Tag: yadda ake

  • Wasiyyar Imamu Husaini (Radiyallahu Anhu)

    Wasiyyar Imamu Husaini (Radiyallahu Anhu)

    An karɓo daga Imamu Husaini (Radiyallahu Anhu); ya ce da ‘yar uwarsa Zainab lokacin da ya ga tana marin kumatunta za ta yaga tufafinta ta faɗi za ta suma, sai ya ce:

    “Ya ke ‘yar uwata, kiji tsoron Allah, kiyi haƙuri, ki sani halittun ƙasa za su mutu; na sama ba za su wanzu ba, babu abinda zai saura sai Allah; wanda shi ne ya halicci halittu da Ikonsa; shi ne makaɗaici sani mahaifina ya fi daraja, haka Kuma mahaifiyata, haka ɗan uwa na (Hassan); kuma ni da duk wani musulmi Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wa Sallam) ne abin koyin mu”.

    Sannan ya ci gaba da cewa: “ya ke ‘yar uwata na yi rantsuwa kada ki karya min rantsuwa ta, idan na mutu, kada ki yaga tufafinki, kada ki yakushe fuskarki, kada kiyimin kururuwa!

    To ɗan uwa ka ji da kansa abinda ya yi umarni, kuma har da rantsuwa kamar ya san a rina…; to don Allah waɗannan koke-koke da dukan jiki har ma da kisan kai a wasu lokuta; daga ina aka samo su?

    Domin karanta cikakken bayani a kan Matsayin Koke-Koke Da Kururuwa danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Kukan Manzon Allah (Sallallahu alaihi wassallam) danna nan.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Gaskiyar Magana A Kan Ashura wanda Shehu Mansur Dala ya wallafa shi; domin karanta cikakken Littafin danna nan.

  • Yadda Buroka Yake (Pidgin)

    Yadda Buroka Yake (Pidgin)

    GABATARWA

    Idan ana maganar harshe, to ana magana ne a kan fagen ilimin kimiyyar harshe wanda yake magana a kan yadda ake bin diddigi ko nazarin harshe a kimiyyance don fahimtar ƙa’idojinsa. Kowace al’umma tana da irin nata tsarin ilimin kimiyyar harshe.

    MA’ANAR HARSHE

    Masana da dama sun tofa al’barkacin bakinsu game da ma’anar harshe ;

    Yakasai (2012); “Harshe wata hanya ce ta bayyana kai da kuma hulɗa tsakanin mutane wanda dabbobi ba su da irinta”.

    MA’ANAR ILIMIN WALWALAR HARSHE

    Yakasai (2012); “Dukkannin abin da ya shafi jama’a ta fannin hulɗa ta rayuwa sannan har za su buɗe baki su yi magana game da wannan abu lallai yana cikin fanni ne na ilimin kimiyyar harshe da ya jiɓanci amfani da harshe a tsarin rayuwar al’umma”.

    Idan ana maganar cewa ilimin walwalar harshe ya shafi dukkan tsarin rayuwar al’umma kenan, ya shafi batutuwa da daman a rayuwar ɗanAdam kamar haka;

    • Addini
    • Siyasa
    • Kasuwanci
    • Al’ada
    • Ilimi
    • Tarbiyya da dai sauran su.

    MANA’ANAR BUROKA (PIDGIN)

    Kamar yadda ƙamusun Oxford ya bayyana ma’anar buroka; “Harshe ne da ya ƙunshi wasu kalmomi da yawa da sassauƙar nahawu wanda ake amfani da shi yayin sadarwa a tsakanin mutane ko al’umma”.

    Shi dai wannan salon harshen ya samu ne a sanadiyyar cuɗanya ko harhaɗuwar al’umma mabambanta masu bambancin harshe a wuri ɗaya, a sakamakon hulɗa ta kasuwanci ko ta siyasa ta addini ko al’ada ko ilimi ko kuma tarbiyya ko kuma ta wani abu na daban. A nan gida Nijeriya buroka an fi samunsa ne a wasu yankuna na ƙasar nan kamar kudanci da yammacin ƙasar.

    Sannin kowa ne dai buroka na samuwa ne a sanadiyyar cuɗanyar harsuna mabambanta biyu ko fiye da biyu a wuri ɗaya. A nan gida Nijeriya a kwai;

    • Inyamurai – masu magana da Ingilishi.
    • Yarbawa – masu magana da Ingilishi.

    A yayin da waɗannan al’umma suka haɗu a wuri ɗaya don aiwatar da wani al’amari, akan sami rashin fahimta a sanadiyyar bambancin harshe, amma kuma a dalilin harshen Turanci sai a juya a koma ana magana da buroka don samun sauƙi da fahimta.

    Misalai; Ana samun buroka a yayin magana, wato a jimlace

    Daidaitaccen Turanci            Buroka

    What is your name?             Weytin be your name?

    Tell him the story                 Tellem the tory/ yanam the tory.

    How are you?                       How you dey? How una dey?

    Come and eat                       Make you come chop.

    Come and sit down                Make you come sit down

    I’m in school                         I dey for sku

    Go and pick the pen              Make you pikam

    I want to go the market         I wan go market

    Let me take the dirnk             I wan drink wota

    Do not be angry please           I beg make you no ves

    She want to eat                     She won eat.

    What are you saying ?            Weytin you dey tok.

    Were are you going?               Wia you won go.

    She traveld to Abia                 She don go Abia.

    I’m hungry.                            Hunger dey waya me.

    Sai kuma ɓangaren ɗaiɗaikun kalmomi

    Daidaitaccen Turanci     Buroka

    Water                          wota

    What                           weytin

    Eat                              Chop

    People                         una

    Story                          Tory

    Stupid                         Mumu

    Mental                         Kolo

    MUHALLIN DA AKE AMFANI DA BUROKA

    Akwai wurare da ake samun buroka kamar ;

    • Kasuwanni
    • Yanar gizo
    • Kafafen sadarwa
    • Barikin soja/ ‘yan sanda

    ALFANUN BUROKA

    Shi wannan salon harshen yana da wasu alfanu da yake ba wa al’umma wajen gudanar da rayuwarsu;

    • Sauƙin fahimta
    • Saurin samar da kalma
    • Sauƙin furuci
    • Saurin isar da saƙo

    RASHIN ALFANUNSA

    Baya ga alfanun wannan salon harshe, akwai kuma wasu naƙasu da yake haifarwa ga al’umma, sun haɗa da;

    • Gurɓata gangariyar harshen Turanci/ Ingilishi
    • A wani lokaci yakan ɓatar da Kalmar asali mai muhimmanci.

    KAMMALAWA

    Duba da bayanan da suka game da ma’anar harshe da kuma ilimin walwalar harshe, tare kuma da kawo ma’ana da bayani a kan buroka mun fahimci abin da buroka ke nufi. Aikin bai tsaya a nan ba sai da ya kawo gurabe da alfanu da kuma rashin al’fanun buroka.

    MANAZARTA

    Hornby A.S, (2015) Oxford Advanced Learner’s Dictionary Of Current English 9th Edition. Oxford University Press. OUP.

    Yakasai (2012), Jagoran Ilimin Walwalar Harshe. Garkuwa Media Services LTD Sokoto Nigeria.

