Tag: yadda ake

  • Haramun Ne Mata Su Halarci Husainiyya

    Haramun Ne Mata Su Halarci Husainiyya

    A baya kaɗan mun kawo wasiyyar da Imamu Husaini ya yi wa mata a gab da shahadarsa har ila yau a cikin wasiyyar ya ce:

    “Yake ‘yar uwata, ya ke Ummu Kulsum, ya ke Fatima; ya ke Rabab ku nutsu idan na mutu kada ku yaga tufafinku, kada ku ya ƙushe fuskokinku.

    Sannan kuma Abul Hasan da Abu Ja’afar (Alaihis Salam) sun faɗa akan fassarar faɗin Allah Ta’ala; “Kuma kada Su (mata) su saɓa maka a kan wani abin aihair? ya ce: “Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wa Sallam) ya gayawa Fatima (Alaihis Salam) cewa; “Idan na mutu kada ki yakushe fuskarki, kada ki cizge gashinki, kada ki yi min kururuwa, kada ki yi makoki. Sai ya ce wannan shi ne ma’anar “abin da Allah ya ke faɗa”.

    Abu Abdullah (Alaihis Salam) ya ce; “Ma’anar wannan ayar ita ce kada su yaga tufafinsu; kada su yakushe fiskokinsu, kada su yi ihu da kururuwa, kada su tsaya a kan ƙabari.

    An karɓo daga Abu Sa’id Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wa Sallam) ya ce; “ya la’anci mace mai rera-kuka da mai sauraro”

    To ‘yan uwa mata (sisters) kun ji abinda Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wa Sallam); da Imamai (Alaihis Salam) suka faɗa a kan matan da suke halartar Husainiyya. Shin ko za ku bi maganar Manzo (Sallallahu Alaihi Wa Sallam) da ta Imamai ku hutar da kawunanku daga zarya da kuke ba dare ba rana; domin ku kaucewa fushin Allah ta’ala da Manzo (Sallallahu Alaihi Wa Sallam). ‘Yar uwa ki bi gaskiya ki bi Allah da Manzo (Sallallahu Alaihi Wa Sallam); ba jagorori ba waɗanda su suna huce cikin raɓa suna kwasar girki ku kuma kullum kuna kan hanya.

    Ni dai nasiha nake yi miki. Kuma gyara kayanka…

    Domin karanta cikakken bayani a kan Tarihi Da Falalar Husaini (Radiyallahu Anhu) A Taƙaice danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kanFalalar Ba wa Ɗan Uwa Sadaƙa danna nan.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Gaskiyar Magana Akan Ashura wanda Shehu Mansur Dala ya wallafa shi; domin karanta cikakken Littafin danna nan.

  • Yadda Ake Mandi Rice

    Yadda Ake Mandi Rice

    Matso kusa ki zauna. Yau na taho muku da yadda ake yin MANDI RICE.

    ABUBUWAN BUƘATA.

    • Shinkafa (Basmati rice).
    • Nama ko Kaza.
    • Albasa
    • tumatur
    • man zaitun ko man salak
    • tafarnuwa
    • citta
    • cinamon stick
    • curry
    • thyme
    • lemon tsami
    • seasoning.
    • Coal (gawayi).

    YADDA AKE HAƊAWA.

    Mataki na farko za ki wanke naman kazarki ko nama ki zuba ɗan gishiri, lemun tsami, tafarnuwa, citta, thyme. Ki dafa shi da ɗan ruwan zafi har sai ya yi laushi ya fara zarewa amma kar ya narke sosai.Kki ajiye ruwan naman don dafa shinkafar.

    Mataki na 2:

    Ki wanke shinkafar ki, ki barta ta jiƙu na minti 30. Ki soya albasarki da tafarnuwa a cikin mai, sannan ki zuba tumatur markaɗaɗe. Za ki saka kayan ƙamshi; kirfa, bay leaf, curry, thyme da gishiri.

    Ki zuba wannan ruwan naman ki bar shi ya tafasa sannan ki zuba shinkafar. Ki rufe ki kuma rage wuta har sai shinkafar ta dahu amma ba ta caɓe ko ta manne da jikinta ba.

    Mataki na 3:

    Bayan shinkafar ki ta dahu, ki jera naman kazar ki ko naman ki a saman shinkafar cikin tukunya. Ki kunna ƙaramin coal ki saka a cikin ƙaramin cokali ko dai wani abu da ba zai ƙone ba ki sa a tsakiyar shinkafar, ki zuba man zaitun a kan coal ɗin ki rufe na minti 5-10.

