Tag: fiyano

  • Ma’anar Fiyano

    Ma’anar Fiyano

    Masana sun tofa albarkacin bakinsu wajen bayyana ma’anar fiyano (Piano). Misali: Gusau (2008:347) ya ayyana Fiyano wata alama ce ta yin kiɗa wadda Hausawa suka samu daga Turawa.

    Sun sami wannan ala bayan yaƙin basasar Nijeriya wajejen shekarun 1970 lokacin da wasu ƙabilun Kudancin Nijeriya; suka fantsamo cikin Arewa. Fiyano (Piano) aba ce wadda ake kaɗawa ta bayar da amo nau’i-nau’i, mai diri ko mai zaƙi ko mai kauri gwargwadon yadda ake buƙata. Turawa sukan gwama masa jita da tasoshi da ganguna a lokacin kaɗa shi.

    Fiyano abin kiɗa ne na Turawa wanda suke haɗa shi da jita da wasu tasoshi da nau’o’in amo na jita; da ganguna da kayan bushe-bushe da buge-buge da sauransu”.

    Zainab (2009:83):

    Ta bayyana fiyano da cewa, “Fiyano abin kiɗa ne da ake amfani da madannai fari da baƙi (keyboard) wadda ke girke a kan tebur don samar da sautin kiɗa.

    Fiyano wata na’ura ce wadda ake amfani da madannai (keyboard) fari da baƙi. Kowane yana aiki kuma da irin sautin kiɗan da yake bayarwa ko kiɗan da ake buƙata.

    Ita Fiyano tana amfani da wutar lantarki da kuma batir. Tana daga cikin sanannun kayan kiɗa na duniya”.

    Binta (2011:76):

    Ta bayyana cewa “Fiyano (Piano) wata na’ura ce mai amfani da wutar lantarki wadda take bayar da amo na kiɗa iri daban-daban.

    Mutum ɗaya yana iya amfani da fiyano ya yi waƙa kuma ƙungiyar makaɗa ma suna yin amfani da fiyano domin rera waƙoƙinsu. Haka nan Kiristoci suna yin kiɗan fiyano a coci”.

    Gusau (2016:27):

    Ya sake bayar da ma’anar fiyano (Piano) da cewa, “Na’ura ce wadda ake iya samar da amo iri-iri na yawancin kayan kiɗa. Ana iya adana amo daban-daban da fiyano ta daddanna wasu mabuɗan amo da aka shirya masa; Fiyano yana da mazauni wanda ake ɗora shi a kansa. Mutum ɗaya yake sarrafa kiɗa da fiyano”.

    Fiyano abin kiɗa ne mai girma wanda yake da madannai fari da baƙi a jere. Ana buga fiyano a zauna a gabanta, sannan a latsa madannan. Akwai kiɗa kala-kala a har dubu bakwai da ɗari biyar (7,500) a cikin fiyano.

    Lokacin da Hausawa suka sami wannan abin kiɗa, sai suka cusa masa amon kiɗa na gargajiya kamar molo da ganga, da kotso, da shantu, da tafi, da busa, da kaca-kaura, da duma da sauransu. Fiyano yana da amon kiɗan zamani da na gargajiya. Ana ɗaukar fiyano a yi kiɗa da ita nan take (live performance). Fiyano koyon shi ake yi, sai a hankali ake fahimtarsa. An ci gaba da amfani da fiyano ana aiwatar da waƙoƙin Hausa.

    Daga baya, an samu kiɗan komfuta wanda ita ma tana da nata kaɗe-kaɗen. Koda yake asalin kaɗe-kaɗen nata daga fiyano ne. Ma’ana daga fiyano ake turawa a cikin kwamfuta. Ana tattara kiɗan fiyano a mayar da shi a kwamfuta. Ana amfani da waya (midi cable) wajen haɗa fiyano da kwamfuta.

    Kwamfuta tana da abin da ake kira (softwares) kamar Sonar. Daga cikinsa ne ake ƙirƙirar duk wani kiɗa. Akwai abin tace murya (cool edit) da (sound edit) a cikinsa.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Kiɗan Fiyano A Wajen Hausawa wanda Ibrahim Baba (Nayaya) ya wallafa shi.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Ire-iren Kiɗan Fiyano danna nan

  • Ire-iren Kiɗan Fiyano

    Ire-iren Kiɗan Fiyano

    Kiɗan fiyano ba kala guda ba ne; ma’ana ba sauti ɗaya ake samu na amo daga fiyano ba, akwai sautuka kala-kala; muhimmai daga ciki kuma sanannu guda uku ne.