    Karanta Mai Maɗi Ke Talla (Mai Zuma Gida Ake Tad Da Shi)

    Edita@rumasau-kallamu

  • Sana’ar Wanzanci Da Sauye-sauyen Zamani Jiya Da Yau (Shimfiɗa)

    Sana’ar Wanzanci Da Sauye-sauyen Zamani Jiya Da Yau (Shimfiɗa)

    Wannan babi ya yi bayani kan hasashe da bagiren wannan bincike da manufarsa da ƙunshiyarsa da kuma dabaru da hanyoyin da aka yi amfani da su wajen tattara bayanan wannan nazari da wuraren da aka samo su.

    1.1 Hasashe da Bagiren Bincike

    Hasashe na kai tsaye da aka kalla a kan wannan bincike ya haɗa da:

    • Nazarin wanzanci a wajen Hausawa don gano tsantsar al’adun wanzanci ba tare da sun sami wata gurɓata ba.
    • Gano nauyin sauye-sauyen zamani da suka yi kaka-gida a wanzancin Hausawa tare da fito da yanayin rawar da al’adun wasu al’ummu suka taka a wannan sana’a ta wanzanci. Shin sauye-sauyen zamani sun taimaka wajen bunƙasa wanzanci ko kuwa sun taimaka wajen dankwafe shi?
    • Shin wanzanci da al’adun da suke zagaye da shi suna nan da kadarinsu har a wannan lokaci da muke ciki?

    Muhimmin hurumi na wannan bincike shi ne sana’ar wanzanci a ƙasar Hausa tare da duba yadda sauye-sauyen zamani suka shiga cikin wanzancin Hausawa daga al’ummomin Fulani da Barebari da Buzaye da Nufawa da Yarabawa. Sannan kuma da abubuwan da Hausawa suka samu na wanzanci daga al’ummar Larabawa da Turawa.

    Akwai wasu ayyuka da aka fara yi a kan wanzancin Hausawa da suka haɗa da Musa (1983) da Suleman (1990) da Sallau (2000). Shi wannan ɗoriya ne a kan abubuwan da aka fara tattarawa tare da shigo da wani sabon bincike inda aka duba sauye-sauyen zamani waɗanda wanzancin Hausawa ya ci karo da su daga al’adun wasu al’ummomi.

    Wannan bincike an karkasa shi yadda zai shafi manyan garuruwan ƙasar Hausa da kuma wasu sassa da suke maƙwabtaka da ƙasar Hausa na kusa da na nesa. Garuruwan da wannan nazari ya duba su ne kamar haka:

    (i) Rukuni na ɗaya ya ƙunshi garuruwan ƙasar Hausa a arewacin Nijeriya waɗanda suka haɗa da Argungu da Birnin-Kabi da Daura da Gusau da Kano da Katsina da Sakkwato da Yawuri da Zariya.

    (ii) Rukuni na biyu ya ƙunshi garuruwan da suke maƙwabtaka da ƙasar Hausa ta kusa ko ta nesa a Nijeriya waɗanda suka haɗa da Bauchi da Bida da Ibadan da Ilori da Jos da Kaduna da Kafanchan da Kagoro da Lafiyar-Barebari da Maiduguri da Kwantagora da Minna da Gwambe da Potiskum da Shagamu da Keffi da Yola da Wase da Lagos da Wamba da Zuru.

    (iii) Rukuni na uku ya ƙunshi garuruwan da suke cikin Jamhuriyar Nijar waɗanda suka haɗa da Maraɗi da Tassawa da Agades da Birnin-Ƙwanni da Yamai.

     1.2 Manufar Wannan Bincike

    Kafin shiga bayani a kan manufar wannan bincike yana da matuƙar muhimmanci a san ma’anar kalmar manufa. A ƙamus na Turanci (Hornby, 2000:804) an fassara kalmar manufa ‘objective’ a “matsayin wani abu ko buri da ake son cimma”. Abin nufi a nan shi ne, manufa na nufin tsara wasu hikimomi don samun biyan buƙata kan abin da aka sa gaba. Misali, babbar manufar duk wani malamin makaranta ita ce, bayan ya kammala darasinsa ɗaliban da yake koyarwa su fahimci abubuwan da ya koya masu.

    Idan muka juyo kan manufar wannan bincike za a ga bisa la’akari da ayyukan da mutane suka yi na rayuwar yau da kullum an fahimci kowane mutum yana da manufar da take cikin ransa da yake son ya cim mata. Masana da manazarta sun gabatar da ayyuka gwargwado kan al’adun Hausawa.

    Yawanci a waɗannan nazarce-nazarce an fi mayar da hankali kan fito da abubuwan da suka danganci al’adun aure da haihuwa da mutuwa da nazarin addinin gargajiya waɗanda suka shafi sihirce-sihirce da tsubbace-tsubbacen Hausawa. Bisa dukkan alamu ba a gudanar da wani bincike mai zurfi kan sana’o’in gargajiya na Hausawa ba, in ban da aikin Sharifai (1990) shi ma wanda ya yi game da kirari da take na sana’o’in Hausawa na gargajiya da kuma na Sallau (2000) wanda ya yi game da sana’ar wanzanci.

    Haka kuma ire-iren waɗannan ayyukan ba a faye duba rawar da sauye-sauyen zamani suka taka a wajen bunƙasa sana’o’in gargajiya na Hausawa ko daƙushe su ba. Saboda haka babbar manufar wannan bincike ita ce nazarin ƙaura da shigowar baƙi da tasirin al’adunsu a kan wanzancin Hausawa. Amma a rarrabe, wannan bincike ya fuskanci waɗannan abubuwa kamar haka:

    (i) Ƙaura da shigowar baƙi ƙasar Hausa tun daga farkon ƙarni na goma sha huɗu zuwa yau.

    (ii) Matsayin sana’ar wanzanci a idon Hausawa da kuma maƙwabtan Hausawa na kusa waɗanda suka haɗa da Fulani da Barebari da Buzaye da Nufawa da Yarabawa da sauran ƙananan ƙabilun sassan kudancin jihar Kaduna da wasu sassan jihohin Bauci da Gwambe da Filato da Nasarawa da Neja. Sai kuma maƙwabtan Hausawa na nesa waɗanda suka haɗa da Larabawa da Turawa.

    (iii) Sauye-sauyen zamani irin waɗanda al’adun maƙwabtan Hausawa na kusa da na nesa suka yi a kan sana’ar wanzanci.

    1.3 Ƙunshiyar Bincike

    Wannan bincike ya ƙunshi babi shida. An fara da yin shimfiɗa a inda aka bayyana hasashen wannan bincike da wuraren da aka samo bayanan da aka yi amfani da su wajen gabatar da wannan nazari.

    Sannan kuma aka yi bitar ayyukan da suka gabata waɗanda suka taimaka wajen sanin wuraren da wannan bincike ya sa gaba. Bayan haka an yi waiwaye kan ƙasar Hausa da ɓunƙasarta da yadda baƙi suka shigo da dalilan shigowarsu da garuruwan da suka zauna. An kuma yi bayani dangane da tasirin addinin Musulunci kan wasu al’adun Hausawa waɗanda suka shafi dabbar suna da askin ranar suna da al’adun kaciya da kaciyar mata, da sauran wasu ayyuka da wanzamai suke yi a ƙasar Hausa.