    Wannan shi ne sirrin ɗanɗanon mandi rice mai ƙamshi.

    Karanta Yadda Ake Faten Tsakin Masara

    Edita@rumasau-kallamu

  • Yadda Ake Faten Tsakin Masara

    Yadda Ake Faten Tsakin Masara

    Assalamu alaikum! Barkanmu da wannan lokacin. Mun jima ba mu leƙa kichen ba. Yau dai na ce bara mu leƙa gargajiya. Dana laluba sai na ga bara mu taɓo FATEN TSAKIN MASARA.

    Abubuwan da ake baƙata idan za a yi faten tsakin masara su ne:

    • Tsakin Masara
    • Manja /Farin mai
    • Yakuwa
    • Attarugu
    • Albasa
    • Seasoning
    • Nama ko kifi
    • Kayan ƙamshi

    Yadda Ake Haɗawa:

    Da farko ki za ki wanke tsakin masara. Ki samu tukunya ki ɗora manja ko farin mai ki soya albasarki da attarugu da ɗan kayan ƙamshi yadda kike so ki ƙara ruwa bayan albasar ta dahu kaɗan sai ki zuba ruwa da ɗan dama.

    Bayan ruwan ya tafasa sosai ki zuba tsakin a hankali kina gaurayawa don kada ya yi guda (lumpy). Ki zuba kayan ɗanɗanon ki kamarsu curry,thyme in kina so amma. Ki zuba namanki ko kifi a ciki su ci gaba da dahuwa tare.

    Sai ki yanka yakuwa ki zuba a ciki. Ki bar shi ya dahu har ya yi laushi kina motsawa don kar ya ƙone lokaci zuwa lokaci, idan ya yi miki kauri sosai ki ƙara ruwa kaɗan.

    Idan ya dahu ya yi laushi kuma ya dahu sosai ,sai ki sauke. Za ki iya ƙara manja a saman don ƙamshi.

    Na barku lafiya. A gwada uwargida da amarya. Sace zuciyar mai gida ba na mai bacci ba ne.

    Don karanta Faten Doya Da Ƙwai

    Edita@rumasau-kallamu

  • Musa Ɗanƙwairo A Gayaunar Waƙa

    Musa Ɗanƙwairo A Gayaunar Waƙa

    Makaɗa Abdu Kurna yana daga cikin makaɗa na ƙungiya; waɗanda suka yarje wa wasu mataimakansu su dinga zuwa taɓe na yin waƙa; wato gayaunar kiɗa.

    A lokacin da Sarkin Kiɗa Abdu Kurna ya lura wazirinsa Musa Ɗanƙwairo ya laƙanci waƙar baka; sai ya ba shi faraga ya dinga fita da abokansa yawon rera waƙoƙi lokaci bayan lokaci wato sa’i da wata bukata.

    Makaɗa Musa Ɗanƙwairo ya yi waƙoƙin noma da yawa lokacin gayauna. Daga nan ne Abdu Kurna ya ba shi izini ya dinga haɗawa da waƙoƙin masu Sarauta, musamman ma ‘ya’yan Sarakuna.

    Waƙar Gayauna ta Sarauta wadda Musa Ɗanƙwairo ya fara shiryawa da aiwatarwa da rerawa da sadarwa; ita ce wadda ya yi wa Abubakar ɗan Sarkin Noma Usman na Birnin Ƙaya.

    Ga wasu ɗiya na waƙar:

    G/Waƙa: Ɗan Sarki a gode maka,
    : Jikan Dodo Ɗangwamma.
    Jagora: Ya tafi daji ba shi komawa,
    : Kullum daƙe duƙe sai duƙe,
    ‘Y/Amshi: Gyado mai ƙoƙarin gabce,
    : Ɗan Sarki a gode maka,
    : Jikan Dodo Ɗangwamma.
    Jagora: Mijin Ɗiya jikan Nomau,
    : Gwarzon Ango karsanin Ali,
    : Gungaman Iro ɗan Jatau,
    : Kullum daga duqe sai duqe,
    ‘Y/Amshi: Gyado mai ƙoƙarin gabce,
    : Ɗan Sarki a gode maka,
    : Jikan Dodo Ɗangwamma.
    (Waƙar Musa Ɗanƙwairo 30 ta Abubakar Birnin Ƙaya)

    Domin karanta cikakken bayani akan Sauya Akalar Kiɗan Gado Zuwa Na Fada Da Na Game-Gari danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Gudumawar Waƙoƙin Baka na Situdiyo Wajen Haɓaka Tattalin Arziki danna nan.

