Waƙa Mai Taken Gudumar Dukan Rashawa

0
9
  1. Ya Allah sunanKa farko,

Don aikina ya yi ƙarko,

Har al’umma duk su farko,

Mu kauce hanya mai duɗewa.

 

2. Na yi salati gun sa Manzo,

Wanda ya ce duk mu yi ƙwazo,

Biɗar halal duk inda mun zo,

Shi ne tafarki mai ɓulewa.

 

3. Waƙa zan yi a kan halinmu,

Wanda ya zam shi jiki gare mu,

Tamkar umarnin khaliƙinmu,

Mun ɗauke shi muna riƙewa.

 

4. Yin rashawa ko toshe baki,

Don kwaɗayin ai wani aiki,

Wanda ya kauce wa tafarki,

Albarkarmu yake ragewa.

 

5. Guba ce wallah in ka karɓa,

Ko ko ka bayar anka karɓa,

Dokar Allah ce ka saɓa,

Ƙin gaskiya hanyar ɓacewa.

 

6. Mutunci farko zai zubewa,

Aiki ya zam ba kyautatawa,

Sai amaja da sukurkucewa,

Al’amuranmu su dagulewa.

 

7. Mai haƙƙi ne an hana shi,

Wanda take mai kyau niyarshi,

An ba mai bayar da toshi,

Wanda niyarsa abar gujewa.

 

8. Muddin an haka ba amana,

Ba adalci sai hiyana,

Sannan babu zaman lumana,

Sai ɗar-ɗar sai firgicewa.

 

9. Kwai rashawar daɗaɗa zance,

Wata da aiki kan kasance,

Wata jaka ce za a sunce,

Ɗan hasafi a zamo yiwowa.

 

10. Wata ko kyauta za a ba ka,

Iyaye ko ko a ba wa ɗanka,

Domin biɗar wani abu gun ka,

Ka yarda ko ko ka zam ƙiyawa.

 

11. Kowane nau’i ya haramta,

Annabi ya tsine wa yin ta,

Mai karɓa har wanda yai ta,

Dai dai ne suke ba rabewa.

 

12. Ga lamura yau sun ƙazanta,

Harka duk an sassaka ta,

An rufe duk munin sifarta,

Sunanta an kyautatawa.

 

13. Na yi tunanin me ya sa ne,

Ba ƙyamar ta wurin mutane?

Duk mai cin rashawa mu gane,

Har mai ba shi abin gujewa.

 

14. Rashin kishi ni a ganina,

Shi ke sawa har a raina,

Halali sai a ga wai kaɗan na,

Sai an ɗora haram daɗawa.

 

15. Duk mai kishi ga ƙasarsa,

Mai kishin kuma al’umarsa,

Ba ƙofar rashawa a gun sa,

Siraɗi gobe yake wucewa.

 

16. Son kai yai kanta a zuci,

Tai tsatsa sassanta ya ci,

Shi ke sa rashawa ake ci,

Ba ƙyama sai ƙawatawa.

 

17. Ƙyashin samu ga waninmu,

Da ci da zuci ke hana mu,

Yin haƙuri bisa matsayinmu,

Wanda Ilahu ya zam rabawa.

 

18. Sai haɗama sa har da wannan,

Son a fiye wancan da wannan,

Su ke sa rashawa ƙasar nan,

In mun bar su tana gushewa.

 

19. Yaƙin halayen ga dole,

Kishin ƙasa mu riƙe shi lalle,

Sai lamuranmu su sake lale,

Albarka ta isa ga kowa.

 

20. Irin haka ne manyan ƙasashe,

Da ke amo kowane sashe,

Na duniya suka yi koyaushe,

Al’umarsu take ta shewa.

 

21. Ba su barin azzalumina,

Sun taushe maciya amana,

Ba sa ƙyashin ikhiwana,

Cima gabansu suke biɗowa.

 

22. Dubi yawan jama’a ta Caina,

Sun haɗa kai babu hiyana,

Sun aiki a dare da rana,

Yau kayansu muke shigowa.

