Shin ko ya Halatta A Je Wajen Boka Ko Ɗan tsubbu Domin Sihirce Kishiya?

0
964

A’a, ina fa zuwa wajen boka ko ɗantsubbu (mai duba) zai halatta! Ai haramun ne a Musulunce, Musulmi ya je wajen boka ko ɗan tsubbu (mai duba), ko da kuwa da nufin ya tambaye su ne, ballantana kuma ya yarda da abin da za su gaya masa na bokancin ko kuma duban.

Dalili kuwa Imamu Muslim ya rawaito hadisi da aka karɓo shi daga Hafsa (Radiyallahu An ha) daga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: “Duk wanda ya je wajen wani mai jin yana da masaniyar abubuwa tun kafin faruwar sa sai ya tambaye shi game da wani abu, to, ba za a karɓi wata sallarsa ba har tsawon kwana arba’in.
Idan kuwa har musulmi ya kuskura ya gaskata abin da boka ɗan duba ya gaya masa, to ya yi asarar imaninsa. Dalili kuwa an karɓo hadisi daga Abu Huraira (Radiyallahu An hu) daga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: “Duk wanda ya je wajen boka ya gaskata shi game da abin da yake faɗa, to, haƙiƙa ya kafirce wa abin da aka saukar wa Annabi Muhammadu tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi. Abu Dawud, Tirmizi, Ibn Majah, Darimi da wasun su ne suka rawaito shi.
Sannan kuma a dangane da sihirce kishiya; akwai cutar da mumina, baiwar Allah, ga shi kuwa Allah maɗaukaki ya ce:
Ma’ana
“Waɗanda suke cutar muminai maza da mata, ba tare da sun yi laifi ba, to, haƙiƙa sun ɗauki nauyin ƙage da kuma zunubi bayyanan ne”.

Wannan bayani an ciro Shi ne daga littafin Duhun Kai Gaba Da Kishiya wanda Abubakar Abbas ya wallafa shi Domin karanta cikakken littafi danna nan.

labarin da ya wuceAbubuwan Dake Sa Kishiyoyi Shiri da Zaman Lafiya.
Labarin na GabaHira, ko Kuma Shiga Ɗakin Wata Daga Cikin Matar Da ba Ranar Kwananta ba.