    Wannan bayanin an ciro shine daga Littafin; Tarihin Rayuwa Da Halifofin Makaɗa Alhaji Musa Ɗanƙwairo Maradun A Aiwatarwa Da Sadar Da Waƙoƙin Baka Na Hausa; wanda Prof. Sa’idu Muhammad Gusau ya wallafa shi; domin karanta cikakken Littafin danna nan.

  • Tarihin Alaramma Malam Aliyu Ɗan Kadawa (1868-1998)

    Tarihin Alaramma Malam Aliyu Ɗan Kadawa (1868-1998)

    An haifi Malam Aliyu a zamanin Sarki Abdullahi a garin Kadawa cikin ƙaramar Hukumar Warawa da ke Jihar Kano. Hamshaƙin malamin Alƙur’ani, ma’abocin zaumunci da kyauta.

    Malam Aliyu ya yi tafiye-tafiye na neman Alƙur’ani har sai da ya dangana da ƙasar Maiduguri, baya ga lokacin da ya ɗauka yana gwagwarmayar neman karatu tsakanin Gaidam da Gayan da ke garin Haɗeja.

    An ce a lokacin da Turawa suka fara zuwa Kano, Malam Aliyu na rubuta AIƙur’aninsa na biyu. A lokacin kuwa da Gwani Hamad ya bayyana a birnin Kano. Malam Aliyu Ɗankadawa na daga cikin Gwanayen AIƙur’ani da suka sanya allo a gabansa don ɗosana daga hasken da Ubangiji Ya ba shi na ilmin tajwidi da ƙira’o’i.

    Saboda irin shaharar da Malam Aliyu ya yi wajen sada zumunci kuwa, ya kasance duk da girma ya kama shi; ya kan yi shiri wani lokaci ya yi tafiya mai nisa da ƙafa cikin wasu garuruwa don kai ziyara ga tsofaffin alarammomi abokan karatu tun lokacin ƙuruciya.

    Game da karamcinsa kuwa, ya lazimta wa ‘ya’yansa zuwa gidajen aminansa da ke kusa; domin gaishe su a kowace safiya da yi musu wasu ayyuka kafin ma su gaishe shi ya amsa. Alaramma Malam Aliyu ba ya shigar da wani abu na sadaka gidansa har sai ya rabar da shi ga almajransa. Almajiri ba ya samun fada a warin malam sai in kaɗai ya rungumi Alƙur’ani ka’ in da na’in.

    Game da baiwar Alƙur’ani da rubuta shi kuwa; Alaramma Malam Aliyu Ɗankadawa ya kasance hatta a lokacin tafiya ba ka rasa shi da kayan rubutun AIƙur’ani. Da ya samu wata dama ko yaya ta ke to, sai ya cigaba da rubuta Alƙur’ani abinsa. Da haka ya ribaci rayuwarsa ta hanyar amfanı da lokaci komai ƙan-ƙantarsa.

    Kaɗan daga cikin almajiransa sun haɗa da:-

    • Malam Yalwa
    • Malam Musa Gurgu Takai
    • Malam Abubakar
    • Malam Garba Kurna
    • Malam Rabi’u Gezawa
    • Malam Isa Ringim

    Ubangiji Maɗaukaki Ya yi wa Malam Aliyu Ɗankadawa tsawon rai don ya rasu a shekarar 1998 yana ɗan shekaru 130; ya bar ‘ya’yaye waɗan da suka haɗa da:-

    • Malam Ya’u
    • Malam Ɗayyabu
    • Malam Tasi’u da
    • Malam Haruna

    Domin karanta cikakken bayani a kan Tarihin Sheikh Malam Mahammad Ɗan Almajiri danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Taƙaitaccen Tarihin Waƙafi A Musulunci danna nan.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Tsarin Tsangayun Alƙur’ani A Arewacin Najeriya; Tarihin Su Da Zamantakewar Su Da Hanyoyin Raya Su wanda Dr. Sunusi Iguda Ƙ/Nasarawa ya wallafa shi; domin karanta cikakken Littafin danna nan.

  • Tattali da Kulawar Ɗanƙwairo da Majiɓintansa

    Tattali da Kulawar Ɗanƙwairo da Majiɓintansa

    Kamar yadda tarihin rayuwar Makaɗa Musa Ɗanƙwairo ya tabbatar; shi mutum ne mai kula da ciyarwa da shayarwa da tufasarwa da samar da muhallai na zaman iyalinsa da makusantansu; da sauran waɗanda suke majiɓinta a gare shi.

