Sallar Idi

1
19

SALMANU FARISS ADAMU

Idin musulmi guda biyu ne, idin buɗa baki (karamar sallah), bayan watan Ramadan, da idin layya (Babbar sallah) bayan ranar Arfah. Allah Maɗaukakin Sarki ya canza mana da su daga idikan jahiliyya da ma duk wani idi ƙirƙirarre.

An karɓo daga Anas ɗan Malik (Allah ya yarda da shi)ya ce, Mutanen jahiliyya suna da kwana biyu a shekara da suke wasa a cikinsu, yayin da Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya zo Madinah, sai ya ce, “Kuna da kwana biyu da kuke wasa a cikinsu, kuma haƙiƙa Allah ya sauya musu da waɗanda suka fi su alheri, idin buɗa baki, da idin layya” (Nisa’i ne ya rawaito shi).

Ba ya halatta a yi tarayya da kafirai a cikin idinsu, saboda idi shi ne babbar alamar kowane addini ta fili, da tsarinsa. Allah Maɗaukakin Sarki ya ce, “Kada ka bi son zuciyarsu wajen barin abin da ya zo maka na gaskiya, kowanne daga cikinku mun sanya masa shari’arsa da tsarinsa” (Suratul Ma’ida aya ta 48).

Idi a musulunci ya haɗa wasu ibadu da bayyana farin ciki da cin abubuwa daɗaɗa na halal, saboda haka waɗannan kwanaki suka zama kwanakin farin ciki da na jin daɗi, da ci da sha. Ba ya halatta a haɗa idi da abin da ya saɓawa koyarwar musulunci. Misali kamar cakuɗuwar maza da mata, ko tozarta lokutan salloli, ko shan abin da aka haramta, ko wasa da abin da Allah ya haramta, ko jin abin da Allah ya haramta, ko wanin haka daga cikin abubuwan haramun.

Hukuncin Sallar Idi Biyu

Sallar idi nafila ce, kuma abar kwaɗayi ne a kan kowane musulmi ya himmatu wajen zuwa idi, saboda ana samun lada mai tarin yawa sosai gami da gafarar Allah (S.W.A). Sannan kuma Manzon Allah (Sallallahu alaihi wasallam) ya yi umarni da maza da mata su fita zuwa sallar idi, sannan kuma a sadar da zumunta gami da rarraba abinci da abin sha ga mabuƙata.

Yadda Ake Sallar Idi Biyu

Sallar idi raka’a biyu ce, ba a kiran sallah, ba a yin iƙama, ana bayyana karatu a cikinsu, ga yadda ake yin su :

1. Raka’ar farko zai yi kabbara bakwai, bayan ya yi kabbarar harama, sai ya yi addu’ar buɗe sallah, kafin ya fara karatu. Amma a mazahabar Imamu Malik bin Anas, an ware wasu surori, wanda ake buƙata ya karanta a raka’a ta farko kamar Suratul A’ala, ko Suratul Ƙamar.

2. Idan ya kammala raka’a ta farko, to a raka’a ta biyu, da zarar ya miƙe tsaye, zai yi kabbarta sau biyar ne, sai ya karanta Fatiha da wata surar. Ita ma a raka’a ta biyu a mazahabar Imamu Malik bin Anas an ware wasu surori da ake buƙatar a karanta su; Suratul Ghashiyati ko Suratul Kahfi, ko Suratul Shamsi da sauransu.

Saboda haka, idan mutum ya duba da kyau, zai ga an yi kabbarori guda goma sha uku, duk da kabbarar harama. Sannan ita sallar idi, ba a yi mata nafila, saboda ita ma nafila ce. Haka kuma sallar idi sai an gama ta tsaf, sannan liman zai ta shi ya yi huɗuba, wanda sauraron huɗuban liman, Allah yana cewa da Mala’iku “Ku shaida dukkanin wanda ya tsaye a wannan wajen, na gafarta masa dukkanin zunubansa”.

Wurin Da Ake Sallar Idi Biyu

A sunna dai, shi ne a yi sallar idi a filin sallah, ba a cikin  masallaci ba, wato ita sallar idi ba a so a yi ta a inda yake da rufi, a fili fayau ake buƙatar a yi ta, amma idan  akwai buƙatar haka, wato ruwan sama ya cike inda za a yi sallar, ko kuma ruwan sama ya hana a yi sallar, ko sanyi ya tsananta, ko dai wani abu wanda shari’a ta amince da shi, sai ayi ta kawai a cikin masallacin Juma’a.

