Tag: turare

  • Yadda Ake Turaren Sikari

    Yadda Ake Turaren Sikari

    Kayan Haɗawa

    Ruwan turare (alcohol)

    Yara-yara gwangwani 1

    Sikari kwano

    Kala

    Filabo

    Madarorin Turare 5

    Yadda Ake Haɗawa

    A juye Sikari a cikin mazubi. A juye Yara-yara, a sa madarorin turare 5. Sai a sa kala, a yi ta juyawa har sai ko’ina ya haɗe jikinsa sosai.

    Shi ma wannan turare a cikin garwashi ake sawa a turara ɗaki da shi.

    A ƙarshe dai amfani da turare ya kewaye dukkan ƙasashe. Haka kuma da sauran jihohi. Ya Kuma cancanci a ce yana ciki kasafin wata-wata na kowanne mai gida. Gidanka ƙamshi Kuma jikin matarka ƙamshi. Haka zai sa wa ma’aurata natsuwa da samu gamsuwa da juna. Duba yadda ake haɗaɗɗiyar humra.

    Littattafai da aka duba:

    Taron ƙara wa juna ilmi.

    Hikimomin Kulawa da Mai gida.

    Mu Koyi Sana’a.

    7th Nuwanba, 2015,
    Gidan Mumbayya, kano.

    Domin karanta cikakken bayani akan Yadda Ake Turaren Ɗaki Na Musamman danna nan

    Domin karanta cikakken bayani akan Yadda Ake Turaren Wuta Na Musamman danna nan

  • Yadda Ake Turaren Hammata

    Yadda Ake Turaren Hammata

    A yau zau koyi yadda ake turaren hammata, Turaren hammata turare ne da yake da matuƙar amfani a wajen mutane, kula da hammata wajibi ne a kan ko wane mutum, domin yana daga cikin tsabtoci na sahun farko da ya kamata a kula da su. Saboda samun nutsuwar kai da kuma abokan hulɗa

    Abubuwan da ake buƙata

    Alimun
    Misik
    Mahalab

    Yadda ake haɗawa

    1. Za ki sa Alimun shi kaɗai a tukunya, ki ɗora a wuta har ya narke.
    2. Sannan ya sake bushewa, sai a ɓanɓare shi, a daka shi a tankaɗe shi da rariya mai laushi.
    3. Sai a cakuɗa da dakakken misik da mahalab ( waɗanda aka tankaɗe su).

    Domin sanin yadda ake sabulun salo na amare danna koren rubutun nan

  • Yadda Ake Turaren Wuta Na Musamman

    Yadda Ake Turaren Wuta Na Musamman

    Turaren wuta ana yin sa ne da itace, domin turara ɗaki, da dukkanin jiki da na tsugunno, da kuma na sutura . Ana zuba shi cikin gaushi (garwashi) ne a kasko. Nan da nan kuwa ka ji ƙamshi ya gauraye ko’ina a cikin gida. Daga cikin Itatuwa da ake turare da su kuwa Sun haɗa da:
    Icen Sandal
    Ice, Hawi
    Icen Gab-Gab
    Icen Durot
    Da dai Sauransu.

    Ana yin turare na soyawa kuma ana yin na jiƙawa. Ya danganta da buƙatar mutum.

    Larabawa da kuma mutanen Maiduguri ne suka fi shahara wajen amfani da turaren wuta. Mazansu na taimakawa sosai, su siya wa matansu turare akai-akai. A wajensu tamkar dole ne amfani da turare . Mace ba ta da daraja sai da kasancewa cikin ƙamshi a kodayaushe .

    KAYAN TURAREN WUTA
    Icen Hawi
    Matan Arewa
    Farce
    Misik
    Alhaji Abdullahi
    Salamalekum
    Sasorabia
    20 fragrances
    Madara turare ( 8)

    YADDA AKE HAƊAWA
    Za a sa icen Hawi a turmi a daddaka shi sama-sama. A sa icen gab-gab shima haka. Sai a juye su cikin mazubi. A dauko ruwan turare Matan Arewa a zuba a kan itatuwa. A juye Soyayyen farce. A zuba Misik. Sai a ɗauko turaruka: Alhaji Abdullahi, da salamalekum, da Sasorabia, da 20 fragrances. Kowanne a buɗe a juye. Sai kuma a dauko madarar turare masu matukar ƙamshi a zuba su. A juya da kyau ko’ina ya samu ya haɗe . A samu mazubi a juye a ciki. Kuma a rufe shi sosai.

    Littattafai da aka duba:

    Taron karawa juna ilmi.

    Hikimomin Kulawa da Mai gida.

    Mu Koyi Sana’a.

    7th Nuwanba, 2015,
    Gidan Mumbayya, kano.