“Wanda ya mallaki bayanai, ya mallaki duniya”
-Nathan Rothschild.
Guglielmo Marconi, Reginal A. Fessenden da sauran waɗanda suka ba da gudumawa wurin samar da rediyo don wasu amfani da a tunaninsu bai taka kara ya karya ba. Amma bayan wasu ƙarnuka masu yawa da wucewar su, an samu ci gaba sosai a rayuwar mutane, wannan yasa an fahimci tasirin rediyo da kuma gidajen rediyo. Musamman idan muka kalli ƙasashen Turai a yaƙin duniya na biyu, sun yi amfani da gidan rediyo don yaɗa farfaganda. Saboda sanin mahimmanci da tasirin rediyo ya sanya ƙasashe kamar su Birtaniya buɗe sashen Hausa da sauran sassa da ba na Turancin Ingilishi ba, don cimma manufofinsu.
Gwamnatoci sun fahimci tasirin da rediyo take da shi a rayuwar waɗanda ake mulka, wannan yasa gwamnatoci kakkafa gidajen rediyo don isar da manufofinsu da ƙudurorinsu, wasu lokutan don isar da wata manufa ta ƙashin shugabannin. Haka ma manyan ‘yan kasuwa/attajirai da `yan siyasa sun fahimci wannan tasiri da rediyo take da shi, su ma sai suka fara kakkafa gidajen rediyo don tallata manufarsu na kasuwanci ko siyasarsu.
Wannan tasiri za mu iya ganin shi a fili, idan muka kalli yadda mutane da yawa suka mai da rediyo makusanciya ta mussaman, wadda ba a iya rabuwa da ita, don harkar saye da sauran mu`amala da ita. Mutane sun mayar da gidajen rediyo wurin samun labaru da sanin abin da yake faruwa na yau da Kullum. Wasu lokuta yadda mutane suka yi amanna da duk abin da aka faɗa a gidajen rediyo, yakan zamo abu mai wahala kafin ka canza su. Ba wani abu ba ne, sai tasirin abin da aka faɗa ta hanyar rediyo da yawan nanata shi.
A Kano an fara kafa gidan rediyo mai zaman kansa ne a shekarar 2003, tun daga wannan lokaci ya zuwa yanzu, ana hasashen gidajen radioyo masu zaman kansu sun kai sama da guda ashirin (20+). Mai karatu ya san duk waɗannan ba a banza ake buɗe su ba, amma babban abin lura shi ne an fahimci tasirinsu ne a cikin al`umma da rayuwarsu.
Duk wanda ya buɗe gidan rediyo yana da dalilinsa da manufar da yake so ya isar ko ya cimma, ba manufar kaɗai ake gabatarwa a waɗannan gidajen radiyo ba, ana gabatar da wasu shirye-shirye na daban waɗanda su ma suke da tasirinsu a cikin rayuwar mutane. Kamar shirye-shiryen abubuwa da suke faruwa na yau da kullum a cikin al`umma. Duk wanda yake Kano ko yake sauraron shirye-shiryen gidajen rediyoyin Kano, ya san irin waɗannan shirye-shiryen, waɗanda aka samo daga wani shiri daga gidan rediyon Kano mai suna “Taskar Labarai”.
Waɗannan shirye-shirye suna da matuƙar tasiri a cikin rayuwar mutane fiye da yadda ake tsammani. A mafiya yawan lokuta, a waɗannan shirye-shirye ana yawan kawo labarukan manya-manyan laifuka, kamar fyaɗe ga ƙananan yara. Duk lokacin da aka yi wa masu gabatar da waɗannan shirye-shirye magana kan yadda suke faɗan waɗannan laifuffuka, sai su ce kaso mafi ƙaranci na irin abin da yake faruwa da suka samu haƙiƙanin labarai a kai suke faɗa.