    Ire-Iren Kiɗan Fiyano su ne:

    • Raps ko Rapping

    Rapping na ɗaya daga cikin ire-iren Kiɗan fiyano. Rapping-Wikipedia da The Free Encyclopedia sun nuna Raps na nufin “karatu da sauri ko magana da sauri”. Raps wani salo ne na waƙa wanda ake jin tashin sautin murya da sauri-sauri mai kama da magana.

    • Reggae Reggae

    An samo asalin wannan kiɗa ne daga ƙasar Jamaica tun a shekarar 1960, wanda mutanen Jamaica ke amfani da shi wajen kaɗe-kaɗe da raye-rayensu, kuma yana daga cikin tsofaffin nau’o’in kiɗa kamar Ska da Rocksteady. Kiɗan Reggae ya fi sauri a kan Rocksteady amma kuma ya fi kiɗan Ska tsauri.

    Ƙamusun Reggae- Wikipedia da The Free Encyclopedia, sun bayyana cewa, asalin kalmar ta fara bayyana a cikin ƙamusun Ingilishi ta Jamaica a shekarar 1967. Waƙar Reggae salonta yana fitar da damuwa a zuciya. Duk waƙar da aka yi da wannan salo, tana da abin da ake kira code, wani nau’in kiɗa daban.

    • Hip Hop

    Wani salon kiɗa ne wanda ake yin rap a cikinsa. Salon waƙar Rap da na Hip Hop suna da kamanci, suna maye gurbin juna a wasu lokuta.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Kiɗan Fiyano A Wajen Hausawa wanda Ibrahim Baba (Nayaya) ya wallafa shi.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Samuwar Fiyano A Ƙasar Hausa danna nan

  • Asalin Kiɗan Fiyano

    Asalin Kiɗan Fiyano

    Encyclopedia Americana (2003), ta bayyana cewa, a shekarar 1709;

    Fiyano – Bartolommeo Cristofori ya ƙirƙiri wani abin kiɗa da ake kira gravicembalo col piona e forte. Wanda yake samar da sautin piano (soft) da forte (loud). Daga haka aka samu sunan pianoforte ko fortepiano. Daga haka aka gajerce sunan zuwa piano.

    Binta (2011:76) ta bayyana cewa “Ana jin mutumin da ya fara ƙirƙiro fiyano, shi ne Bartolemo Cristofori ɗan ƙasar Italiya. Mawaƙi kuma ƙwararre a kan sanin kayan kiɗa wanda kuma iyalan Medici suka riƙe shi.

    Amma zuwa ƙarshen 1700, kiɗa da fiyano ya zamo abin zaɓi ga masu haɗa kiɗa da kuma su kansu mawaƙan”.

    Zainab (2009:83) ta bayyana asalin fiyano daga ƙasar Italy aka ƙirƙire shi, tun a ƙarni na sha tara (19), kuma Pianoforte shi ne cikakken sunanta, kuma sunan asali. Pianoforte ita ce nau’in fiyano na farko da aka fara samu. Mawaƙi mai amfani da fiyano ana kiransa pianist. Akwai wasu abubuwa da suka haɗu, suka tayar da fiyanon kamar strings da keys da pedal da pianostool.

    Enclyclopedia Americana (2003) da Concise English Dictionary (2006), sun ƙara bayyana cewa, fiyanon na da nau’o’i biyu cikinsu akwai: Grand Piano da Upright Piano.

    Grand piano ita ce wadda take da madannai guda tamanin da takwas (88), hamsin da biyar (55) farare ne, su kuma baƙaƙe talatin da shidda (36) ne. Ana latsa madannan tsawon inci 3/8 (9.6 mm). Ita Upright piano tana da wasu ɓangarori na grand piano, sai dai akwai ‘yan bambance bambance a tsarinsu.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Wuraren da Ake Kiɗan Fiyano (Situdiyo)