Siyasa

0
6

Babahabu49

GABATARWA

Adabi sha kun dum ne cikin al’amuran rayuwar al’umma, kama daga abincinsu, abin sha, tufafi, kai har siyasa adabi bai bari ba, ya ratsa cikin rassan adabin nan uku, wato:Zube, Waƙa da kuma Wasan kwaikwayo.

MA’ANAR SIYASA

Siyasa hanya ce da mutane ke bi wajen rayuwa a haɗe, ko a tare, ko a ƙungiyance cikin manufa ɗaya. Siyasa na nufin haɗa yarjejeniya tsakanin mutane domin su zauna tare duk da maban-bantan ra’ayoyi, ƙabilu da addinai, a birane da ƙasashe.

MA’ANAR SIYASA DAGA BAKIN MASANA

Manzur (1978) Ya kawo asalin inda kalmar siyasa ta samo asali. Inda ya ce”Ta samo asali ne daga “sa’asa” sai ta koma “siyasa” wato ma’anarta tafiyar da shugabancin jama’a ko kuma july away kan wani al’amari ko yarda da wani abu ko jiɓintar al’umma tare da saninsu ko kuma ba su sani ba”

Bargery (1934) Ya ce”Siyasa na nufin ko dai rangwame a farashin kowane abu, ko kuma tausayawa a cikin al’amura”

Manzur (1978) Ya ce “Siyasa na nufin ilimi ne dake nuni da kuma gabatar da hanyoyi da manhajoji mabanbanta a cikin gida da kuma alaƙanta da al’umma a waje”.

NAU’O’IN SIYASA

Dangane da yadda zamani yake tafiya, haka nau’in siyasa ya dinga ratsuwa a tsakani har aka samu nau’i kamar haka:

-Siyasar Gargajiya.

-Siyasar Addini.

-Siyasar Mata.

-Siyasar Jami’a .

-Siyasar Jam’iyya.

Ga taƙaitataccen bayaninsu.

* Siyasar Gargajiya: Idan aka ce “Gargajiya”wato abin da al’umma ta gada tun daga kaka da kakanni kafin wasu al’ummu su yi kutse cikinsu.

Siyasar Gargajiya siyasa ce da aka samo ta daga addinin gargajiya, wanda wasu na ganin bauta ta gargajiya da imani da iskoki dodanni ita ce tsari na samar da shugabanci a tsakanin al’ummar Hausawa, wanda duk wani mai ƙarfi ko jarumi a wurin bauta da alaƙa da dodanni ko iskoki to shi ne jagorancin kuma shugaba, don kuwa babu wani mai iya taka shi ko mai musu da shi.

*Siyasar Addini: Nau’in wannan siyasa ita ce wacce ta shafi addinin musulunci, wanda ake samun shugaban da hukunce-hukunce daga Alƙur’ani da Hadisi.

*Siyasar Mata: Ƙwarai su ma mata ba a bar su a baya ba, don tun lokacin da aka haɗa kudancin Nijeriya da Arewa a shekarar 1914 mata suke taka rawar gani a siyasar jam’iyya. Ko a yanzu za mu ga a Jihar Kaduna Dr. Hajiya Hadiza Balarabe ita ce mataimakiyar Gwamnan Jihar a 2019 zuwa 2023. Haka kuma ita ce za ta yi wa zaɓaɓɓen Gwamnan wato Sanata Uba Sani a shekarar 2023 zuwa 2027.

Haka Hajiya Aisha Binani, ita ce Waƙiliyar Majalisar Dattawa a yankin garin Adamawa, haka kuma ta fito takarar Gwamna, wanda ita ake tsammanin cin ta, sai dai abin akwai ruɗani, sai an sake fafata zaɓen Jihar.

*Siyasar Jami’a:Irin wannan siyasar ita ce wacce ake gudanar wa a farfajiyar Jami’o’i, kuma ana gudanar da ita ne irin tsarin siyasar Damukuraɗiyya, akwai tsarin Kwansutushon da komai.

Babban misali kuwa idan muka kalli wannan Jami’ar da muke ciki ta Jihar Kaduna (KASU) za mu ga ita kanta ana fafata siyasar a cikinta. Shugaban ɗalibai na shekarar 2021/2021 shi Abdulhamid Umar, bayan shi kuwa Abubakar Abdullahi ne ya hau a shekarar 2021/2022.