Tasirin irin waɗannan shirye-shirye ga tarbiyya, abu ne mai girma wanda ba a ganin tasirin abin a lokaci guda. Amma idan an lura sosai suna da tasiri mai yawa ga tarbiyya. Idan muka dubi abin ta ɓangaren tarbiyya, za mu ga irin waɗannan shirye-shirye suna da mummunan tasiri ga tarbiyya ta ɓangarori kamar haka:
Na farko duk abin da ake faɗa a fili musamman ta hanyar rediyo, bisa dukkan dalilai yakan kai inda ba a zato, to a nan, ana sanar da wanda bai sani ba, sannan ana tunatar da wanda ya manta, ana kuma jaddada wa wanda ya sani wani abu. Shi kuma a shari’ance da tarbiyya, ba a son bayyana ɓarna. A hadisin Abi Hurairah ya ce, na ji Manzon Allah (SAW) ya ce: “Dukkan al`umata waɗanda ake yi wa rangwamen zunubansu ne (wato ana yafe musu) sai masu bayyana ɓarna” – ba masu aikin gidan rediyo ake nufi a nan ba, ana nufin waɗanda idan suka aikata ɓarna a ɓoye sai su fito fili suna faɗa. Waɗannan su ake nufi. Amma mene ne dalilin da ya sa aka ce ba a yi wa masu bayyana ɓarna rangwame? Saboda koya wa wasu suke yi, kuma nuna wa wanɗanda da ba su sani ba suke yi da kuma tunatar da waɗanda sun gafala daga aikata ɓarna suke yi. Wannan shi ne abin da suke yi kenan. Wanda bai san fyaɗe ba, an faɗa masa kenan sai ya fara tunanin aikatawa da hanyar da zai kauce, kada a kama shi kamar yadda aka kama na baya.
Na biyu yawan fadin waɗannan laifuffuka, yakan dasa waɗannan laifuffuka a zuciyar mutane, musamman matasa. Shi yasa za a ga matasa sun fi kowa yawan faɗawa cikin ɓarna da laiffufuka musamman waɗanda ake yawan tallata su”
Na uku yawan fadin laiffufuka yana ƙara yawaitar su, da ƙaruwarsu. Misali a yanzu zai yi matuƙar wahala a yini ba a ji labarin garkuwa da mutane ba, tun ana jin labarin a Kudancin ƙasar nan, yanzu ga shi har gida kuma ƙaruwa yake yi a kullum. Duk da akwai dalilai daban-daban na ƙaruwarsa, wanda rashin ɗaukar ƙwaƙƙwaran hukunci a kan masu aikitawa yake ƙara yaɗuwarsa da sauransu.
Misali na biyu na irin shirye-shiryen da gidajen rediyoyi suke gabatarwa mai tasiri sosai a cikin al`umma su ne shirye-shiryen siyasa. Ta yadda ake bai wa mutane dama su faɗi albarkacin bakinsu. Mutane da yawa ba sa lura da mummunan tasirin abin ga tarbiyya. Idan muka duba sosai kafin yaɗuwar gidajen rediyo da waɗannan shirye-shiryen a Kano, malamai da sarakuna da kuma manyan mutane suna da matuƙar ƙima da daraja a idon mutanen gari, amma a yanzu saboda waɗannan shirye-shirye ya sa mutane da yawa sun samu dama na cin mutuncin malamai da sarakuna da kuma shugabannin al`umma. A Kano kowa ya san a yanzu waɗannan mutanen da na faɗa a sama duk da ƙimar da suke da ita a baya, kowa yana iya shiga gidan rediyo ya faɗi maganar da yake so a kansu kai tsaye. Wannan tasirin waɗannan shirye-shiryen ne kai tsaye.
A bangaren tarbiyya, rashin girmama babba a al`umma alamu ne na rugujewar tarbiyya da taɓarɓarewar al’umma, kuma alama ce ta lalacewar wannan al’umma. Tasirin waɗannan shirye-shirye kenan ga tarbiyya.
Wannan su ne kaɗan daga cikin tasirin gidajen rediyo a rayuwar al’umma da tarbiyyarsu. Saboda haka, ya kamata mu san irin shirye-shiryen da ya kamata mu dinga saurara. Sannan kuma lallai shugabannin addini su tashi su faɗakar da mutane game da irin waɗannan abubuwa da suke lalata tarbiyyar al’umma.