Tag: Mabiya

  • Hadisi Na Bakwai Akan Falalar Adalci Da Tausayawa Mabiya Da Illolin Gallaza Musu

    Hadisi Na Bakwai Akan Falalar Adalci Da Tausayawa Mabiya Da Illolin Gallaza Musu

    An karɓo daga Abdullahi ɗan Amr ɗan Asi (Radiyallahu Ahuma) ya ce: Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce: “Haƙiƙa masu adalci za su kasance a kan mimbarai na haske a daman Allah mai rahama, kuma duk hannayensa biyu dama ne. Su ne waɗanda suke yin adalci a cikin hukuncinsu da iyalansu da waɗanda suke jagoranta.

    Muslim da Nasa’i ne suka rawaito shi.

    ƘARIN BAYANI

    Haƙiƙa masu yin adalci da gaskiya a shugabancin da yake kansu da iyalansu suke kaucewa zalunci da nuna bambancin a tsakanin waɗanda suke jagoranta, za su samu babban matsayi a wurin Allah ranar lahira.

    Hannun dama da ya zo a wannan hadisin sifa ce daga sifofin Allah Ta’ala waɗanda ake yin imani da su kamar yadda suka zo, ba tare da an yi musu tawali ko canja su ko kore su ba ko kuma kamanta su da sifofin halittu ba.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Hadisi Na Takwas Kan Falalar Adalci Da Tausayawa Mabiya Da Illolin Gallaza Musu danna nan.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Shugabanci A Musulunci (Hadisai Tamanin Da Biyu A kan Shugabanci) wanda Shehu Mansur Dala ya wallafa shi domin karanta cikakken Littafin danna nan.

  • Hadisi Na Biyar A Kan Falalar Adalci Da Tausayawa Mabiya Da Illolin Gallaza Musa

    Hadisi Na Biyar A Kan Falalar Adalci Da Tausayawa Mabiya Da Illolin Gallaza Musa

    An karɓo daga Aliyyu (Radiyallahu Anhu) ya ce: “Maganar ƙarshe da Manzon (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya yi ita ce: “Ku kula da sallah, ku kula da sallah, ku ji tsoron Allah ku kula da haƙƙoƙin waɗanda suke a ƙarƙashinku”.

    Abu Dawud da Ibn Majah ne suka rawaito shi.

    ƘARIN BAYANI

    Wannan hadisi yana daga cikin wasiyyoyin da Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya bar wa al’ummarsa dab da wafatinsa. Ya yi wasiyyar a kula da sallah kuma a kula da haƙƙoƙin bayi da barori da duk waɗanda suke ƙarƙashin mutum.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Falalar Adalci Da Tausayawa Mabiya Da Illolin Gallaza Musu danna nan.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Shugabanci A Musulunci (Hadisai Tamanin Da Biyu A kan Shugabanci) wanda Shehu Mansur Dala ya wallafa shi domin karanta cikaken Littafin danna nan.

  • Hadisi Na Uku A Kan Falalar Adalci Da Tausayawa Mabiya Da Illolin Gallaza Musu

    Hadisi Na Uku A Kan Falalar Adalci Da Tausayawa Mabiya Da Illolin Gallaza Musu

    An karɓo daga Abu Hurairah (Radiyallahu Anhu) ya ce: Na ji mai gaskiya abin gasgatawa mai wannan ɗakin baban Alƙasim (Sallallahu Alaihi Wasallam) yana cewa: “Ba a cire tausayi sai daga zuciyar mara rabo a lahira”.

    Abu Dawud da Tirmizi ne suka rawaito shi.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Hadisi Na Huɗu A kan Falalar Adalci Da Tausayawa Mabiya Da Illolin Gallaza Musu danna nan.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Shugabanci A Musulunci (Hadisai Tamanin Da Biyu Akan Shugabanci) wanda Shehu Mansur Dala ya wallafa shi domin karanta cikakken Littafin danna nan.

  • Hadisi Na Tara Akan Falalar Adalci Da Tausayawa Mabiya Da Illolin Gallaza Musu

    Hadisi Na Tara Akan Falalar Adalci Da Tausayawa Mabiya Da Illolin Gallaza Musu

    An karɓo daga Abu Huraira (Radiyallahu Anhu) ya ce; Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce: Allah Ta’ala yana ƙin mutane huɗu; Ɗan kasuwa mai yawan rantsuwa, da talaka mai girman kai, da tsoho mazinaci da kuma azzalumin shugaba.

    Nasa’i da Ibn Hibban ne suka rawaito shi, Muslim ma ya rawaito makamancinsa sai dai a ruwayarsa ya ce; “Da talaka mai girman kai da shugaba maƙaryaci”.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Hadisi Na Goma A Kan Falalar Adalci Da Tausayawa Mabiya Da Illolin Gallaza Musu danna nan.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Shugabanci A Musulunci (Hadisai Tamanin Da Biyu A Kan Shugabanci); wanda Shehu Mansur Dala ya wallafa shi; Domin karanta cikakken Littafin danna nan.

  • Hadisi Na Goma Sha Biyu A Kan Falalar Adalci Da Tausaya Wa Mabiya Da Illolin Gallaza Musu

    Hadisi Na Goma Sha Biyu A Kan Falalar Adalci Da Tausaya Wa Mabiya Da Illolin Gallaza Musu

    An karɓo daga Ibn Abi Aufa (Radiyallahu Anhu) ya ce: Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce: “Haƙiƙa Allah yana tare da alƙali matuƙar bai yi zalunci ba. Idan kuwa ya yi zalunci, sai Allah ya rabu da shi, sai shaiɗan ya naniƙe masa.
    Tirmizi da Ibn Majah da Ibn Hibban da Hakim ne suka rawaito shi. Sai dai a ruwayar Hakim ya ce: “Idan ya yi zalunci sai Allah ya yi watsi da shi”.

    ƘARIN BAYANI
    Allah Ta’ala yana taimaka wa shugabanni da alƙalai masu adalci, yana kuma ba su kariya, yana rufa musu asiri, ya ɗaukaka su. matuƙar sun kama hanyar zalunci da rashin gaskiya, sai Allah ya yi watsi da su, ya bar su da dabararsu, su yi ta ɗimuwa da shirme, ga rashin ƙima a idon mutane, sannan in suka tafi a haka, a lahira su haɗu da matsananciyar azaba.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Hadisi Na Goma Sha Uku Kan Falalar Adalci Da Tausaya wa Mabiya Da Illolin Gallaza Musu danna nan.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Shugabanci A Musulunci (Hadisai Tamanin Da Biyu A kan Shugabanci) wanda Shehu Mansur Dala ya wallafa shi domin karanta cikaken Littafin danna nan.