Tag: Dankali

  • Yadda Ake Groundnut Sweet Potato Balls.

    Yadda Ake Groundnut Sweet Potato Balls.

    Barkan mu da sake kasancewa a cikin shirinmu na GIRKE-GIRKEN WikiHausa wanda muke koyarda ƙayatattun abinci namu na gida Najeriya da kuma na ƙetare, tare da bayani a kan lafiyarsu cikin harshen Hausa a sauƙaƙe tare da ni Hafsat Shettimah. A yau za mu koyar da yadda ake yin groundnut sweet potato balls (groundnut cake) ku biyo ni a sannu domin mu koya tare……

    Ko kun san groundnut sweet potato balls na da saurin narkewa a jikin ɗan Adam. Hakan yasa ya zama abinci mai kyau wurin yara da tsofaffi.

    Abubuwan Buƙata

    1. Soyayyar gyada ¼ cup
    2. Dankalin Hausa matsakaita
    3. Albasa a yanka Ƙanana ko a jajjaga
    4. Curry ½ tablespoon
    5. Markaɗaɗɗen nama
    6. Sinadarin ɗanɗano
    7. Attaruhu guda biyar jajjagge
    8. Tafarnuwa
    9. Breadcrumbs 1 cup
    10. Kwai 3 (a fasa a kaɗa shi)
    11. Man gyaɗa na suya

    Yadda ake haɗawa

    1. A cikin kwano mai kyau a zuba dafaffen dankali, sai a farfasa su, su fasu da kyau.
    2. Sannan a zuba albasa, attaruhu, tafarnuwa, sinadarin ɗanɗano, curry, thyme da nama a juya a hankali
    3. A samu dan faranti a ringa ɗiban dankalin ana cura kamar ball ana ajiye
    4. A tsoma wannan ball cikin ƙwai sai a saka shi cikin bread crumbs a juya sai a saka cikin mai me zafi idan ya soyu a kwashe. Bon apetite

    Domin koyon  Yadda Ake Groundnut Sweet potato Pie  danna nan.

  • Yadda Ake Faten Dankali

    Yadda Ake Faten Dankali

    A yau za mu koyi yadda ake faten dankali; Faten dankali abinci ne mai daɗi da sauƙin sarrafawa.

    Abubuwan da ake buƙata:

    Dankali
    Attaruhu
    Albasa
    Maggi
    Citta
    Kifi (ice fish)
    Alayyahu
    Kori
    Man gyaɗa

    Yadda ake haɗawa

    1. A fere dankali, a yanka daidai misali.
    2. Sai a wanke kifi, a cire dattin, a yanka gunduwa-gunduwa; a zuba albasa da maggi da citta a kai, sannan a ɗora a wuta.
    3. Bayan haka, sai a jajjaga attaruhu da albasa da citta a ajiye.
    4. Idan ya tafasa a sauke a bar shi ya ɗan huce, in ya huce, sai a ɓare shi a ajiye.
    5. A nan sai a ɗauko tukunya, a zuba man a yanka albasa a ciki, a bar shi ya soyu kaɗan.
    6. A sa jajjagaggen attaruhu da aka jajjaga, sai a zuba ruwa daidai misali, a rufe ya yi mintina ya tafasa.
    7. Idan ya yi, sai a zuba dankalin, a sa maggi da gishiri kaɗan da kori da citta, a rufe ya dahu.
    8. In ya yi sai a zuba kifi da alayyahu da albasa, a juya, sai ki rufe, a bar shi ya yi minti biyar.

    Domin sanin yadda ake kifi mai fulawa danna nan

  • Yadda Ake Ƙosan Dankali Mai Haɗe Da Nama

    Yadda Ake Ƙosan Dankali Mai Haɗe Da Nama

    KAYAN HAƊI

    • Dankali
    • Nama
    • Kwai
    • Attaruhu
    • Albasa
    • Maggi
    • Gishiri
    • Man gyaɗa
    • Fulawa ko garin busashen buredi

    *YADDA AKE HAƊAWA*

    Da farko ki wanke nama ki zuba a tukunya, sai ki zuba maggi da gishiri, ki tafasa sai ki kwashe ki zuba a turmi ki jajjaga tare da albasa da attaruhu, idan ya yi laushi, sai ki kwashe a kwano ko roba, sannan ki dawo ɗan dankalin Turawa ki tafasa ya yi laushi, sai ki murmushe shi ko kuma ki jajjaga a turmi, sai ki kwashe shi a cikin kwanon da kika kwashe naman da kika jajjaga, sai ki ɗauko ƙwai ɗanye ki fasa a kai, ki zuba fulawa ko garin busasshen buredi a ciki, ki sa gishiri da maggi ki juya sosai, ki ɗauki farantin suya ki zuba man gyaɗa ki ɗora a kan wuta ki dinga ɗiba kina zubawa a cikin man gyaɗa mai zafi idan ya soyu za ki ga ya yi brown sai ki kwashe ki yi wa Oga ya yi breakfast da shi.

    ƘOSAN DANKALI

    *KAYAN BUƘATA*

    • Dankalin Turawa
    • Nama
    • Fulawa
    • Kwai
    • Albasa
    • Attaruhu
    • Gishiri
    • Maggi
    • Man gyaɗa

    *YADDA AKE YI*

    Ki jajjaga albasa da attaruhu, ki kwashe a kwano ko roba, sai ki ɗauki dankali, ki tafasa ki zuba a turmi ki daka shi, amma kar ya yi laushi sai ki kwashe a cikin kwanon da kika zuba jajjagen attaruhu da albasa, ki tafasa nama shi ma ki daka a turmi, duk ki hada da sauran kayan haɗin ki juya, sai ki dinga mulmulawa kina tsomawa a ruwan ƙwai, ki juya shi a cikin fulawa ki jefa a cikin man gyaɗa mai zafi ki soya , akwai daɗi matuƙa.