    An ci gaba da kawo bayanan da suka danganci wasu al’adun Turawa cikin sana’ar wanzanci waɗanda suka haɗa da aski da kaciya da cire haƙori da gudummuwar ba da jini da matakan da ake bi don kula da mai ciki da iren-iren hanyoyin da ake bi don tanadin abin da aka haifa da kuma irin yadda magungunan Turawa suka yi tasiri a kan ire-iren waɗanda wanzamai suke bayarwa.

    Daga ƙarshe an kawo bayani kan nason da al’adun wasu baƙi waɗanda suke zaune a cikin ƙasar Hausa da kuma na wasu al’ummomi maƙwabta waɗanda Hausawa suke zaune a cikin ƙasashensu suka yi a kan wanzanci.

    1.4 Dabarun Aiwatar da Bincike

    A wajen aiwatar da wannan aiki an bi wasu dabaru da hanyoyi don gabatar da shi waɗanda suka haɗa da:

    (i) Hanyar nazarin zaune inda aka bi ɗakunan ajiye littattafai da kundaye digiri na uku da na biyu da na ɗaya da littattafai na ɗab’i aka karanta waɗannan ayyuka aka taƙaita su. Daga cikin ɗakunan karatun da aka ziyarta akwai na Jami’ar Bayero ta Kano da na Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo ta Sakkwato da na Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya da Jami’ar Maiduguri da Babbar Kwalejin Ilimi ta Abdullahi Augie ta Argungu da Babbar Kwalejin Ilimi ta Gwamnatin Tarayya a Kwantagora da Babbar Kwalejin Ilimi ta Gwamnatin Tarayya a Zariya da Babbar Kwalejin Ilimi ta Jihar Kaduna a Gidan-Waya Kafanchan. Haka kuma an ziyarci ɗakunan karatu na Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Hassan Usman a Katsina da Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Kaduna.

    (ii) Hanyar ziyartar ɗakunan ajiye kayan tarihi na jihohi waɗanda suka haɗa da Hukumomin Binciken Tarihi da Kyautata Al’adu na Jihohin Kano da Katsina da Zamfara da Sakkwato da Kabi da Neja da Nasarawa da Kaduna da Yobe da Borno da Adamawa da Bauci da kuma Gwambe. An kuma ziyarci Hukumar Adana Kayan Tarihi ta Ƙasa da take Kaduna. Haka kuma an ziyarci Cibiyar Binciken Tarihin Arewacin Nijeriya wadda take ƙarƙashin Sashen Koyar da Tarihi na Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya. An kuma ziyarci Cibiyar Nazarin Harsunan Nijeriya ta Jami’ar Bayero Kano da kuma Cibiyar Al’adun Gargajiya ta Jami’ar Ahmadu Bello Zariya.

    (iii) Hanyar amfani da takardun tambayoyi da aka rubuta da harshen Hausa waɗanda aka rarraba wa wasu Hausawa a sassa daban-daban na ƙasar Hausa da wasu garuruwan da suke maƙwabtaka da wannan ƙasa. Akwai kuma wadda aka rubuta da harshen Turanci aka rarraba wa musamman waɗanda ba Hausawa ba mazauna ƙasar Hausa da maƙwabtanta. An rarraba waɗannan takardu ga maza da mata, matasa da dattawa.

    iɓ) Hanyar yin hira da mutane daban-daban musamman wanzamai su kansu da ungozomomi da masana da manazarta da sauran jama’a waɗanda suka bayar da ra’ayoyinsu. Haka kuma an zauna cikin waɗannan wanzamai aka yi nazarin yadda suke aiwatar da aikace-aikacen wanzanci, musamman a garuruwan da ba a ƙasar Hausa ba.

    An gudanar da waɗannan hirarraki a garuruwan:

    Akwanga da Arugungu da Bauchi da Bida da Birnin-Kabi da Birnin-Ƙwanni da Damagaram da Damaturu da Daura da Gusau da Gwambe da Ibadan da Ilori da Jega da Jos da Kaduna da Kafanchan da Kagoro da Katsina da Keffi da Koko da Kwantagora da Lafiyar-Barebari da Lagos da Maiduguri da Manchok daMaraɗi da Minna da Potiskum da Sakkwato da Tassawa da Wase da Yamai da Yawuri da Yola da Zariya da Zuru.

    A taƙaice kamar yadda aka gani wannan babi na share fage ne don kuwa bayanan da suke cikinsa an yi su ne inda aka fito da hasashen binciken da manufofinsa da abubuwan da nazarin ya ƙunsa da kuma dabarun da aka yi amfani da su wajen tattara bayan da suka haifar da wannan kundi.

    Wannan bayani an ciro shi ne daga kundi mai taken SANA’AR WANZANCI DA SAUYE-SAUYEN ZAMANI JIYA DA YAU: NA BASHIR ALIYU SAFANA SALLAU

    KUNDIN BINCIKE WANDA AKA GABATAR A TSANGAYAR FASAHA DA ADDININ MUSULUNCI, SASHEN KOYAR DA HARSUNAN NIJERIYA, JAMI’AR BAYERO, KANO, DOMIN CIKA WANI ƁANGARE NA SAMUN DIGIRI NA UKU (Ph.D) A FANNIN HAUSA

     MAYU 2009/JUMADA ULA 1430

    Edita@rumasau-kallamu

     

     

  • Jigo Da Salo A Littafin Mace Mutum

    Jigo Da Salo A Littafin Mace Mutum

    Littafin Mace Mutum na Rahma A. Majid na magana ne kan danne haƙƙin mata da akan yi, musamman na daga abin da ya shafi al`adar Bahaushe. Marubuciyar ta ma fara ne da shimfiɗa labarin littafin da nuna yadda talauci kan jefa mafi yawa daga cikin mata su shiga harkar barace-barace, bayan sun sha wahala ko dai ta aure, wanda ya ƙi daɗi, ko kuma wadda ake yi a gargajiya.

    Ginin labarin ya fara daga ƙauye, yadda Fatima wadda aka fi sani da Godiya ke ba da labarin yadda rayuwa ke gudana a ƙauyensu, na yadda mazauna ƙauyen ke fama da rashin wayewar kai, da kuma irin yadda al’adun ƙauyen suka kasance na ko-in- kula dangane da abin da ya shafi mata gaba ɗaya, ga abin da take cewa:

    ‘Ta ɓangaren karatu dai mu mata babu ruwanmu, aure kawai muke jira.’

    Godiya dai ta ci gaba da nuna mana cewa su dai matan wannan ƙauyen ba su da wata ƙima ko daraja da suke da ita, domin duk wani aiki mata ke yi, kuma babu ruwan su da wani karatu, kuma don duhun jahilci, ko su mazan karatun addini kawai ake tura su gabas su yi, shi kuwa karatun zamani, suna samun labarin cewa ne kawai duk wanda ya yi zurfi cikinsa, to ya fantsama ne cikin duhun kafirci.

    Hasali ma, mutanen wannan ƙauyen ba su da wata alaƙa da mutanen birni, balle ma har su sami wata yarda ko aminta da wannan ilmin zamani da suke jin labarinsa, wanda na kafirci ne, sannan tsakaninsu da birnin ma tafiya ce mai tsawo, domin mota ma ba ta zuwa daga kasuwa sai kasuwa ta garin wadda ke ci mako- mako suke ganin mota. A taƙaice dai Godiya a nan tana ƙoƙarin nuna yadda jahilci, da duhun kai da kuma talauci ya yi wa mutanen ƙauyensu katutu.

