-
Allahu ba ni dubun basira mayyawa,
In yi baitukan bege ga ɗan Adanani
-
Ga munasaba ta watan Rabi’ul Lawwali,
Wata na samun Sayyidul kaunaini.
-
Kafin zuwansa duniyar ga baƙi ƙirin,
Duk ta nutse a duhun ɓata tai muni.
- Tauhidi loton babu shi sai nadiran,
Kaɗaita bautar Rabbu tai nuƙusani.
- Sai kame-kame ake cikin kogin ɓata,
Bautar wanin Allah da bin shaiɗani.
- Sai zulmu ko a ina da danne haƙƙuna,
An juya shar’un Rabbana Mannani.
- A wanga hali Ɗaha ya zo duniya,
Don tsarkake ta ga dukkanin ɗuguyani.
- Ta tsatson ababen zaɓuwa gun Rabbana,
Nasaba da halayen ƙwarai ihsani.
- Ya zo a tsarkake ba ƙazanta ko kaɗan,
Ya girma kamamme ga duk buɗlani.
- Mai gaskiya aka san shi fai har baɗini,
Da riƙon amana sun kira shi Amini.
- Allahu ya zaɓe shi don manzantaka,
Ta isar da Tauhidi ga dukkan kauni.
- Ya ba da dukkan rayuwarsa wajen isar,
Saƙo na Tauhidi a san gufrani.
- An tsangwame shi a Makka har dangi nasa,
Da dukan Sahabbai masu bin Rahmani.
- Yai shekara har Sha Uku a cikin matsi,
Laifinsa Tauhidi da ƙin ausani.
- Ya bar garinsa na haihuwa a bisa haka,
Haka ma Sahabbai nasa sun hijrani.
- A Madinatu Yasrib ya zauna har zuwa,
Ƙarshe na rayuwarsa bisa ga amani.
- Qur’ani an saukar garai don shiriya,
Bautar Ilahu da kyauta dukkan shani.
- Rayuwarsa ta zam bauta Rabbil izzati,
Koyar da Qur’ani gami da bayani.
- Mai tausayi ga dukan halitta ya zamo,
Mai kyauta hulɗa ne ga duk insani.
- Mai yafiya ga dukan kure ne Musɗafa,
Mai tarbiyantarwa bisa ihsani.
- Mai tsai da adalci ga kowa Annabi,
Mai ƙyamatar haƙƙin wani a yi danni.
- Mai koya shar’a aikace don ai biya,
Bai bar a keta umarnukan Rabbani.
- Mai ƙas da kai ne babu girman kai ga shi,
Mai girmamar babba da ma sibyani.
- Mai yin hidimtawar iyali nasa ne,
Haka ma sahabbansa bila firƙani.
- Mai son lumana ba shi son ce-ce-ku-ce,
Bai yaƙi kowa sai bisa burhani.
- Mai murmushi ne shi ga kowa Sayyadi,
Kowa gare shi yana zuwa ya yi zauni.
- Mai yin du’a’in shiryuwar umma yake,
Don sauƙaƙar tsayuwa gaban Rahmani.
- Kyawun halinsa ya ba Sahabbai kwaikwayi,
Suka ɗabbaqa su a ko’ina ba zanni.
- Sun tarbiyantu gare shi baban Ƙasimu,
Suka yaɗa Tauhidi a ƙauye birni.
- Sun keta dazukka Hamada sun isar,
Sun ƙetare Kogi da dukkan Tsauni.
- Haka Tabi’ai suka bi a wannan hidima,
Ta yaɗa saƙonnin farin addini.
32.Matsayinsa gun Allahu mai girma yake,
Tamkar ya shi babu cikon Manzanni.
- Duk Manzani izuwa mutanensu kaɗai,
Ya taƙaita saƙon Rabbi kan imani.
- Shi ko Rasulullahi dukkan duniya,
Allah ya ce ya isar da Alqur’ani.
- Haiwanu dabbobin tudu da na Maliya,
Bayan dukannin ‘yan Adam wal Jinni.
- Ceto a ranar tsayuwa shi za a ba,
Farko gabanin dukkanin Manzanni.
- An ba shi tafkin Kausara mai waraka,
Ga dukan ƙishi Manzo jinin Adanani.
- Saƙon da an masa ya isar mun tabbata,
Kamar da Rabbi ya ba shi ba nuƙusani.
- Musulunci ya ratsa dukannin duniya,
Lungu da saƙo sai tilar Qur’ani.
- Ya Sayyadi baban Ruqayya da Ɗayyibu,
Mun shaida ka yi isar da duk saƙonni.
- Ya mai yawan zikiri da bautar Rabbana,
Mun yarda Allah ɗai yake Wahadani.
- Ya mai yawan jinƙai ga dukkan talikai,
Ka ceci al’umma ga bin ausani.
- Ya Sahibas Siddiƙi Umar naka ne,
Suruki wajen Usmanu Zun-Nuraini.
- Ya surukin Haidar Aliyu mazan ƙwarai,
Kakan tagwaye Alhasan da Husaini.
- Ya wanda zai karɓi Luwa’ul Hamdi ran,
Tsayuwa ga Allah Sahibat Tijjaani.
- Ya wanda zai ceci Musulmi na ƙwarai,
Ranar hisabi da awon mizani.
- Ya Sayyadi Allah muke roƙo ya sa,
Mu mutu bisa ga biyar Kitab was Sunni.
- Ya Abba Fatima Albatulu Habibuna,
Allah ya ba mu zama da kai a Jinani.
- Allah muna yin hamdala munka zamo,
A cikin Musulmi khiiratul adyani.
- Allah ka tsai da mu siraɗul mustaƙim,
Izuwa macewa kar mu zam khusrani.
- Allah ka dumata zuciyarmu bisa biyar,
Manzo naka da ka bai wa Alqur’ani.
- Allah muna a cikinsa ƙarshen zamani,
Mai haɗari da yawan biye shaiɗani.
- Allah tsare mu da makarul a’adaa’i,
Na son mu raunata har mu bar imani.
- Allah ka dawwama son Rasulu a zuciya,
Ya zamo abin koyinmu dukka shu’uni.
- Begen masoyi ya halatta ga taliki,
Balle Rasulu da Rabbi ya yi umarni.
- Yabon gwani ko wajibi haka anka ce,
Manzo gwani na gwanaye ne ba zanni.
- Aikin da ya yi wa duniya tamkar ya shi,
Ba a yo ba har yau in akwai wane ni?
- Kullum salati gare shi kar mu sake da yi,
Guzuri gare mu manauyayin mizani.
- Sallaa alaikallahu ya khairal bashar,
Wa ’Alika wa Sahabi wal ikhwani.
- Mai tsara waƙar Nasiru G. Ahmadu,
Mai son Rasulu hasanarsa da rauni.
Alhamdu lillahi.
Wannan waƙa an ciro ta ne daga littafi mai suna TASKIRA wanda Nasiru G. Ahmad ya wallafa.
Karanta Yadda Falalar Suratul Ƙulhuwallahu Ahad Take
Edita@rumasau-kallamu