*Mashi (1986) ya bayyana siyasar jam’iyya da cewa “Jam’iyya tana nufin wata ƙungiya mai wakiltar wani ra’ayi na neman mulkin al’umma, irin wannan ƙungiya akan same ta a ƙasa ɗaya ne, kuma sukan yawaita yadda manufofinsu suka kasance, wannan shi ne ya jawo samun hanyoyin siyasa iri-iri, wato akan sami salon siyasa na Damukuraɗiyya, wato mulkin al’umma ta hanyar abin suke buƙata, kuma suke da ikon tarfe ra’ayinsu cikin lamarin tafiyar da mulki” Wannan ke nuna siyasar jam’iyya tana nufin irin gwagwarmayar da jam’iyyan suke yi don neman kafa gwamnati da saman mulkin al’ummar ƙasa.

A taƙaice ma iya cewa siyasar Jam’iyya dai wata ƙungiya ce da take gudanar da siyasarta a jam’iyya ɗaya da samun haɗin kai don su kayar da wata jam’iyya daban wato ta abokan hamayya.

A ƙarƙashin wannan siyasar ta jam’iyya akwai Jamhuriyya har huɗu, inda kowacce Jamhuriyya akwai rawar Jam’iyyu da dama da suka taka rawa a ƙarƙashinta.

*Jamhuriyyar Najeriya ta farko (1963 – 1966)

Akwai jam’iyyu kamar su :

AG, BYM, DP, KPP. Da sauransu

*Jamhuriyya ta Biyu (1979 – 1983)

Akwai jam’iyyu kamar su:

PRP, NPP, NAP, NPN, Da sauransu.

*Jamhuriyya ta uku (1993)

Akwai jam’iyyu kamar su:

SDP, NRC.

*Jamhuriyyar Najeriya ta Hudu (1999 – yanzu)

Akwai jam’iyyu kamar su:

CND, JP, CNC, APC, CPC, PDP, Da sauransu.

Yanzu za mu ɗauki ɗauki waƙa ta Jamhuriya ta farko don fito da hoton siyasa a ciki.

WAKAR ‘YAN SAWABA GAMBO HAWAJA JOS.

Wannan waƙa ta ƙunshi hotunan siyasa da dama kamar su: son yunƙurin canja jam’iyya yayin da aka gane zaluncinta, kamar yadda ya faɗi a baiti na 10 zuwa na 17.

AMSHI: Allahu Taimaki NEPU Kan Azzalumai

10. Albarkacin Manzonka zan yabi jam’iya,

Mai son ta tunɓuke zaluman Nijeriya.

11. Mu ne mutanan nan da munka fito biɗar,

‘Yanci ya samu a tsarkake Nijeriya.

12. Ita jam’iyar NEPU ta ɗau aniya,

Sai ta ga bayan zalumanga masha giya.

13. Ta ɗau makamai sun fi bom har bindiga,

Kun san su ko in faɗe su su ne gaskiya.

14. Iggwa da bom bai magani in sun zaka,

Wa ke da ikon dankwafe wa gaskiya.

15. Kai fankashali shazumami ka dakata,

Koron da ba shi da nasa sai ƙwalamar tsiya.

16. Kai baka noma ba fatauchi ko kaɗan,

Kuma ba sana’a sai yawan faharin tsiya.

17. Na tabbata ɗan NEPU ba zai so ka ba,

Tamkar ƙudan shadda ya sauka a kan miya.

Haka daga baiti na 18 ya yabi jam’iyyar,kuma ya nuna da su za su samu nasara gami da kirari ga jam’iyyar ta NEPU har zuwa 20.

18. Mu NEPU mu ne kainuwa bisa kan ruwa,

Wawan da zai taka mu shi zai dulmiya.

19. Ga NEPU dutse ba a far maka nan da nan,

In munka far wa zalumi zai sha wuya.

20. Mu ne tsakin tsakuwa a gun azzalumai,

Kafin a ci mu aradu sai an sha wuya.

Haka tun daga na 21 zuwa na 40 Ya fito da nuna addinanci ne a siyasa, don kuwa ya bayyana yadda za a tsani wanda ba musulmi ba kwata-kwata da shugabanci, don kuwa munanan halayensu da ɗabi’unsu marasa kyau.

21. Kai turdimi jaki daƙiƙin duniya,

Ƙaton cikin wofi na cinye haramiya.

22. Ni zan gaya maka gaskiya in za ka ji,

Bar sa Wali a cikin a batun dab a shi da gaskiya.

23. Don Shehu bai ja kafiri a jikinsa ba,

Shi sai musulmi wanda ke riƙe gaskiya.