Abubuwan Da Ake So A Idi

1. Maza su yi ado da kyawawan kayansu, mata kuwa su fita sallah ba tare da ado da turare ba.

2. Mutane su fito masallaci da wuri.

3. Canza hanyar tafiya, wato idan mutum ya bi ta wata hanya a lokacin da zai tafi masallaci, to idan zai dawo sai ya canza wata hanyar.

4. Yawaita kabbara tun daga gida har zuwa masallacin.

5. Cin dabino kafin a yi sallar idi ƙarama, da kuma cin dabino bayan an yi sallar idi babba (dabino guda uku ko biyar ko bakwai).

6. An so a jinkirta sallar idi ƙarama, don musulmi ya samu damar bayar da zakkar fidda kai, ga waɗanda ba su gama bayarwa ba.

Hukunce-hukuncen Idi

1. An karhanta sallar nafila kafin sallar idi da bayanta, sai dai in a masallaci za a yi ta, to sai a yi gaisuwar masallaci idan an shiga.

2. Sunna ne idan sallar idi ta wuce, ko wani ɓangarenta ya kubce wa mutum, ya rama ta kamar yadda take, ya sallace ta raka’a biyu da kabbarorinta, haka ma abin da ya rasa daga cikinta ya rama shi kamar yadda take.

3. Allah Maɗaukakin Sarki ya shara’antawa bayinSa, a ƙarshen Ramadan su yi masa kabbara, Allah ya ce, “Don ku cika adadin kwanakin (azumi), kuma don ku yi wa Allah kabbara a kan abin da ya shiryar da ku”. (Suratul Baƙara yaya 185). Ma’anar ku yi wa Allah kabbara shi ne, ku girmama shi a cikin zukatanku da harsunanku.

Lafazin kabbarar shi ne : “Allahu Akbarul Lahu Akbar, La’ilaha Illal Lahu, Wal Lahu Akbar, Allahu Akbar, Walillahil Hamdu”.

4. Sunna ne maza su ɗaga muryarsu da mata kuwa za su ɓoye ta (ƙasa-ƙasa), a lokacin da suke yi waɗancan kabbarorin.

5. Za a dinga yin waɗancan kabbarorin ne tun daga lokacin da aka ce an ga watan Shauwal (gama azumi) har zuwa lokacin da liman zai shigo masallaci, don yin sallar idi ƙarama, amma kuma idan a sallar idi babba ne, to mutum zai wuce da yin waɗancan kabbarorin ne har zuwa rana ta ukun bayan sallar idi, saboda ana so mutum ya yi waɗancan kabbarorin a gurbin kowace sallah ta ranar idi babba, wanda zai fara tun daga sallar azahar ɗin ranar har zuwa asubahin rana ta uku ga sallah, wanda idan mutum ya lissafa da kyau, zai ga an samu salloli goma sha biyar ke nan.

Abin Da Ya Kamata Musulmi Ya Yi Ranar Idi

1. Samun sallar asubar ranar Idi.

2. Wankan zuwa Idi.

3. Ba da zakkar fidda-kai ga mabuƙata.

4. Cin abinci kafin tafiya masallaci (ga ƙaramar sallah, babba kuma sai an dawo).

5. Sanya tufafi masu kyau.

6. Takawa zuwa masallaci.

7. Zikiri yayin tafiya.

8. Ba a sallar nafila a filin idi.

9. Sauraron huɗuba bayan sallar idi.

10. Gaisawa da juna bayan sallah.

11. Sauya hanyar tafiya wajen dawowa.

12. Yara da mata da tsoffi duka na zuwa idi.

13. Mata masu haila za su iya zuwa sallah, amma za su tsaya a gefen guda na masallaci.

14. Ana son musulmi su yi wa junansu murnar idi.

15. Ana son bayyana farin ciki da idi, da yi wa`yan uwa da masoya da makusanta murna.

16. Idi wata dama ce da ya wajaba a ribace ta, don sada zumuncin da aka yanke, da sulhuntawa a tsakanin masu husuma.

17. Ba shara’anta ziyarar maƙabarta ba a ranar idi, don hakan ya saɓawa farin cikin da annushuwa cikin idi.

18. An shara’anta yalwatawa iyali da tufafi da abinci da kayan cin daɗi, waɗanda Allah ya halatta, a ranar idi, saboda idi kwanaki ne na farin ciki da annushuwa.

Domin karanta Addu’ar Daren Lailatul Ƙadri danna nan

Edita@rumasau-kallamu

labarin da ya wuceAddu’ar Buɗe Sallah 2
Labarin na GabaSumbatar Mace Ga Me Azumi

SHARHI ƊAYA