    A haka dai rayuwa ta ci gaba a wannan ƙauyen, ta yadda har aka yi wani baƙon malami daga Nijeriya (wannan labarin ya faro ne daga wani ƙauye a Jamhuriyar Nijar), inda babansu Godiya ya yi wa wannan malamin kyautar Lami wato yayar Godiya. Duk dai a nan wurin mun ga yadda ita Lami ke yi wa ƙanwarta huɗubar kada ta bari a yi mata irin yadda aka yi mata, domin ta nuna irin yadda mata ke rayuwar bauta yayin da aka yi masu aure, musamman wanda ba su so.

    Kuma a haka Alaramma ya ɗauki amaryarsa, aka kuma ba su Godiya domin ta je ta zauna da amarya a can Nijeriya. A can Nijeriya kuma Lami ta je ta faɗa wa kishin kishiyoyi, domin Alaramma na da mata biyu, a haka kuma jininta ya shaƙu da na wadda Alaramma bai cika so a gidan ba, wannan duk sai suka taru suka sa wa Lami da `yar zamanta baƙin jini a gidan.

    Bayan zaman doya da manja da ake yi, da cikin da matan malam biyu suka samu, ciki kuwa har da Lami, kwatsam sai ga malam ya ƙara yin aure, wanda wannan ya ƙara tayar da hayaniya a gidan. Su kuma masu cikin, sai aka yi ta ƙoƙarin ɗura masu rubutun sha, yayin da Lami ta nemi a kai ta asibiti kuwa, ta ji abin da ba ta yi tsammani ba, domin kuwa ta ji cewar ko matar Maigari ma sai idan haihuwar ta zo mata da gardama sannan ake kai ta wurin unguwarzoma, ita ko ga ta matar malam tana maganar asibiti.

    A haka dai haihuwa ta zo wa Yaya Indo, bayan ta yi kwana huɗu tana yin naƙuda ta haihu, amma ɗan bai zo da rai ba, ita kuma wadda ta haihu jini ya ƙi tsaya mata, aka ɗauke ta aka kai wani asibitin ƙauye, an nemi jinin da za a ƙara mata, amma duk wanda aka gwada cikin waɗanda suka kai ta asibitin su ma suna neman ƙarin jini, a haka dai matar malam ta mutu.

    Ita ma yayar Godiya da ta fara naƙudar, amma ta zo da gardama sai aka yi mata yankan gishiri, wanda wannan ya jefa ta cikin mawuyacin hali, wanda ya sanya dole sai an kai ta birni don yin tiyata, ta mutu a birnin, amma da suka dawo ba a gaya wa Godiya ba, sai daga baya malam ya ce su shirya a kai ta gida, bayan zuwansu ƙauyensu ne ta fahimci cewar Lami ta mutu.

    A ƙauyensu ɗin ta sake ganin wannan malamar asibitin wadda ta ke zuwa ƙauyensu malam tana ba su magunguna, wato malama Zubaida, ta yi mata bayanin duk abin da ya faru, sannan ta nemi da ta tafi da ita, domin ta ji ana cewa ita za a mayar wa malam, amma ta rarrashe ta, daga ƙarshe dai da maganar auren Godiya da malam ta tsananta, sai ita Godiya ta ɗauki shawarar da yayarta mai mutuwa ta ba ta, na ta gudu ta bar ƙauyensu.

    Ta gudu ɗin, kuma kamar arashi, sai direban malama Zubaida ya tsince ta ya kai ta wurin malama, wadda dama ta yi ta roƙon da ta gudu da ita. Daga ƙarshe dai ganin Godiya za ta shiga wani hali, tun da ta sha alwashi ko da malamar ba ta tafi da ita ba za ta gudu, malamar ta aminta za ta tafi da ita ɗin, amma bisa sharaɗin cewa bayan ta gama makaranta za ta dawo ƙauyensu, wato lokacin da ta san ciwon kanta, kuma lokacin da ba wata barazana da wani zai yi mata.

    Rayuwar Godiya, wadda yanzu sunanta ya dawo Fati a birni ya shiga cikin wani sabon salo, domin kuwa ta san yadda rayuwa take gudana a birni, ta shiga makaranta, har ya kai ga ta yi jarabawar JAMB domin samun ci gaba da karatu, a cikin wannan halin ne malama Zubaida ta nemi haɗa auren ɗanta Bashir da Fati, saboda ta lura ɗan nata na neman shiga cikin rayuwar Fati ɗin, shi kuma ya nemi jajircewa.

    A dai haka Fati ta samu shiga jami`ar Abuja, yayin da shirye-shiryen aurenta da Bashir ya kankama, amma malama ta ce sai an je ƙauyensu Godiya an bayyana musu. Sun dai je ƙauyensu Godiya ɗin an kuma iske abubuwa da dama sun faru, wasu masu daɗin ji, wasu kuma akasin haka.

    Bayan dawowarsu gida Nijeriya an ɗaura auren Bashir da kuma Fati (Godiya), amma dai a tsaitsaye, domin ga alama dai Bashir ba ya son auren, ita kuma Fati ta fara karatunta a lokacin. Kuma har zuwa lokacin da ta gama bautar ƙasa abubuwa tsakaninta da mijinta ba su sauya ba, a haka dai ta haƙura.

    Sun zauna tsawon lokaci har zuwa sadda malama Zubaida ta rasu, abubuwa dai ba su sauya ba, kuma saboda tsananin halin da Fati ta shiga tsakaninta da mijinta, ya sanya har ta yarda da abokin mijinta suka rinƙa tarayya a lokacin da mijin nata yake Abuja da amaryar da ya aura. Auren Bashir da Fati ya zo ƙarshe lokacin da ya gane suna yin lalata, ita da abokinsa lauya, bayan ya sake ta, ta nemi lauya ya aure ta shi kuma ya turje da nuna cewa idan ya aure ta Bashir zai samu damar nuna wa duniya cewar dama mazinata ne.

    Bayan ƙin auren ta da lauya ya yi, Fati ta ƙara shiga cikin wani ƙangin na gaba-kura-baya-sayaki na yadda za ta tafiyar da rayuwarta, a haka dai ta yanke shawarar barin gidan da lauya ya kama mata, ta tafi Sakkwato wurin wata Hajiya Hassana wadda ta sani. A Sakkwato bayan jin labarinta da Hajiya ta yi, ta tausaya mata, ta kuma ba ta wurin zama, sannan kuma ta nemar mata aiki a makaranatar kwamfuta ta mata da wata tsohuwar kwamishiniya ta buɗe a garin Sakkwato, amma daga bisani aka bar koyarwar, sai dai shiga yanar gizo.

    Tsaron da take yi a wurin ne  ya sa ta samu wani basarake ya nemi auren ta, ta dai amince an yi auren, daga baya take ji a wurin wannan basaraken cewa wai malamin duba ne ya ce za su haɗu, kuma su yi aure saboda shi haihuwa yake nema don ya samu mai gadonsa. Bayan auren ta da basarake an yi soyayya, kuma ta ga kula har take tunanin cewa ko ramuwa ce na soyayyar da ba ta gani ba a baya, har zuwa lokacin da ta samu ciki, har ya kai ga haihuwa, amma abin da ya ɓata harkar shi ne da ta haifi mace, wannan haihuwa ta mace da ta yi kusan ita ta wargaza jin daɗinta da kuma soyayyar da ta gani a baya.