24. Bai je cikin hotel ba Shehu Mujaddidi,

Kuma ba shi ƙarya bai zama da masha giya.

25. Har yai wafati Shehu bai cuce mu ba,

Allah Ya gafarce shi Shehu mazan biya.

26. Ku jakunan Sheɗan ba za ku ga Shehu ba,

Bar sanya Shehu cikin batunku na jam’iya.

27. Kaka, uba bai fidda dan sa ga hallaka,

In dan yace bai kama hanyar gaskiya.

28. Kuma ga misali jalla Ya saukar mana,

Aya a kan Kan’ana inda ya dulmiya.

29. Kai mai kirarin martabar kaka tsaya,

Ka tuna Hassan da Hussaini sun riƙe gaskiya.

30. Bar taƙamar kakanka ban ga fitar ka ba,

Kakanka baya yin hannu da baturiya.

31. Kuma bashi cewa goro ai masa jangali,

Shi bai kawa da Nasara ba ya shan giya.

32. Gemunka har sajenka ba shi da martaba,

In dai ya zam aikinka babu na gaskiya.

33. Ɗan wane jikan wane ba ta isar maka,

Allahu Ya ce sai kana bin gaskiya.

34. Mai ɗaura bante in ya bayyana gaskiya,

Ya zarce mai rawanin da ke son dulmiya.

35. Da martabar kaka ka mulkin duniya,

Awolowo shi kuma wa ya ba shi Firimiya?

36. Kai gafara sa ya ishe ni ku dakata,

Ba na gudu sai na ga goshin saniya.

37. Sun raina hanyar Shehu sun bijire masa,

Ba sa buƙatar lahira sai duniya.

38. Su dai su hau mota su sauka a hil tasha,

Ran Jumu’a ran nan suke shagalin giya.

39. Da ya yi imani ya dubi mazan gaba,

Da sukai sarautar duniya baki ɗaya.

40. Ba su shuka sharran don su cuci waninsu ba,

Su sai shirin da sukai a taimaki gaskiya.

Haka daga 40 zuwa 58 ya suka jam’iyyar hamayya wato NPC da kuma waɗanda suke cikinta.

46. Ba na cikin NPC ba na son shiga,

Manyansu ba sa taimakon Nijeriya.

47. Na raina jam’iyarsu masu abin faɗa,

Ni na tsaya kan NEPU tutar gaskiya.

48. Tutar da ba ta da jahili ko zalumi,

Da baƙi da ja kore farar taurariya.

49. In ban da wawa jahili da rashin shina,

Wai zai bi jam’iyar da ba ta da gaskiya.

50. Wallahi Allah zan faɗa muku ‘yan uwa,

Talakan da ke NPC ba shi da zuciya.

51. Daga dai kawali sai maroƙi ke shiga,

Sai wanda zai ƙi ubansa don kwaɗayin miya.

52. Kuma mai kuɗin da ka ganshi ya shiga tabbata,

Ya raina nasa yana biɗar na haramiya.

53. Ku ne talakka uba talakka uwa haka,

Wai har da ɗan sarki kuke gama jam’iya.

54. Kurdinku ya ruɗe ku kunyi abin faɗa,

Don kun ki bin asalinku kun bi masha giya.

55. Ko mai kuɗi ko malami da ya karkata,

Allahu shawo kan sa mui masa fatiya.

56. Asirin cikin riga jama’a na tuna,

Zan bar uba domin ɗiyansa na gaskiya.

57. Na ‘yanta rand don ruwan da yake ciki,

Ba don wadansu ba wane da ya sha wuya.

Tun daga na 89 zuwa na 117 duk yana shimfiɗa habaici da zage-zage da zambo kan ‘yan jam’iyyar adawa.

89. Babban abin kunyar da sunka yi zan faɗa,

Wasu tajirai suka je su gai da Firimiya.

90. Police ya ce babban su, Alhaji dakata,

Koma, idan kuwa ka ƙi yanzu ka sha wuya.

91. Wani turdumi dunan amale kututtuɓi,

Kun san shi ko in faɗe shi, gara mu sakaya.

92. Ya tattare cuna ya gangare hel tasha,

Ya dafe kansa yana gudu ba waiwaya.

93. Ya manta rancen dukiyar da ya tambaya,

Ya tuna da kwanan yari, gara ya sakaya.

94. Im ban da jahilcinka ba ka da hankali,

In anka cinye kuɗinka sui maka dariya.

