“Garina Abin Alfaharina.” Littafi ne da ya zamo tamkar madubin da ke haskaka zuciyar al’umma, domin a cikinsa an ɗaura labarin a kan gaskiya, haɗin kai, da sadaukarwa. Gari fitila ce, amma mutane su ne wutar da ke haskakata (kunna ta).
Marubucin ya zubo bayanai cikin hikima, ya zana halaye da ɗabi’u a matsayin tubalin gina al’umma. Har ila yau, al’umma ba ta tashi da cigaba, sai da haɗin kai. A wannan littafin an nuna mana cewa “Gari na bunƙasa ne da mutanensa”, domin ba gine-gine ba ne kaɗai suka gina gari ba, hasalima zuciyar mutanenta ce.
Ga Malam Yahaya Garba, Malam Mammaada, Malam Surajo Yunusa, Malam Aliyu Labaran, Malam Magaji Ƙofa, Malam Idi Ɗanlula da sauran malamai, waɗanda suka zama tamkar katanga ga iska, suna tsayawa a kan ilimi da tarbiyya.
Haka kuma marubucin ya kawo wasu matasa masu kirki; Dakta Mujaheed da Salmanu Faris, Alhaji Abubakar Suleiman, Barrister Anas Lawal Audi, waɗanda suka yi tsayawan tsayin daka ga ‘ƴan siyasa, don ganin an samar da cigaba a garinsu.
Kuma sun tabbatar da haka, domin sai da suka miƙa kundin buƙatun al’ummarsu ga duk ɗan siyasan da yake neman ƙuru’arsu kafin su zaɓe shi.
Lafiya uwar jiki, babu mai fushi da ke in ji Ɗan Hausa, a cikin littafin an ga lokacin da Dakta Ado Zakari, Dakta Murtala Muhammad, Dakta Khalid Gambo da Hajiya Gude suka tsayin daka wajen warware wasu cututtuka a garin gami da sadaukar da ilimin su, don amfanuwar garin.
Abin da ya fi jan hankali shi ne yadda marubucin ya sassaƙa turakun zaman lafiya tsakanin ƙungiyoyin addini, wato Tijjaniya, Izala da Shi’a. Kamar yadda ake cewa: “Idan ruwa ya yi yawa, sai ya zama teku.”, kuma ” Zaman lafiya ya fi zama ɗan Sarki.
Saboda, gari yana samun cigaba ne a lokacin da aka samar da zaman lafiya (tsaro), ilimi, sana’a da kasuwanci da sauransu. An hango wasu harsunan mutane, waɗanda suka sadaukar da rayuwarsu don cigaban garin ta fuskar tsaro, an kuma zayyano wasu gwadabe na samar da tsaro da cigaban gari.
Shi ya sa wannan littafin ya kasance tamkar gorar ruwan sanyi ne ga mai tafiya a cikin sahara.
Danna nan don karanta Waƙa Ta 2 Ga Farfesa Mu’azu Sa’adu Muhammad Kudan
Edita@rumasau-kallamu










