Shan Azumi Ga Matafiya

0
17

SALMANU FARISS ADAMU

Shari’ar Musulunci ta sauƙaƙawa matafiya, idan za su yi tafiya wacce za ta ba su wahala sosai, sai su ajiye azumin su, bayan sallah, sai su rama abin da suka sha, kamar yadda wannan hadisin ya nuna mana haka;

حدثنى يحي عن مالك عن هاسم بن عروة عن أبيه: أن همزة بن أمرو لأسلمى قال لرسول لله صلى الله عليه وسلم يارسول لله إنى رجل أصوم أفأصوم فى السفر, فقال له رسول الله صلى الله عليه وسلم :إن شئت فصم وإن شئت فأفطر.

An ruwaito daga Yahaya daga Malik daga Hashim bin Urwata daga mahaifiyarsa (yace) Tabbas Hamza bin Amru Al-asalami yace ga Mazon Allah (Sallallahu alaihi wasallam), Ni mutum mai azumi shin zan iya ajiye azumi (idan tafiya ta kama Ni), idan kuma ka so ka yi azumi, idan kuma ka so ka sha azumi.

Saboda haka ba wajibi ne a kan matafiya a duk lokacin da za su yi tafiya, sai sun sha azumi ba, saboda wannan hadisin na annabi (Sallallahu alaihi wasallam), ya nuna mana idan ka so ka yi azumi, haka kuma idan ka so ka ajiye azumi, ka ga a nan an ba shi zaɓi ne, amma idan matafiya sun ƙi shan azumin a cikin tafiyarsu, babu laifi a kan su, sannan kuma azumi a cikin azuminsu ya yi, Saboda ba cewa aka yi dole sai mutum ya ajiye azumi, idan zai yi tafiya zuwa wani wajen.

حدثنى مالك عن نافع : أن عبيدالله بن عمر كان لا يصوم فى السفر.

An ruwaito daga Malik daga Nafi’u (yace) Tabbas Abdullah bin Umar ya kasance yana cewa ba ya yin azumi idan zai yi tafiya.

حدثنى مالك عن هاشم بن عروة عن أبيه : أنه كان يسافر فى رمصان ونسافرمعه فيصوم عروة ونفطر نحن,فلا يأمرنا بالصيام.

An ruwaito daga Malik daga Hashim bin Urwata daga mahaifinsa (yace), Tabbas ya kasance, yana yin tafiya a cikin watan Ramadan, sannan kuma muna tafiya tare da shi, sai Urwata ya yi azumi, mu kuma sai mu sha azumi (Sannan shi Urwata) ba ya umartan mu da mu yi azumi.

Abin nufi a nan shi ne, sun kasance suna tafiya tare da Urwata, sai wata rana Urwata ya tashi da azumi, sai su kuma su sha azumi, Saboda annabi Muhammda (Sallallahu alaihi wasallam) yace an sauƙaƙa ga wanda zai yi tafiya ya sha azumi, bayan sallah sai ya rama abin da ya sha.

Sannan kuma a wannan lokacin shi Urwata ba ya takura musu ko Umartarsu da yin azumi, saboda wannan dalilai, amma idan mutum zai yi tafiya sai ya ƙi ajiye azuminsa, azuminsa ya yi, saboda ajiye azumin ba wajibi ba ne.

Bugu da ƙari kuma, idan mutum yana azumi, sai tafiya ta kama shi, sai kuma ya ji tsoron zai sha wahala a cikin tafiyarsa, sai ya ajiye azuminsa, bayan sallah sai ya rama abin da ya sha.

حدثنى مالك عن إبن شهاب عن عبيدالله بن عبدالله بن عتبة إبن مسعود عن عبدالله بن عباس: أن رسول لله صلى الله عليه وسلم خرج إلى مكة عام الفتح فى رمضان ,فصام حتى بلغ الكديد, ثم أفطر فأفطر الناس,وكانوا يأ خذون بالأحدث فالأحدث من أمر رسول لله صلى الله عليه وسلم.

An ruwaito daga Malik daga Ibin Shihab daga Ubaidullah bin Abdullah bin Utbatu bin Mas’ud daga Abdullah bin Abbas (yace), haƙiƙa Mazon Allah (Sallallahu alaihi wasalla) ya fita zuwa garin Makkah, shekarar Fatahu Makkah (Buɗe Makkah) a cikin watan Ramadan, sai ya tashi da azumi, har sai da suka kai Kadida (sunan wani guri a tsakanin garin Makkah da Madina) sai (Annabi) ya sha azumi, sai su ma mutanen (Sahabban da ke tare da shi) suka sha azumi, har zuwa ƙarshen wannan hadisi.

Saboda haka wannan hadisi ya nuna mana matuƙar mutum ya ji zai sha wahala sosai a cikin tafiyarsa zai iya shan azumi, ko rashin lafiya da sauransu. Amma kuma an ruwaito daga Umar bin Khaɗɗab ya kasance idan zai yi tafiya ba ya shan azumi kamar haka;

حدثنى يحي عن مالك أنه بلغه: أن عمر بن الخطاب كان إذا فى سفر فى رمضان فعلم أنه داخل المدينة من أول يومه دخل وهو صائم.

An ruwaito daga Yahaya daga Malik, labari ya same shi (cewa) haƙiƙa Umar Ibn khaɗɗab ya kasance yana tafiya a cikin watan Ramadan ba ya shan azumi, idan ya san tabbas zai shiga garin Madina a farkon ranarsa (sai ya yi azumi) alhalin shi yana azumi.

قال مالك :وإذا أراد أن يخرج فى رمضان ,فطلع له الفجر وهو بأرضه قبل أن يخرج فإنه يصوم ذالك اليوم.

Imam Malik bin Abbas yace idan yai nufin zai yi tafiya a cikin watan Ramadan, sai alfijir ya fito yana cikin garinsa, kafin ya fito sai ya yi niyyar azumin wannan ranar.

Abin nufi a nan, idan Imam Malik ya haraman tafiya zuwa wani gari da Asubah, sai ya ta shi da azumi aranar, sannan kuma ya yi tafiyarsa zuwa garin da ya yi niyyar tafiya yana azumi, saboda shan azumi ba farillah ba ne.

Haka ma babu laifi a kan matafiyin da zai yi tafiya, sai ya ji tsoron zai sha wahala, sai ya ajiye azumi, sannan ita ma matarsa ta ajiye azumi, zai iya ganawa da ita da rana matuƙar ba ta jin haila, amma a wannan hali kaɗai, saboda ba sa yin azumi, sannan kuma shari’ a ta amince su, amma idan don kawai suna so za su gana ne, to akwai kaffara a kan su.

Danna nan don karanta Sumbatar Mace Ga Me Azumi

Edita@rumasau-kallamu

labarin da ya wuceMutuwar Mata Masu Jego
Labarin na GabaƘaiƙayi Mai Kamar Tafiyar Kiyashi A Jiki (Formication)