    Zama bai ga Fati ba domin an yi zargin cewa ma cikin ba na Ciroma ba ne, domin dai bai nan ya yi tafiya, bayan ya dawo aka ce tana da ciki, wannan shi ya sanya ta sake yin hijira ta bar Sakkwato, ta nufi Kano bisa hanyarta ta zuwa Legas. Ta isa Legas cikin jirgin ƙasa, kuma ta faɗa hannun innar ‘yan Arewa wato Inna Yaya mai sai da abinci, inda ta kasance mai ba da tikiti idan an ci abinci, amma zama bai yi tsawo ba, domin da uwar ɗakinta ta haɗa ta da wani don ya zama farkanta, ita kuma ta ƙi, sai ta fatattake ta.

    Ita kuma ta koma Zango, gidan wata Mai alkubus, inda ta zauna kuma har daga baya ma ta buɗe wurin karantar da yara, amma nan ma ba da daɗewa ba ta wargaje, sai daga baya aka samar mata tuƙa tuwo a wani gidan sai da abinci, kuma daga fara aikinta a wannan gidan tuwon ba da daɗewa ba wani ciwo ya taso mata a gabanta, wanda likitoci suka ce sai an yi mata tiyata, su kuma ba su da waɗannan kuɗin, wannan ciwon dai shi ne ya yi ajalin Godiya, ta rasu ta bar ɗiyarta guda ɗaya Amina.

    Ɗiyar da Fati ta bari wato Amina ta ci gaba da rayuwa a hannun Mai alkubus, har zuwa lokacin da rikicin ƙabilanci ya kaure, Aminar na makaranta yayin da ta dawo gida sai ta iske an fasa gidan nasu, wannan shi ya yi sanadiyar komawarta hannun wata wai ita yaya Bilki, ita ta ci gaba da rainon ta a Legas ɗin har zuwa lokacin da ta gama makaranta. Ta bar wurin mama Bilki saboda ta ƙi yi mata tallar ruwa, daga baya ta haɗu da wasu matasan `yan jami`a, mace da namiji waɗanda suka tafi da ita gidansu na gado suka ci gaba da zama.

    Daga baya dai Amina ta sake haɗuwa da Mai alkubus, kuma ta samu gurbin karatu a jami`ar Ahmadu Bello da ke Zariya. Amina dai ta gama jami`ar Ahmadu Bello, bayan abubuwa da dama da suka faru. A ciki ta yi karatu tuƙuru, ta kuma ƙi jinin da ƙaunar duk wani ɗa namiji bisa dalilinta na rashin tausai da riƙon amana. Ta yi ƙawaye `yan birni daga ciki har da Ummi, wadda daga baya saurayin Ummin ya dawo wa Amina bisa dalilinsa na cewa Ummin ba `yar goyo ba ce, wannan kuma ya haifar da rigingimu, iri-iri, amma dai duk da haka ta gama karatunta na likitanci da sakamako mai kyau. Sannan daga ƙarshe ta auri Abbas, wanda shi ne tsohon saurayin Ummi.

    A dunƙule, dai bayan auren Amina da Abbas rayuwa ta yi daɗi, kuma Amina ta ƙaddamar da shirinta na neman `yancin mata wanda shi ne ƙashin bayan littafin.

    Jigo A Littafin Mace Mutum

    Kai tsaye duk wanda ya fara karanta wannan littafin zai san jigonsa neman haƙƙin mata ne. Duk da akwai ƙananan jigogi, amma dai wannan jigon shi ne kan gaba. A farkon buɗe littafin maganar babban jigon ce ta fara fitowa fili inda wata `yar kare haƙƙin mata ta rubuta buɗaɗɗiyar wasiƙa zuwa ga wata ƙungiya mai iƙirarin kare matan mai suna HATTARA! CI DA GUMIN MATA !

    Sannan idan muka kalli irin wahalhalun da marubuciyar ta ce Godiya (wato mahaifiyar Amina) ta sha, a wurare da dama, an nuna yadda maza ke tauye haƙƙin mata ne. Dubi rayuwarta ta farko a ƙauyensu, sannan lokacin da ta dawo birni irin yadda Bashir ya yi faman neman ɓata rayuwarta kafin daga baya mahaifiyarsa ta tilasta masa auren Fatimar.

    Haka ma ko bayan auren an nuna irin azabar da ta yi ta sha, har zuwa lokacin da ta auri basarake a Sakkwato, nan ma duk an nuna yadda aka danne haƙƙinta, kai a cikin littafin, a rayuwar Godiya kaf, an nuna cewa ta rayu cikin bautar maza, har zuwa lokacin da ta mutu, ɗiyarta ta karɓa.

    Jigon dai ya fara fitowa fili ne lokacin da Abbas ya nemi ta amince su yi aure, wato lokacin da take labarta masa irin wahalar da mahaifiyarta ta sha a hannun maza, ta ce:

    ‘… don haka ba na son maza, don ba sa son mu. Ba su son mata, amma sun ƙi fitowa fili su nuna mana ba sa son mu, ba don komi ba sai don imaninsu da cewa mu ba mutane ba ne, don haka ba za mu fahimci ƙiyayya ba. Yaudarar mu nishaɗi ce… ? Yaudararmu sana’a ce, mai riba. Yaudararmu kamar halaccin lallashin dabbar da ake son a kama ne domin a yanka a ci namanta…. Suna zuba mana kayan kwaɗayi, sai mun shagala, muna ci kamar dabbobi, sai mu ji harbi.

    Wasu sun mayar da mu karnukan farauta. Mu suke tasawa a gaba wajen kamo `yan uwanmu a gabanmu su wulaƙanta. Su auri mai mutunci, ba don su yi mutunci ba, sai domin ta renar masu mutuncin gidansu, su suna waje suna yaga mutuncin `yar uwarta. Wasu suna mana wayo, sun ce sun sakar mana wuya, mu sha ruwa, bayan sun sakar mana tarko a ƙafa, suna talla da mu, mu ne sana`ar da ke ciyar da su, ta shayar da su, amma ba mu sani ba, muna zaton su ke ba mu abin da muke ba su. Muna zaton mu ke dogara da su, ashe su ke dogara da mu. Sun sanya mu mun fi dabba dabbanci’.

    A nan wurin duk abin da Amina take nunawa bai wuce irin abin nan da Bahaushe ke cewa na an ci moriyar ganga, an ya da kwaurenta ba, domin duk abin da take cewa bai wuce rashin nuna yarda da namiji ba, ko kuma irin yadda maza ke amfana da mata, amma a koma a rinƙa cewa mata ba su da amfani, ko kuma a yaudare su, ko wani abu makamancin haka.

    Jigon littafin bai fito fili sosai ba sai lokacin da Amina ta zama cikakkiyar mace, lokacin da ta gogu da boko, lokacin da suka kafa ƙungiyarsu ta fitattun mata a arewa, kuma lokacin da suka tashi tsaye don neman `yancin mata, ga abin da suke cewa:

    ‘… Ba gasa muke ba… Ba hassada muke ba. Haƙƙinmu muke nema. Amma ba za mu samu ba, sai mafi akasarin mata sun san suna da haƙƙin da aka danne masu. To ta yaya za mu yi haka in ba da ilmi da ilimantarwa ba ? Ke nan ashe ilmi ne kan gaba a harkarmu.’