 

23. Turawa haka sunka dage,

Duk aiki nasu babu coge,

Cin rashawa duk sunka toge,

Ba sa yin sa suna ƙiyawa.

 

24. Don haka ne duk al’umarsu,

Tai bunƙasa arziƙinsu,

Yai albarka kowanensu,

Na fahari da abin da kewa.

 

25. Mu ma dole mu ɗaura niyya,

Yin aiki ja mui gamayya,

Kowa ya zo yara da manya,

Mu ɗau rashawa izuwa kushewa.

 

26. Niyya ƙwaƙƙwara mu ɗaura,

Don yaƙar duk asharara,

Masu zagon ƙasa masu ƙera,

Turakun ci bayan da kewa.

 

27. Ba wasu ne maciya amana,

Ga dukiya ta ƙasa su danna,

Wasoso sun ƙi su daina,

Ha’intar mu suna ta yowa.

 

28. Ƙaunar ƙasa ta zamo gabanmu,

Don bunƙasar arziƙinmu,

Da ci gaban duk jama’armu,

Alheri ya isar wa kowa.

 

29. Lallai mu so wa ɗan uwanmu,

Abin da muke ƙauna ga kanmu,

Ko ma mu fifita shi kanmu,

Babu ganin ƙyashi da rowa.

 

30. Doka mai tsanani a yo ta,

Kan rashawa duk masu yin ta,

A kame don sun yo mugunta,

A kai wa Yari ya zam tsarewa.

 

31. A nusarshe da dukan mutane,

Munin aikin don su gane,

Su ƙyamaci mai yi ko wane ne,

Don ba son mu yake yiwowa.

 

32. Azzalumai ku mu yo rahoto,

Zuwa hukuma don a ƙwato,

Haƙƙoƙi kowane loto,

Ba tsoro ko razanewa.

 

33. Mutum ne zai tono masifa,

Ba shi ɗai ne za ta shafa,

Har kowa dole mu dafa,

Ɓarnatai mu zamo hanawa.

 

34. Cin rashawa ke sa talauci,

Aikin ɓarna ya yi kauci,

Duk lamura saura su ɓaci,

Dole mu yaƙar ba gazawa.

 

35. Aikin kowa ne da kowa,

Hukumomi ku mu tallafa wa,

Domin ƙasarmu ta zamowa,

Abar fahari ba ha’inawa.

 

36. Hukumomin jin ƙorafinmu,

Sun tsaye domin taimakon mu,

Yaƙar kaskar da ka cin mu,

Cima gabanmu suna hanawa.

 

37. Mu roƙi Allah taimakonsa,

Kan yaƙi bisa ‘yan ta’asa,

Masu ciye rashawa su ƙosa,

Da ha’inai ‘yan handamewa.

 

38. Allah ba mu yawan ƙana’a,

Ƙaunar juna da muru’a,

Cin rashawa mu yi mai bara’a,

Don Manzo ɗan Hashimawa.

 

39. Nasiru G. Ahmad ya yi ta,

Don harkar rashawa mu bar ta,

Mu soyi juna mu rabauta,

Halinmu ya zamo yabawa.

 

40. Goma huɗu baitinta jumla,

Ce Arba’in na gode Allah,

Allah tsare mu biye ralala,

Amin sarki mai iyawa.

 

Danna nan don karanta Waƙa Mai Taken Masha-Jini

Edita@rumasau-kallamu

labarin da ya wuceWaƙa Mai Taken Masha-Jini
Labarin na GabaRasuwar Makaɗa, Sarkin Kiɗan Maradun Alhaji Musa (Ɗanƙwairo)
Nasiru G. Ahmad
Haifaffen jihar Kano ne a unguwar 'Yan awaki. Ya yi digiri na ɗaya da na biyu a kan harshe da adabin Hausa. Yana cikin ƙungiyoyi da dama na marubuta a ciki da wajen jihar Kano. Malami ne kuma mawallafin littattfai da waƙoƙi.