    Sannan yakan yi wa iyalinsa tarbiyya gwargwadon yadda addinin Musulunci da al’adu kyawawa na Hausawa suka tanada.

    Mutum ne kuma wanda yake fafutukar haɗa kan dukkan zuriyyarsa da yi musu addu’a su zauna salim alim; ba ƙyama ko faɗa ba wata hauragiya ko ƙiyayyar juna. Haƙiƙa, wannan wata hanya ce ta wanzar da zuriyya bisa haƙuri don ta zama tsintsiya maɗaurinki ɗaya.

    Musa Ɗanƙwairo kamar yadda ya tashi, ya gani a gidansu, ya himmatu ta fuskar yin noma da duka ayyuka na gona; don samar da abinci da abubuwan masarufi waɗanda suka zamanto abokan zama.

    Sau da yawa; Makaɗa Musa Ɗanƙwairo ba ya buƙatar duk wani abu da zai hana shi yin noma a kowace faɗuwar damina. Ta haka Alhaji Musa Ɗanƙwairo Maradun ya nuna ba ya son jama’arsa ta tagayyara. Saurari wata damuwa ta makaɗa Musa

    Ɗanƙwairo a sa’ilin da Damina Bakolori ya tauye shi a yin noma a wata damina:

    Jagora(Daudu): Allah shi ka kawo komi,
    : Yaƙin Dam Bakolori ya ci mu,
    ‘Y/Amshi: Sai in faɗa ma Mamman,

    : Ban da gida yanzu ban da gona, Jagora(Daudu): Yanzu cikin damina ni kai ta shirin,
    ‘Y/Amshi: Gyaran wurin da za ni bacci, Jagora(Daudu): Yanzu gidan Makaɗa ya zamo gurbi na ƙwarai,

    : Wanda ad da zurhi,
    ‘Y/Amshi: Sarkawa su sukai da taru,

    Jagora(Daudu): Sarkin Daura ko da damina,
    : Sai kai ta shirin tariyab baƙi,
    ‘Y/Amshi: In wasu sun kore mu mu taso,

    : Muhammadu in wasu sun kore mu mu taso,
    Jagora(Daudu): Ba ni zama inda babu gona,
    ‘Y/Amshi: Ba ni zama inda ba abinci,

    : Babban jigo na Yari,
    : Uban Shamaki tura haushi.
    (Ɗanƙwairo, Waƙar Babban Jigo, ta Sarkin Daura, Alhaji Muhammad Bashar (1966-2007)

    Bayan harkokin noma, makaɗa Musa Ɗanƙwairo kuma ya yi kiwon shanu da tumaki; da awaki da Kaji da sauran dabbobi da tsuntsaye. Ya ƙaura ya bar wa iyalinsa yin waɗannan sana’o’i.

    Domin karanta cikakken bayani akan Rasuwar Makaɗa, Sarkin Kiɗan Maradun Alhaji Musa (Ɗanƙwairo) Usman Ɗankwanagga a 1991 danna nan.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Tarihin Rayuwa Da Halifofin Makaɗa Alhaji Musa Ɗanƙwairo Maradun; A Aiwatar Da Sadar Da Waƙoƙin Baka Na Hausa; wanda Prof. Sa’idu Muhammad Gusau ya wallafa shi; domin karanta cikakken Littafin danna nan.

  • Tarihin Shehun Malami Muhammad Rabi’u Ɗan Tinki (1897-1959)

    Tarihin Shehun Malami Muhammad Rabi’u Ɗan Tinki (1897-1959)

    Malam Rabi’u ɗan Yunusa ɗan Alhasan ɗan Baru. An haife shi a garin Tinki a cikin ƙaramar hukumar Bici da ke Jihar Kano cikin shekarar 1897.

    Malam Rabi’u ya taso ciki ƙuruciya manisanciyar wargi da wasanni irin na matasa. Ya yi karatu a gaban mahaifinsa. Muhammad Rabi’u Ɗan Tinki ya kasance mutum ne mai yawan haƙuri da kawaici da yawan sabo da jama’a. Ya haddace Alkur’ani tun yana ɗan shekara goma sha huɗu. Sannan ya fara karatun littatafai irin su Ahalari da lziyya.