    Kai tsaye mun fahimci cewar `yancin mata kawai suke son ƙwatowa daga danne shi da ake yi. Kamar yadda muka ce akwai ƙananan jigogin da suka tallafa wa fitowar babban jigon, kamar jigon soyayya da jigon haƙuri da sauran su.

    Salo A Littafin Mace Mutum

    Salon littafin duk da cewar mai sauƙi ne, amma yana da ɗan ruɗarwa, domin kuwa an yi amfani da wani salon kwan-gaba-kwan-baya daga farkon littafin domin fara nuna inda aka dosa, da yake dama so ake a yaƙi danne haƙƙin mata, sai aka ɗauko salon buɗe littafin da yadda mata da sauran mabarata suka cika garuruwan ƙasar Hausa. Sannan Hausar da aka yi amfani da ita mai sauƙin ganewa ce, ga karin maganganu da aka yi amfani da su bila haddin.

    Wani salon kuma da ya bambanta wannan littafin da wasu littatafai shi ne yadda a sashi na biyu na littafin sai aka nuna cewa kamar Amina ta gama karanta labarin mahaifiyarta ne ga mai karatu, ba shakka wannan wani salo ne wanda ba duka marubuta ke amfani da shi. Haka kuma an yi amfani da kalamai da lafuzza masu sauƙi da daɗin fahimta. Kuma an yi amfani da salon fara rayuwa daga ƙauye zuwa birni.

    Naɗewa

    A wannan babin an yi nazarin littattafai guda huɗu; Rabin Raina da So Jinin Jiki da Ina Son Sa Haka da kuma littafin Mace Mutum ta fuskar jigo da salo domin fito da wancan fasalin na adabin Kasuwar Kano da muka gani.

    Wannan bayani an ciro shi ne daga rubutaccen kundi mai taken: ADABIN KASUWAR KANO: Nazari da Sharhi Game da Ƙagaggun Labaran Hausa (1984-2008) wanda Bashir Abu Sabe 07/211111002 (M.A Hausa Studies) USMANU ƊANFODIYO UNIVERSITY, SOKOTO, NIGERIA ya wallafa.

    Domin karanta Sharhin Littafin Ina Son Sa Haka danna nan

    Edita@rumasau-kallamu

     

     

  • Yadda Ake Zikiri Yayin Fita Daga Gida

    Yadda Ake Zikiri Yayin Fita Daga Gida

    “Bismillaahi Tawakkaltu alallaahi walaa haula walaa ƙuwwata illaa bil-laahi”.

    {Da sunan Allah (nake fita), na dogara ga Allah, kuma babu dabara, babu ƙarfi sai da Allah}.

    “Allahumma inni A’uzu bika an adhilla au udhilla, au azhilla au uzhalla, au azlima au uzlama au ajhala au yujhala alayya”.

    {Ya Allah! Ina neman tsarinka daga na ɓata ko a ɓatar da ni, ko na zame ko a zamar da ni, ko na yi zalunci ko a zalunce ni, ko na yi wauta ko a yi mini wauta}.

    Domin karanta cikakken bayani akan Zikiri Yayin Shiga Gida danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani akan Ladubban Addu’a A Musulunci danna nan.

    Wannan bayanin anciro shi ne daga littafin Garkuwar Musulmi Ta Addu’o’i Daga Alƙur’ani Da Sunna; wanda Sheikh Sa’id Ibn Ali Ibn Wahf Al-Kahdani ya wallafa shi; Domin karanta cikakken littafin danna nan.

  • Yadda Falalar Zikiri Bayan Sallar Asuba Har Zuwa Ɓullowar Rana Ya Ke

    Yadda Falalar Zikiri Bayan Sallar Asuba Har Zuwa Ɓullowar Rana Ya Ke

    An karɓo daga Anas ɗan Malik (Radiyallahu Anhu) yace; Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasalam) yace; “Wanda ya yi sallar asuba a cikin jam’i, sannan ya zauna yana ambaton Allah har rana ta ɓullo; sannan ya yi salla raka’a biyu za a ba shi lada hajji da umra cikakku, cikakku, cikakku (Tirmizi 586).

    Domin karanta cikakken bayani a kan Yadda Falalar La Ilaha Ilallahu Ta Ke danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Falalar Ƙulhuwallahu Ahad danna nan.

    Wannan bayani an ciro shi ne daga littafin Ingantattun Nafiloli Da Falalarsu; wanda Usman Abubakar Muhammad (Shehu Mansur Dala) ya wallafa shi; Domin karanta cikakken littafin danna nan.

  • Tatsuniyar Ɗankaɗafi

    Tatsuniyar Ɗankaɗafi

    Ga ta nan ga ta nan ku.

    Wata mata ce dai ba ta taɓa haihuwa ba, tun da ta ke. Sai ta ce, ‘Allah, ba ka ba ni ɗa ba, ka ba ni ko Ɗankaɗafi ne?’
    Allah sai ya karɓi roƙonta, sai ta haifi ɗanta namiji.

    Shi ke nan, yaro yana nan yana girma. Sai ran nan ta goya shi. Da ta gaji da goyo, sai ta ce da shi, ‘To, sauko ka kwanta Ɗan inna’.

    Sai ya ce, ‘Mhm, mn, a baya’.
    Ta kuma cewa, ‘Sauko a wanke maka ido.’
    Ya ce, ‘Mhm, mn, a baya’.
    Kome dai ta ce sai ya ce, ‘Mhm, mn, a baya’.

    Sai ran nan ta ce, ‘Kai ni dai na gaji; Gun malami za ni ko yana da abin da zai yi mini in rabu da ɗan nan. Na gaji.’

    Sai ta je wajen malami.
    Malami ya ce, ‘Duk abin da aka gaya miki kya iya?’
    Sai ta ce, ‘I, zan iya’.
    Sannan ya ce, ‘To, sayo sa guda ki kawo mini’.
    Sai ta sayo sa ta kai wa malami.
    Sai ya ce, ‘biyu za a raba, ki ɗauki rabi, in ɗauki rabi’.

    Ta ce, ‘To’,
    Aka raba naman sa kashi biyu, Malami ya ɗauki rabi, ta ɗauki rabi.
    Sai ya ce, ‘Ki soya wannan ki tafi da shi daji ki haɗa da majanyi da zane. in kin sauko yaron yana cin naman sai ki gudo ki baro shi can’.

    Sai ta ce, ‘To’.

    Taje gida ta soya nama. Sai ta tafi daji da shi. Ta ce, ‘Ɗan Inna, sauko ka ci nama’.
    Sai ya ce, ‘Mn, a baya’.
    Sai ta ce, ‘Ga naman naka nan sauko ka ci’.
    Sai ya sauko. Da ya sauko yana cin naman, sai uwar ta waiga; ta waiga ba ta ga kowa ba; sai ta gudu ta bar shi da majanyi da zane.

    Fatar bayanta har ta kwaye saboda goyo.
    Shi ke nan sai ga kura, ita da ‘yan uwanta suna wasa. Sai ta ce, ‘Ɗan ƙanena, ɗan ƙanena, sam min ɗan naman in ci in goya ka.
    Shi ke nan, ya ba ta.

    Ta ɗauke shi ta goya shi suna wasa. Sai ta ce, ‘Sauko in huta’.
    Sai ya ce, ‘Mn, a baya’.
    Kome dai ta ce, sai ya ce, ‘Mn, a baya’.

