Sunan Fati Nijar na yanka shi ne Fatima, Mahaifinta kuma Abdurrahman wanda ake yi wa sunan rana Labaran, mahaifiyarta kuma A’ishatu ‘yar Hassan Ɗan Tanko.
Fatima (Binta) ta sami sunan fati Nijar daga Sadi Sidi Sharifai a lokacin da take yi masa amshi na waƙoƙin finafinai.
Labaran bisa asali mutumin Madawa ne cikin Jihar Tawa, kuma ɗan kasuwa ne mai zagayen garuruwa da ƙauyuka a ranakun cin kasuwanni a Jamhuriyyar Nijar.
Haihuwar Fati Nijar
Haihuwar Fatima (Binta) ta auku ne a ranar Alhamis 26/10/1984 a birnin Maraɗi, Jamhuriyar Nijar.
Bishiyar Nasabar Binta Labaran (Fati Nijar):
Ibrahim Tanko
Hassan
Abdurrahman ==== A’ishatu
Saudatu Usman Fatima Ibrahim Isa Musa (Fati NIjar) (Binta)
Yanayin Karatun Fati Nijar
Fatima (Binta) ta yi karatun Alqur’ani, mai tsarki. Haka kuma Fatima ta kori jahilci ta fuskar ilimin boko.
Fara Waƙar Fati Nijar
Binta Labaran mutum ce mai sha’awar waƙoƙin gaɗa na ‘yan mata, musamman waƙoƙin dandali masu tafiya da wasannin al’ada. Fati (Binta) ta zama zabiya, mai zaƙin murya, wadda ake son a ji amon muryarta a tsakanin ƙawayenta.
A wata ziyara da Binta ta kawo wa ‘yar’uwarta wadda take aure a Nijeriya cikin 2003, ta sami damar haɗuwa da wasu daga cikin makaɗa da mawaƙan sitidiyo, tun ma ba Ali Baba Yakasai da Sadi Sidi Sharifai ba.
Daga nan ne ta shiga hidima ta yin waƙoƙin fina-finai har ta kai lokacin da take shirya waƙoƙi nata na kanta daga 2006, kuma tana yaɗa su ta albam -albam. Fati Nijar tana da kyakkyawar dangantaka da makaɗan sitidiyo na lokacinta a Nijeriya da Jamhuriyyar Nijar.
Fati Nijar tana yin waƙoƙi na sitidiyo a ƙungiya da kuma a kaɗaita. vii) Wasu waƙoƙin Fati Nijar sun haɗa da:
– Waƙar ‘Ɗan Amina’
– Waƙar ‘Girma-Girma’
– Waƙar ‘Nijar-Nijeriya’
– Waƙar ‘Ala Gidigo’
– Wakar ‘Na yi Ritayar So’
– Waƙar ‘Duniya’
– Waƙar ‘Uwa mai Gyara ɗanta’
– Waƙar ‘Dawo Aliyu Dawo’
– Waƙar ‘Gamji Jijjige’
– Waƙar ‘Manguno’
– Waƙar ‘Gidan Sauro’
– Waƙar ‘Musa Ango’
– Waƙar ‘Al’amarin Hassan yana ban Mamaki’1
– Waƙar ‘G Cell’
– Waƙar ‘Fati Nijar ba ta Mutu ba’
– da sauransu
Farfesa Sa’idu Muhammad Gusau
Alhamis 26/4/2018
Edita; Rumasa’u Muhammad Kallamu