    Daga nan ya nemi izinin muhaifinsa ya bi wani baƙon mashahurin malami da ake kira Malam Kunta. Bayan ya zauna tsawon lokaci a wurinsa, sai ya nemi izini zuwa wajen Mahiru Kalla mutumin Damagaram cikin Jamhuriyar Nijar.

    Ya zauna a wajensa tsahon lokaci har ya sauke litlatafai da yawa a fannin ilimin ƙira’a da Tawhid da litlafai irinsu Nuniyar Sakawiy da Hidayatussibiyan da Tuhfatul adfal da Mukaddimat Jazary, da Shadibiyya da Lamiyyatul Kira ‘at.

    Shaihun malamin bai gushe ba yana kutsawa cikin fagagen ilmai da gogayya da malamai har sai da ya dangana da garin Maiduguri ya yi karatu a wurin Mahiru Ahmad. Daga nan ya dawo Kano ya sauka Haɗejiya ya kara dukuta a gaban Malam Is’hak daga bisani ya dawo Kano ya cigaba da koyarwa.

    A lokacin da Malam Ɗantinki ya samu labarin Mahiru Hamid, sai ya nemi izinin ya zama almajirinsa. A nan ma ya karanta littafai da dama musamman fannin dabti wanda shi ma ɓangare ne na ilimin Rasmu da ilimin wasullan Alkur’ani.

    Abokan karatun Shehi Rabi’u wurin Gwani Hamid sun haɗa da Malam Ɗan Gunduwawa da Malam Aliyu Mai Kwaro da Malam Ɗan Karofin Yashi da Malam Yunus Ɗan Gumel da Malam Ɗan Kanuri da Malam Isah Ɗan Kwandarai da Malam Sabo Ƙofar Wambai da Malam Umar Ɗan Mai-Rigar-Fatu.

    A halin yanzu tsangayarsa ta cigaba da bunƙasa kuma ta yi rassa a hannun ɗan sa Halifa Sheikh Is’haka Rabi’u.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Tarihin Gwani Saleh Danzargu danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Taƙaitaccen Tarihin Samuwar Waƙoƙin Baka a Ƙasar Hausa danna nan.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Tsarin Tsangayun Alƙur’ani A Arewacin Najeriya; Tarihin Su Da Zamantakewar Su Da Hanyoyin Raya Su wanda Dr. Sunusi Iguda Ƙ/Nasarawa ya wallafa shi; domin karanta cikakken Littafin danna nan.

  • Yadda Falalar Karatun Al-Ƙur’ani Ya Ke

    Yadda Falalar Karatun Al-Ƙur’ani Ya Ke

    Karatun ƙur’ani ibada ce babba wacce babu sama da ita; musamman in ta haɗu da ikhlasi da lura da ma’anoni da manufofin abinda ake karantawa (Tadabbur) da karantawa dai-dai da ƙa’idodin karatun (Tajwidi); da kuma abinda ya fi komai muhimmanci wato aiki da abinda ake karantawa.

    Hadisai da dama sun zo kan bayanin Falalar Karatun Al-Ƙur’ani a jumlace; da kuma falalar karanta waɗansu keɓaɓɓun surori da ayoyi.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Yadda Falalar Koyo Da Koyarwar Da Al-Ƙur’ani Ya Ke danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Falalar Zikiri danna nan.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga littafin Ingantattun Nafiloli Da Falalarsu; wanda Usman Abubakar Muhammad (Shehu Mansur Dala) ya wallafa shi; Domin karanta cikakken littafin danna nan.

    Edita@rumasau-kallamu

  • Falalar Sadaƙar Mai Ƙaramin Ƙarfi

    Falalar Sadaƙar Mai Ƙaramin Ƙarfi

    An karɓo daga Abu Huraira (Radiyallahu anhu) ya ce: “Haƙiƙa Manzon Allah (Sallallahu alaihi wasalam) yace: “Sadaƙar dirhami ɗaya ta rigayi sadaƙar dirhami dubu ɗari” Sai wani mutum ya ce; Kamar yaya Manzon Allah (Sallallahu alaihi wasalam)?

    Sai ya ce: “Mutum ne yana da dukiya mai yawan gaske, sai ya tsakuro dubu ɗari ya bayar sadaƙa; kuma wani dirhami biyu ne kaɗai da shi. Sannan ya yi sadaƙa da dirhami ɗaya” (Nasa’I Ibn Khuzaimah), (Sahihul Targib 875).

    Domin karanta cikakken bayani a kan Falalar Ciyarwa Da Shayarwa Da Tufatarwa danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Ratiban Nafiloli danna nan.