    Da ta yi ta yi ta cire shi daga bayanta ya ƙi; sai ta kira ‘yan uwanta su cire mata shi. Da suka zo garin cire shi sai fatar bayan kura ta ciro, ta ce, ‘Na gamu da jaraba’.
    Sai suka gudu suka bar shi nan.

    Can sai ga dodo ya zo ya ɗauke shi ya ɗora a bayan dokinsa, shi kuma yana gaba yana cewa:

    Za ni za ni za ni,
    Za ni za ni,
    Za ni da namana,
    Za ni da namana,
    Za ni da kai sharɓa,
    Ɗankaɗafi za ni da namana

    Suna cikin tafiya a daji, sai Gizo ya ga dodo da yaro, sai ya sauke yaron, ya ajiye a ƙasa.
    Shi kuma ya hau kan dokin dodo.
    Dodo bai sani ba yana ta waƙa.

    Shi ke nan sai ana ta tafiya da Gizo; sai kurciya ta ga Gizon a kan dokin dodo sun kusa da kogi, sai ta ce da Gizo; ‘Ku ne a yi muku rana, ku yi wa mutum dare.
    Gizo ya ce, ‘A’a, ba zan miki ba’.

    Shi ke nan, sai kurciya ta ɗauke Gizo a fiffikenta.
    Da dodo ya je bakin kogi, sai ya waiga don ya ɗauko yaro ya cinye ya sha ruwa; sai ya ga ba kome. Baƙin ciki sai ya sa shi ya faɗa cikin ruwan nan, ya zama gawa.

    Shi kuwa Ɗankaɗafi kura ta cinye shi a can dajin da aka ajiye shi.
    Shi ke nan.

    Ƙurunƙus.

    Domin karanta Tatsuniyar Gizo Da Giwa danna nan.

    Domin karanta Tatsuniyar Yarinya Da Dodanni danna nan.

    Edita@rumasau-kallamu

  • Kiɗa Da Waƙoƙin Makaɗa Musa Ɗanƙwairo

    Kiɗa Da Waƙoƙin Makaɗa Musa Ɗanƙwairo

    Kiɗa da waƙa ta baka wani fage ne wanda yawancin makaɗa masu tunani da ƙwaƙwalwa da fasahar shirya kalmomi; musamman ta fuskar zaɓensu da baiwa ta hangen nesa da furuci mai cusa tarbiyya ta ruhi da ta gangar jiki suke aiwatarwa ga al’ummominsu.

    Wasu ladubban waƙoƙin baka sun haɗa da bayanai na tarbiyyatarwa da faɗakarwa da jan hankali; zuwa ga kyawawan ayyuka da halaye na gari, musamman waɗanda al’umma da addinin al’umma suke aiki da su.

    Domin haka, waƙar baka ta ƙunshi wasu matakai da sigogi na aiwatarwa wato shiryawa da ƙullawa; da kuma rerawa tare da sadar da ita ga al’umma. Kuma waɗannan su ne suke ɗaukar hankalin al’umma wajen sauraron waƙoƙin baka da aiki da su.

    Makaɗin baka yakan zama tilas ya san waɗannan ladubban waƙar baka; waɗanda Allahu yake yi masa ilhama da su ta hanyoyin koyo da biyayya ko jibilliyya ko bisa wata buƙata ta rayuwa.

    Domin karanta cikakken bayani akan Musa Ɗanƙwairo a Koyo da Biyayyar Waƙa danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani akan Mawaƙan Da Ake Yi Wa Kiɗan Fiyano danna nan.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin; Tarihin Rayuwa Da Halifofin Makaɗa Alhaji Musa Ɗanƙwairo Maradun A Aiwatarwa Da Sadar Da Waƙoƙin Baka Na Hausa; wanda Prof. Sa’idu Muhammad Gusau ya wallafa shi; domin karanta cikakken Littafin danna nan.

  • Tarihin Sheikh Malam Muhammad Ɗan Almajiri

    Tarihin Sheikh Malam Muhammad Ɗan Almajiri

    An haifi babban malami Muhammad ɗan Malam Adamu a Ƙasar Kazaure. Malam Muhammad ɗan Almajiri ya fara karatu a gaban mahaifinsa Malam Adamu.

    Malam ya yi tafiye-tafiyen neman Alƙur’ani har sai da ya dangana da garin Bajanwa a ƙasar Katsina wajen Malam AbdusSamad a inda ya yi karatun Alƙur’ani wurinsa. Daga nan ne Malam AbdusSamad ya tafi da shi izuwa garin Rawayau wurin mashahurin malamin nan Malam Goji. Daga Rawayau, ya bazama izuwa Unguwar Ciranci cikin Birnin Katsina don ƙara gogewa da Alƙur’ani.

    Malam Ɗan Almajiri ya zo Kano a inda ya sauka a unguwar Fagge wajen babban malami Malam Ibrahim Badamagare a inda ya karanci fiƙhu da Nahwu. Malaman Sheikh Ɗan-almajiri a Kano sun haɗa da Malam tijjani Zangon Barebari. Malam ya rasu a shekarar 1960.

    Makarantar marigayi Ɗan Almajiri ta yi fice tsakanin makarantun Alƙur’ani da yawan almajirai da tsare-tsare masu ban sha’awa. Wan nan ya sa ta yi rassa da ɓangarori daban-dabun. An kafa wan nan makaranta ne a shekarar 1945.

    Almajiran Malam Ɗan-almajiri sun haɗa da Malam Ɗan-Inna da ‘ya’yansa. Malam ya rasu ya bar ‘ya’ya 14; bakwai maza bakwai mata. Bayan rasuwar sa sai Malam Haruna Rashid ya jiɓinci gudanar da ita kuma ta cigaba da bunƙasa a hannunsa da hannun wasu almajiransa musamman a wasu jihohi cikin tarayyar Nijeriya. Kaɗan daga rassan makarantar marigayi Malam Ɗan almajiri su ne:-

    – Makarantar Alƙur’ani da Islamiyya, Kaduna
    – Makarantar Alƙur’ani da Islamiyya, Katsina
    – Makarantar Alƙur’ani da Islamiyya, Bauchi
    – Makarantar Alƙur’ani da Islamiyya, Lagos

    Domin karanta cikakken bayani akan Tarihin Sheikh Is’haƙ Rabi’u Khadimul Alƙur’ani danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani akan Asalin Sunan Ƙabilar Ƙuraish danna nan.

    Wannan bayanin anciro shi ne daga Littafin Tsarin Tsangayun Alƙu’ani A Arewacin Najeriya Tarihin Su Da Zamantakewar Su Da Hanyoyin Raya Su; wanda Dr. Sunusi Iguda Ƙ/Nasarawa ya wallafa shi; domin karanta cikakken Littafin danna nan.

  • Gaskiyar Abinda Ya Faru Na Shahadar Husaini (Radiyallahu Anhu)

    Gaskiyar Abinda Ya Faru Na Shahadar Husaini (Radiyallahu Anhu)

    A wannan gaɓa zan bayyana gaskiyar abinda ya faru a taƙaice dangane da shahadar husaini (Radiyallahu Anhu) kamar yadda amintattun masana tarihi suka bayyana.

