Tarihin Alaramma Malam Salisu Ɗanruwantsa

0
12

An haifi Alaramma Malam Salisu ɗan Malam Ahmad ɗan Usmanu ɗan Ahmad a garin Ruwantsa. An ce asalin zuriyarsu sun fito daga ƙasar Mali, Alaramma Malam Salisu ya taso a garin Ruwantsa a inda ya fara karatu a wurin Malam Abdul’Aziz ɗan Malam Ibrahim.

Lokacin da ya ƙara datawa kuma idonsa ya yi ƙwari, sai tsananin kwaɗayinsa ga Alƙur’ani ya ƙaru, ya ƙara duƙufa. Malam Salisu ya kasance tun ƙuruciyarsa ba ya zama wuri guda face yana tsakanin wancan gari da waccan tsangaya izuwa waccan cibiya ta makaranta. Wannan ya ba shi damar huɗuwa da gwarazan malaman zamaninsa irin su Malam Haruna Ningi wanda a wurinsa ne ya haddace AIƙur’ani Mai Girma.

Koda Alaramma Malam Salisu ya sami labarin bayyanar Gwani Hamad a garin Taura kuwa; sai ya zabura ya haɗa kayansa ya nufe shi kuma ya kamfata daga marmaron ilmin Gwani Hamad. Daga nan kuma ya wuce garin Malamawa wurin Bajimin malami Malam Abdullahi. Malam Sal ısu bai gushe ba yana kutsawa cikin kowane loko da saƙo na ƙasar Kano da kewayenta; har sai da ya dangana da garin Insharuwa cikin Jamhuriyar Nijar.

Bayan Dawowar Malam Salisu daga ƙasar Nijar ne ya yi aure a mahaifarsa. Daga nan ne ya taso tare da Wani adadi na almajiransa ya dawo Kano ya sauka Unguwar ƙofar Wambai; wurin Malam AbdulKarim inda ya karanta ilimin Tajwidi da Fiƙihu. Manyan malaman Malam Ɗanruwantsa sun haɗa da Shehin Malami Rabi’u Ɗantinki da Shehu Mai Hula. Bayan nan ne kuma ya sake zabura izuwa garin Ɗabbatta wurin babban malami Malam Adam; don sanin ilimi littafin Shaɗibiyya da ilmin Rasmu.

Sannan ya sake dawowa birnin Kano karo na biyu a inda ya sauka a wurin Malam Garba Tudun Nufawa.

Ya zauna shekaru biyu a wurinsa yan karantar Alfiyyar ɗan Malik. A lokaci guda kuma, shi Malam Garba Tudun Nufawa (Malam Abubakar Ramadan) yana koyon ilmin Tajwidi da Kira’o’i a wurinsa; Daga nan ne ya koma Unguwar Yakasai ya kafa makarantarsa a shekarar 1945.

Bayan ya tumbatsa da ilmi da Alƙur’ani; daga bisani kuma ya koma Gwauron Dutse kusa da Masallacin Juma’a na Sheikh Is’haka Rabiu a matsayin Na’ibin Limamin Masallacin.

A takaice dai zamu iya cewa Malam Salisu Ɗanruwantsa shi ne magajin kambin Shehi Rabiu Ɗantinki a fagen ilmin Alƙur’ani; da ƙira’o’i a faɗin Kanon Dabo. Tsangayarsa ta shahara da tsare-tsare masu ban sha’awa tare da sanya cigaban zamani a Wasu ɓangarori daban-daban. Alal misali, akwai tsarin azuzuwa inda ake sanya yara goma sha bakwai; a Kowane aji ana biya musu rabin sumuni da safe har sai sun haddace. Da yamma kuma a ƙara musu rabi don a samu kyakkyawar haddar AIƙur’ani.

Domin karanta cikakken bayani a kan Tarihin Alaramma Gambon Takai danna nan.

Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Tsarin Tsangayun Alƙu’ani A Arewacin Najeriya; Tarihin Su Da Zamantakewar Su Da Hanyoyin Raya Su; wanda Dr. Sunusi Iguda Ƙ/Nasarawa ya wallafa shi; domin karanta cikakken Littafin danna nan.

labarin da ya wuceHaramun Ne Mata Su Halarci Husainiyya
Labarin na GabaYadda Falalar Karanta Ayatul Kursiyyi Ya Ke