,
- Albarka sa min na ɗau ƙuri’a.
- —————————–
- Na yo salati ga Manzona,
- Na Khadija, Hafsat, Uban Nana,
- Na Sadiƙu, Umar, Usumana,
- Na Aliyu zaki kisan arna,
- Na Mu’awiyya sahihin ƙima
- ————————–
- Zuma farar gani farar saƙa,
- Na ƙulla baiti cikin waƙa,
- Na tsara ɗango cikin sarƙa,
- Domin yabon Ɗaha kun ji haka,
- In ka bi Manzonmu ka fi haka.
- ——————————-
- Kyawun ɗabi’unsa sun fi ɗari,
- Kufurun, musulmanmu sun nazari,
- Zama da Manzon fa ba haɗari,
- Rayuwa a tsarinsa ba garari,
- In ka bi Manzonmu ka ci gari.
- ——————————–
- An haifi Manzo a Makkiya,
- Ran Litinin sha biyun ku jiya,
- Auwal Rabiyun na ɗan juya,
- Shekara ta giwa a Habshiyya,
- Islam kalanda ta Hijriyya.
- —————————-
- Nasabar Mahaifinsa Abdallah,
- Abdulmuɗallib cikin jumla,
- Haashim fa Kaka ga Abdallah,
- Abdulmanaf ɗan Ƙusai Allah,
- Ya sa Kilab don cikar falala.
- ——————————
- Umminsa Babba Aminattu,
- Yar Wahab, Manafi, Zuhuratu,
- Sun haɗe a Kaka taƙaita batu,
- Na biyar Kilab sai ku gane batu,
- Sirarsa Manzon da bai shantu.
- ———————————
- Matansa sha ɗai na lobayya,
- Khadija farkonsu kun ji ɗaya,
- Assha da Hafsat suna baya,
- Ummu Habiba da Salmayya,
- Hindattu, Saudat ba sa ƙarya
- —————————-
- Sai Zai nabu bintu Jahshiyya,
- Maimunatu bintu Harisiyya,
- Zainab Khuzaima na jerayya,
- Sai kam ta ƙarshe Juwairiyya,
- Matansa cif-cif da sha ɗay
- —————————-
- ‘Ya’yanSa bakkwai cikar sunna,
- Ibrahim a farko mai suna,
- Abdallah, Ƙasim da ba su tsana,
- Fatima, Kulsum cikar ƙauna,
- Ruƙay da Zainab cikon juna.
- ——————————
- Manzo yana nan da mu’ujiziyya,
- Ƙur’an da ba wasa ba ƙarya,
- Tatsuniyar nan ta yan zolaya,
- Ba shirme danniyar nan ku jiya,
- Halinsa ne kun ji khairiyya.
- ——————————
- Halinsa Manzo cikar kunya,
- Nutsuwarsa Manzo a taffiya,
- Maganarsa ƙamshi yake zirya,
- Dattijo ne mai halin manya,
- Ƙur’an dalilinsa baki ɗaya
- —————————
- Dini na Manzo da ba ƙarya,
- Ba yaudara ko kisan hanya,
- Shi gaskiya ce zancensa ɗaya,
- Dinin da Shaiɗan yake baya,
- Ba ya kusantarsa don kariya.
- ——————————-
- Islam ya kawo a Makkiya,
- Ya ƙira Ƙuraishi su bar ƙarya,
- Sata da shirka da camfiyya,
- Da kisa na juna da shirya tsiya,
- Su riƙe ƙiran nan na kimtsiyya.
- ——————————-
- Rukunai shida ne na Addini,
- Zan ambato su ku ɗan ji ni,
- Kalma ta farko shahadataini,
- Sallah, Azum, Zakka ba raini,
- Hajji a ƙarshe ga mai sukuni.
- ——————————-
- Iman ku gane ajinsa shida,
- Iman da Allah, Mala’iku da;
- Littattafan nan na aƙida,
- Manzanni, Lahira kui shaida,
- Ƙaddar fa wajib cikon na shida.
- ——————————-
- Ya yaƙi arna cikin sa’a,
- Ya rusa daular da ba ɗa’a,
- Ya ce gumaka mu yo bara’a,
- Kisa na juna mu bar bidi’a,
- Kushe da juna mu bar ta ba’a.
- ——————————
- Yaƙi talatin na yo nazari,
- Ya yo su ba ɗai Ya buɗe gari,
- Islam ya zamto cikin fahari,
- Kufurun suna can suna garari,
- Aljanna ce duk cikar guzuri.
- ——————————-
- Daula ta zamto ta Islama,
- Kowa ya zamto cikin hidima,
- So, taimakon juna ba ƙyama,
- Ba soke-soke da yin gulma,
- Cab! Kun ji hanyar mutan ƙ
- —————————–
- Zan dakata zana sa birki,
- Tamkar fa mota a kan tuƙi,
- Nayaya ƙanin Bilki,
- Yobe gari na da ba raki,
- Tammat salamun na yo birki.
domin samun karanta cikakkiyar waƙar danna koren rubutu