    Mutanen Iraƙi sun sami labarin cewa Hussaini (Radiyallahu Anhu) bai yi wa yazidu mubaya’a ba a shekara ta 60 daga hijira, saboda haka suka yi ta aika manzanni da wasiƙu zuwa gareshi, suna gayyatarsa ya zo don su yi masa mubaya’a, saboda su ba sa bayan yazidu har ma da halifofin da suka gabace shi, su kawai Aliyu da jikokinsa suke buƙata yawan waɗannan wasiƙu ya kai ɗari biyar.

    Da husaini (Radiyallahu Anhu) ya ga haka, sai ya tura Muslim ɗan Aƙilu don ya binciki gaskiyar lamarin. Da farko da ya je sai ya ga dubban mutane suna kan wannan ra’aiyi kuma da alama da gaske suke kuma gidan Hani ɗan Urwata shine ya zama cibiyar yin mubaya’a ga husaini (Radiyallahu Anhu).

    Da yazidu ya sami labari, sai ya tura gwamnansa na Basra Ubaidallahi Ibn Ziyad Kufa, ya kuma kuma haɗa masa da Basrar, domin ya shawo kan wannan matsala, ya hana mutanen Kufa yin tawaye, amma bai ba shi umarnin ya kashe Husaini ba.

    Da ya je Kufa ya yi zurfin bincike har ya gano cewa a gidan Hani Ibn Urwah ake kitsa komai. Ubaidullah Ibn Ziyadu ya yi fito-na-fito ya yi jawabai ga waɗannan dakaru yana razana su da ƙarfin rundunar Sham, yana kuma lasa masu zuma da yi musu alƙawarirrika na kuɗi da muƙami nan dai dakaru suka rinƙa zare jiki suna komawa cikin rundunar zaiyadu, kafin ƙanƙanin lokaci cikin mutum dubu huɗu sai mutum talatin kacal ne suka ragu a bayan Muslim, suma kafin faɗuwar rana sun canza sheƙa.

    Shine ya sa aka kama Muslim Ubaidullah ya ba da umarni a kashe shi sai ya nemi a bashi izini ya rubuta wasiƙa zuwa Husaini (Radiyallahu Anhu) sai aka ba shi izini ya rubutawa Husaini cewa: “ka koma gida da iyalanka, kada ka ruɗu da ƙarerayin mutanen Kufa, makaryatane”. Bayan kuwa a da ya rubuta masa cewa yayi sauri ya taho Kufa saboda komai ya yi dai dai. Ubaidullah ya sa aka kashe Muslim Ibn Akil.

    Shi kuwa Husaini (Radiyallahu Anhu) tuni ya fito, duk da yunƙurin da manyan sahabbai suka yi domin su hana shi tafiya Kufa, sun yi masa iya nasiha, amma ƙaddara ta riga fata.

    Ibn Umar. (Radiyallahu Anhu) ya ce: da shi “Bari in gaya maka wani hadisi, jibrilu ya zo wurin manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wa Sallam) ya ba shi zaɓi tsakanin duniya da lahira, sai ya zaɓi lahira, kai kuwa tsoka ne daga gare shi, saboda haka, wallahi babu wani a cikinku, da zai sami mulki har abada, kuma Allah ya yi muku haka ne, saboda ya tanadar muku abinda ya fi Alheri a gurinku.

    Amma husaini bai gamsu da wannan ba ya yi gaba sai Ibn Umar ya rungume shi ya fashe da kuka, yace ina bankwana da wanda za a kashe.

    Ibn Abbas (Radiyallahu Anhu) ya ce da shi: “ba don kar mu yi abin faɗa ba, da sai na hana ka tafiya, koda kuwa za mu yi kokawa”.
    Abdullahi Ibn Zubair ya ce: “me za ka yi a wurin waɗanda suka kashe mahaifinka, su ka soki wanka da wuƙa a cinya?

    Abdullahi ɗan Amar ɗan As (Radiyallahu Anhu) yace: “Husaini ya yi gaggawa zuwa ƙaddararsa, wallahi da na tarar da shi da na hana shi tafiya, sai dai in ya fi ƙarfi na”.

    Tun akan hanya Husaini (Radiyallahu Anhu) ya sami labarin an kashe Muslim Ibn Aƙil da kuma yadda mutanen Kufa suka ba da shi, sai ya juya akalar tafiyarsa zuwa Sham wurin Yazid, amma sai ya yi kiciɓus da rundunar ɗan Ziyadu a ƙarƙashin jagorancin Umar Ibn Sa’ad da Shimmar Ibn Zil Jaushan da Husaini Ibn Tamim.

    Sai Husaini ya sauka daga dokinsa yana yi musu magiya su dubi girman Allah su ƙyale shi da ya kai kansa wurin Yazidu ya yi masa mubaya’a, saboda ya san ba zai so a kasha shi ba, ko ya koma Madina ko ya tafi jihadi har ƙarshen rayuwarsa.

    Amma suka ƙi bashi ɗaya daga waɗannan abubuwan guda uku, suka ce sai dai ya yarda yana ƙarƙashin hukuncin ɗan Ziyadu sai abin da ya ga dama ya yi da shi.

    Har sai da wani daga cikin kwamandodin ɗan Ziyadu mai suna Al-Huff Ibn Yazid ya ce: “Don me za ku ƙi yarda da wannan tayi da suka yi muku? Ai ko Turkawan Lailamawa suka nemi ɗayan waɗannan abubuwa kwa yi musu”? Amma a banza ba su saurare shi ba. Da ya ga haka, sai ya miƙa wuya ga rundunar Husaini (Radiyallahu Anhu) har ya kashe mutum biyu daga cikin rundunar ɗan Ziyad, sannan suka kashe shi. Ya Allah ka yi masa rahama.

    In ana maganar yawa ne, ba za a iya kwatanta yawan rundunar ɗan Ziyad da dakarun Husaini (Radiyallahu Anhu) ba, amma fa duk inda jarumai suka kai sun wuce nan, sun yi bajinta sai da suka ƙare gaba ɗayansu akan bada kariya ga Husaini (Radiyallahu Anhu) ƙarshe ya rage sai shi kaɗai kamar zaki a cikin dubban mayaƙa, ya yi kansu amma sarkin yawa yafi sarkin ƙarfi.

    Duk da haka kowane ɗaya daga wannan runduna yana shayin, afkawa Husaini (Radiyallahu Anhu) har sai da wani tsagera mai suna Shimmar Ibn Zil Jaushan ya yi tsaurin ido ya cakawa husaini mashi, ya faɗo ƙasa daga kan dokinsa, daga nan suka rufar masa da sara da suka har suka kashe shi. An ce shi Shimmar ɗin nan shine ya ciro kan Husaini waɗansu kuwa sun ce Sinan Ibn Anas Annakh’i ne.
    Allahu Akbar! Allahu Akbar!! Allahu Akbar!!!

    Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un”.

    Haƙiƙa Husaini (Radiyallahu Anhu) da waɗanda suke tare da shi sun rubauta sun kasa sun sayar sun ci riba. Su kuwa waɗannan ‘yan ta’adda sun yi hasara. Ya Allah ka jaddada rahama ga Husaini (Radiyallahu Anhu) da waɗanda suka yi shahada tare da shi amin.

    Domin karanta cikakken bayani akan Sauran Waɗanda Suka Yi Shahada Tare Da Husaini (Radiyallahu Anhu) danna nan.

    Wannan bayanin anciro shi ne daga Littafin Gaskiyar Magana Akan Ashura wanda Shehu Mansur Dala ya wallafa shi; domin karanta cikakken Littafin danna nan.