An haifi Ashiru Hamisu a garin Kudan a gidan Tattibu, ɗa ne ga Malam Adamu wanda aka fi sani da Malam Bala, sunan mahaifiyar sa ita ce Maryam Yusha’u wacce aka fi sani da suna Dogora an haife ta a ƙofar Arewa gidan Malam Tanko, ta rasu a shekara ta 2019. Ashiru an fi sanin sa da suna Ashir San, wanda yake amfani da sunan yayan sa, wato Sani, wanda shi ne babban yayan sa.
Ashir San ya yi karatun allo a hannun Malam Abdullahi, wanda shi ne ƙanin mahaifiyar sa, tun yana karatun allo ya fara tunanin yadda zai rubuta waƙa, saboda yawan jin wani shiri da yake yi a Kano a Freedom Radio, wato shirin Taskira sai ya samu takarda ya fara rubuta waƙa, amma da ajami (rubutun harafan larabci) sai mutane suke yi masa dariya, saboda su ba su taɓa ganin inda aka rubuta waƙa da ajami a lokacin su ba.
Bayan ya dawo gida daga makarantar allo, sai ya shiga makarantar zamani (boko) a inda har yanzu yana fafatawa. Sannan kuma Allah ya yi masa baiwar waƙa har muryar Naziru sarkin waƙa yanayi, wanda ya fara koyo masa waƙa shi ne Shu`aibu army na ƙofar Arewa Kudan.
A fannin waƙa har sai da ta kai an kulle shi a police station har sai ya yi kwana uku a can, saboda wata waƙa da ya yi mai suna Kutara-kutara ɓarayi, daga ƙarshe sai uban gidan sa wato Salisu Ten-ten ya fito da shi, tun lokacin da aka kama shi sai ya ƙara samun magoya baya sosai, yana fitowa sai ya yi wata waƙa mai suna kainuwa dashen Allah, domin nuna godiyar sa ga mutanan sa suka ba shi gudunmawar su a lokacin da aka kulle shi, a ƙarshe kuma ya yi waƙoƙi da dama ga kaɗan daga cikin waƙoƙinsa;
1. Duniya .
2. Ita gaskiya.
3. Nusaiba.
4. Ashir San Salisu M. Rana.
5. Yayyafin kuɗi.
6. Kainuwa dashen Allah.
7. Ku tara ɓarayi.
8. Sarkin dole.
9. Tinjim.
10. Mazurai.
11. Sarkin Zazzau.
12. Fatima.
13. Baƙar masarauta.
(Mun samu wannan bayani ne daga bakin Ashir San wanda ya turo min ta waya ta a ranar Talata 13/06/2020 a misalin ƙarfe 5;03 na yamma).
Danna nan don karanta ƙa’idoji sha shida na samun nasara a rayuwa
Edita; Rumasa’u M. Kallamu