1. Suna na Allah farawa,
Baiwarsa mun yo godewa,
Yawan salati ƙarawa,
Wajen Rasulu abin kewa,
Gare mu ba ma fasawa.
2. Batu nake son saƙawa,
Kan duniyarmu ta Hausawa,
Da ba shi kyautu mu mantawa,
Tadarmu mai kyau da daɗewa,
Da ayyukanmu na kyautawa.
3. Sunanmu ya tafi nesawa,
Da kyan halinmu na yabawa,
Aikin fasaha da ƙwarewa,
Abin amana mu tsarewa,
Da gaskiya ba sauyawa.
4. Tsarin shigarmu gwanin ƙawa,
Da kwarjini ba kushewa,
Kowa ya gan mu yana shawa,
Duk duniya tai shaidawa,
Kyawun ɗabi’un Hausawa.
5. Tsarin sarautun mulkawa,
Mun yi fice mun tserewa,
Mun gaji wannan da daɗewa,
Har yau muna ta kiyayewa,
Don kar su zam salwancewa.
6. Zumuntaka mai ɗorewa,
Haƙƙin zumunci sadawa,
Ƙauna ga juna aikawa,
Kullum muna sabuntawa,
Da ƙin zumunci yankewa.
7. Mun yi fice gun kyauta wa,
Dukkan maƙwabta ba rowa,
‘Ya’yanmu duk babu rabewa,
Tare muke tarbiyyarwa,
Sashensu ba fifitawa.
8. Kowa yana da abin yowa,
Yara ga tarbiyyantarwa,
Ba ware Bora ko Mowa,
Babu batun wannan nawa,
Don me ka bi shi ka mar tsawa?
9. Kowa sana’a ka riƙewa,
Don al’uma amfanawa,
Mu ke saƙa tufar sawa,
Mu zam rina ta ta yi ƙawa,
Kafin mu kai ta ga ɗinkawa.
10. Mu jeme fata tsafcewa,
Mu yo jaka takalmawa,
Taiki Kube da Zabirawa,
Har da su Banten ɗaurawa,
Domin mu kare tsiraicewa.
11. Abinci mu ke nomawa,
Mu taskace mai saidawa,
Kowa ya ƙoshi ba yunwa,
Nama muna kiwantawa,
Muna fita mu farautowa.
12. Ba mai zama haka Hausawa,
Kowa sana’a tai kewa,
Zama na banza ba maiwa,
Wanda ya ɗau sangarcewa,
Ba zai yi matar aurawa.!
13. Zaman iyalinmu da ƙawa,
Kwai disfilin adaltawa,
Yara ba a bambancewa,
Ɗan kishiya ma ka riƙewa,
Tamkar uwar da ta haifawa.
14. Akwai haɗin kai da gamewa,
Idan larura ta zo wa,
Wani guda ba kasawa,
Taro ake don a kawarwa,
Cike da ƙauna tausawa.
15. Yara biyayya sunke wa,
Duk babbuna babu rabewa,
Yi na yi bar shi su dainawa,
Su kuwa manya tausawa,
Ga yara sunka zamo yowa.
16. Kaɗan na yo lissafawa,
Na kyan zamewar Hausawa,
Da munka gada da daɗewa,
Da ya wajabtu mu danƙewa,
Domin na baya su tararwa.
17. Abin takaici da ƙiyawa,
Halin ga ‘yan yau ka gujewa,
Na martabarmu ta nunawa,
Don taƙamar sun wayewa,
Hanyar ba za tai ɓullewa.
18. Dolenmu mui jajircewa,
Ga raya tada mu riƙewa,
Shi ne tafarkin burgewa,
Kayan aro mu yi watsarwa,
Don katara ba shi rufewa.
21. Allah ka ba mu amincewa,
A nan da ranar komawa,
Duk laifukanmu ka yafewa,
Don Musɗafa mai shiryarwa,
Manzo da ka zam aikowa.
22. Nasiru G. suna nawa,
Ɗan Ahmad babu musawa,
Birnin Kano na zamtowa,
Nai shukura na yi daɗawa,
Waƙar a nan ta yi tuƙewa.
Wannan waƙa an ciro ta ne daga littafin TASKIRA wanda Nasiru G. Ahmad Ya wallafa.
Karanta Waƙa Mai Taken Ɗan Achaɓa










