Shayarwa aiki ne da Allah SWT ya tsara halittar jikin mace ta riƙa yinta a duk lokacin da ta haihu, domin samar da ingantaccen abinci ga jariri da kuma nuna masa ƙauna. Kadan daga cikin muhimman abubuwan da ya dace mu sani game da shayarwa su ne:
1. Amfaninta ga jariri (breastfeeding benefits to the baby):
Shayarwa tana samar da ingantaccen abinci ga jariri daidai da buƙatar jikinsa, domin yin girma yadda ya kamata. Nonon uwa yana ƙunshe da ƙwayoyin halitta masu bayar da kariya ga jikin jariri (antibodies) don su tsare shi daga cututtuka iri-iri. Sa’annan tana kare jarirai daga hatsarin mutuwa farat ɗaya (Sudden Infant Death Syndrome – SIDS).
2. Amfaninta ga uwa (breastfeeding benefits to the mother):
Shayarwa tana taimakon jikin mai-jego wajen saurin murmurewa daga ciwon haihuwa (faster postpartum recovery), ta hanyar sanya mahaifarta ta koma yadda take kafin samun juna biyu. Sa’annan tana matuƙar rage hatsarin kamuwa da cututtukan daji na nono (breast cancer), da mahaifa (uterine cancer), da jakar ƙwan haihuwa (ovarian cancer). Bugu da ƙari, tana ragewa mace hatsarin kamuwa da cutar rashin ƙarfin ƙashi (osteoporosis) wanda yakan iya samunta a lokacin ɗaukewar al’ada (menopause).
3. Ingantacciyar shayarwa ta hanyar sanya jariri ya kama kan nono sosai (establishing good latch):
Ya kamata uwa tana rungume jaririnta da kyau kuma ta tabbatar kewayen nan mai launin duhu na kan nono (areola) ya shiga cikin bakin jariri a lokacin shayarwa, ba kan nonon (nipples) kawai ba. Idan baki iya ba, to, ki nemi ‘yan uwanki su koya miki. Hakan zai kare mace daga matsalolin tsagewar kan nono (nipples crack).
4. Shayarwa a kai-a kai (breastfeeding on demand):
Jarirai sukan sha nono a kai-a kai, don haka uwa ta tabbatar da cewa tana bai wa jaririnta nono a ƙalla bayan duk awa 2 zuwa 3. Idan yana buƙata ma kafin wannan lokacin, to, ta ba shi. Hakan zai kare ta daga matsalolinmu ciccikowar nono (breast engorgement).
5. Isasshen ruwan nono (breast milk sufficiency):
Ruwan nono yana taruwa ne gwargwadon yadda mace take ƙoƙarin shayarwa tare da cin wadatacce kuma ingantaccen abinci. Ma’ana, idan mace tana shayarwa akai-akai, to, ruwan nononta zai yi saurin taruwa. Idan kuma ba ta shayarwa akai-akai, to, za ta fuskanci ƙarancin ruwan nono.
6. Matsalolin shayarwa (breastfeeding challenges):
Yawancin mace takan fuskanci matsaloli a lokacin shayarwa, kamar, ciccikowar nono, tsagewar kan nono, ƙarancin ruwan nono, ciwon nono, da sauransu. Idan hakan ya faru, to, a je asibiti domin a yi abinda ya kamata.
7. Matse ruwan nono (breast milk expression):
Idan nonon mace yana samar da ruwan nono fiye da buƙatar jaririnta, to, za a iya fuskantar matsalar ciccikowar nono, wanda zai haifar da zazzaɓi. Domin kaucewa hakan, ana iya matsewa a cikin mazubi mai tsabta domin ta bai wa jariri a lokaci na gaba. Ga matan da suke zuwa wurin aiki a ofisoshi kuwa, suna barin jariransu a gida, to, shikenan sai a riƙa bai wa jariran ruwan nonon da suka matse. Ana yin matsewar ne da hannu (hand expression), ko da na’urar matsewa (breast pump), wanda ba duk mata ne suka sanshi ba.
Daga ƙarshe ya kamata musan cewa shayarwa abu ce ta halitta (natural). Idan mace tana yinta bisa ƙa’ida, to, bai kamata ta ji zafi ba. Idan mace tana Shayarwa kuma tana jin zafi to yana nuna cewa akwai matsala, don haka sai a yi ƙoƙarin gane ta kuma a magance ta.
Karanta Menene Ƙaiƙayi? (ITCHING)
Edita@rumasau-kallamu