    Wannan bayani an ciro shi ne daga littafin Ingantattun Nafiloli Da Falalarsu; wanda Usman Abubakar Muhammad (Shehu Mansur Dala) ya wallafa shi; Domin karanta cikakken littafin danna nan.

    Edita@rumasau-kallamu

  • Tarihin Gwani Saleh Ɗanzargu

    Tarihin Gwani Saleh Ɗanzargu

    An haifi Gwani Saleh ɗan Abdullahi jikan Abdullahi a Ƙasar Jahun. Mahaifin sa ya rasu yana ƙaramin yaro, don haka sai mahaifiyar sa ta koma da shi garin Zarga ta kuma kyautata tarbiyar sa.

    Gwani Saleh ya taso da kaifin basira da son Alƙur’ani. Don haka ya lazimci makarantan garin Zarga irinsu Malam Abdullahi har Ubangiji Ya hore masa Alƙur’ani ya haddace shi yana ɗan shekara tara (9). Gwanin Alƙur’ani ma’abocin ƙan-ƙan da kai da gaskiya da riƙon amana. An ce tun yana ɗan shekara sha biyu ya sha fari.

    Gwani Saleh ya yi tafiye-tafiye na neman karatu a inda yazo Kano ya sauka a tsangayar Gwani Nadudu. Daga bisani kuma ya lazimci mashahurin malami Malam Aliyu Basakkwace ya karanci Fiƙhu da Hadisi da tafsiri Shaharar da tsangayarsa ta yi ya sanya makaranta daga nisan duniya yin takakkiya don ɗosana daga haskenta. Manyan abokanen karatun Gwani Saleh sun haɗa da:-

    • Gwani ɗan Kwandarai
    • Gwani Ɗan birni
    • Gwani Daudu

    Game da yawan almajiran da suka samu Alƙur’ani a hannun sa kuwa, wannan ɗan littafi ba zai ɗauke ambaton su ba, sai dai mu yi ishara ga waɗansun su:

    • Malam Muktari Abdullahi
    • Yayan sa Gwani Yahuza da Gwani Lawi
    • Malam Husaini Rijiyar Lemo
    • Malam Sham’unu
    • Malam Ibrahim Maidarasu

    Gwani ya rayu cikin karamci da girmamawa daga maƙwabtan sa, musamman ma Alhaji Sunusi Ɗantata da al’umar Unguwar ƙoƙi da kewayenta. A halin yanzu wannan tsangaya tana ƙarƙashin kulawar ɗan sa Gwani Yahuza inda ta ƙara bunƙasa ta hanyar shigo da tsarin ilmin zamani, ɓangaren firamare da sakandare. A lokaci guda kuma, ga tsohon tsarin tsangaya na gudana da makaranta da mahaddata.

    Gwani Yahuza ya samu gogayya da wayewa ta zamani a inda ya dangana da ƙasar Masar don karatun sa na digirin farko. A halin yanzu Gwani Yahuza ɗaya ne daga manyan alƙalai na musabaƙar Alƙur’ani ta ƙasa. Gwani Yahuza shi ne ɗan Najeriya na farko da ya karɓi kyautar girmama mahaddata Alƙur’ani daga ƙasar Saudi Arebiya. Baya ga wannan rassa na makarantar akwai majalisai a unguwannin Gwammaja da Kurnar Asabe da Ƙoƙi.

    Ita wannan makaranta ta Gwammaja, Gwani Lawi ne ya kafa ta mai suna Ma’ahad Gwani Lawi Litahfizil Ƙur’anil Karim.

    Gwani Lawi ya yi babbar Diflomarsa a Jami’atul Ƙur’anil Karim da ke Sudan, kuma shi ne wan da ya kafa ƙungiyar Mahaddata Alƙur’ani ta farko a Najeriya, mai suna Rabiɗatul Huffazil Ƙur’ani, Nigeriya. Gwani Sale Ɗanzarga ya bar ‘ya’ya goma sha biyu, maza da mata.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Tarihin Malam Ɗankwandarai danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Tarihin Farko Na Nijeriya (1500 BC- 500 AD) danna nan.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Tsarin Tsangayun Alƙur’ani A Arewacin Najeriya; Tarihin Su Da Zamantakewar Su Da Hanyoyin Raya Su wanda Dr. Sunusi Iguda Ƙ/Nasarawa ya wallafa shi; domin karanta cikakken Littafin danna nan.