95. Bayan watanni ‘yan kaɗan suka tabbata,

Kurɗinka sun kare su sa ka a jam’iya.

96. ‘Yan NEPU don ba su ce a cinye kuɗinka ba,

NPC ba ta biyanka wannan dukiya.

97. Na tabbata ɗan NEPU bai ci kuɗinka ba,

Ɗan NPC ne ya ci dukiyarka ta dulmiya.

98. Mai son yana da sule biyar a yi mai jaka,

Ba na saka shi cikin mutanen gaskiya.

99. Koma Kaduna ka nemi mai maka tsibbu can,

Kuma na ji ba shi Kaduna ya tafi Zariya.

100. Jama’a takarda na gaba ta mantuwa,

Na gan ta na tuna jahilin tsohon tsiya.

101. Duk fasiƙin tsohon da bai tsare kansa ba,

Wallahi in muka gauraya zai sha wuya.

102. Wani ɗan farin tsoho cikinsa baƙinƙirin,

Ya manta Allah ya ji ruɗin dukiya.

103. Mai shekara saba’in ka gan shi da daduro,

Me zan kira shi ku ce da shi tsohon tsiya.

104. Tsohon da bai san Fatiha ba munafiki,

Bakinsa na kumfa ya bakin saniya.

105. Duka fasikin tsohon da ba zai tuba ba,

Wallahi zai tozarta tun daga duniya.

106. Kai danƙaro mai danne tsaba, ka ɓata,

Sha talla doki ba ido wa zai saya.

107. Ɗaukar macuci ban ga amfaninta ba,

Noman kisan gero a kewaye harkiya.

108. Yau duk mutan NPC in na ƙididdige,

Maciya amana sai ɓarayin tunkiya.

109. Sai wanda zai baki ya kai su cikin tasha,

Ya gama da ‘yan sane su ɗauke dukiya.

110. Wa ke shiga NPC ban da munafiki,

Sai Alhajin da ya kasa ƙarasa Fatiya.

111. Ko yai karatu in ka bi shi a hankali,

Ka tadda imaninsa babu a zuciya.

112. Jama’a masoya NEPU kar ku yi fargaba,

Wallahi ƙinsu da sonsu ma faɗi gaskiya.

113. Duk mai abin kunya ba zai shiga NEPU ba,

Wallahi ko da ya shigo ta da sakiya.

114. Kai kyankyaso kwaɗayinka bai fishshe ka ba,

Koma cikin shadda, fito daga tsariya.

115. Wani sakarai maganarsa in muka bincika,

Muka buɗa tarihinsa sai a yi dariya.

116. Don sai da tsohon yai shiri yai gangara,

Sannan ya nemi shiri da shi don dukiya.

117. Jama’ar garin muka taru dai aka lallaɓa,

Mutuwarsa ke da wuya ya kwashe dukiya.

Idan muka dauba, za mu ga cewa lallai a wannan waƙa an fito da wasu ƙaɗan daga cikin hoton siyasa dangane da adabi, kamar yadda muke shantalo wasu baitika mu tsatso ma’anonisu a dunƙule.

Ga wasu halayyan ‘yan siyasa ko abin da ya shafi siyasa a wannan waƙa kamar haka:

-Yabon jam’iyya, wato ta NEPU.

-Kirari wa jam’iyya don janyo ra’ayin mutane.

-Nuna Addinanci don a samu damar sukar jam’iyyar adawa.

-Sukar jam’iyyar Adawa wato NPC

-Zambo da zagi da habaici wa jam’iyyar adawa.

KAMMALAWA

Duba da yadda muka tsatso hoton siyasa a wannan waƙa ta NEPU, za a ga cewa lallai ana tsintan abubuwa da dama da suka shafi siyasa a rubutaccen adabi ko kuma adabin baka.

MANAZARTA

-TARIHIN SIYASARNIJERIYA,FACEBOOK GROUP.

-Bawa S 2021


,Siyasa da adabi ;nazari daga wasu rubutattun labaran Hausa.Sashen harsunan Nijeriya da kimiyyar harshe Jami’ar Jahar Kaduna.

-C.N.H.N(2006) Ƙamusun Bayero.Jami’ar Bayero Kano.

-Waƙa a bakin mai ita1,center for nigerian languages,Bayero University,Kano.

Danna nan don karanta Haɗuwar Harshe

Edita@rumasau-kallamu

 

labarin da ya wuceAdana Harshe (LANGUAGE PRESERVATION)
Labarin na GabaMatakan Shiga Shaye-shayen Miyagun Ƙwayoyi