Saiƙo Ko Sanƙo (Baldness)

0
33

Saiƙo inji sakkwatawa, ko sanƙo inji zage-zagi da katsinawa, shi ne ake kira “alopecia” a likitance. A turance kuwa ana kiransa “baldness” ko “bald headedness”. Saiƙo yanayi ne wanda yake sanya zubewar wani ɓangare na gashi (partial loss of hair) ko kuma zubewar dukkan gashi (complete loss of hair) a saman kai (scalp) ko sauran sassan jiki.

A likitance ba a ɗaukar saiƙo a matsayin wata cuta, sai dai ana ganinsa a matsayin yanayin da abubuwa masu yawa suke iya haddasawa. Mafi yawan saiƙon da yake samun namiji ko mace ana kiransa “androgenetic alopecia”, wanda yake faruwa saboda mutum ya yi gado daga iyayensa da kakanninsa.

Wani lokacin kuma saiƙo yana faruwa ne sakamakon rashin daidaiton zubar ruwan sinadarai (hormonal imbalance), ko nisan shekaru (ageing), ko rashin lafiya ta dogon lokaci (chronic illnesses), ko damuwa (stress), ko rashin cin abinci mai gina jiki (nutritional deficiencies), ko laulayin magunguna (medication side effects), ko matsalolin garkuwar jikin (autoimmune disorders), ko salon gyaran gashin kai (hairstyles), ko amfani da mayukan gyaran gashi (hair treatment creams), da sauransu.

Saiƙo yana aukuwa ne idan ƙofofin gashi (hair follicles) suka matse, wanda haka zai sanya gashi ya riƙa fitowa da kyar, har daga ƙarshe ya daina fitowa gaba ɗaya.

SASSAN JIKI DA SAIƘO YAKE KAMAWA (BODY PARTS AFFECTED BY BALDNESS)

Anfi samun saiƙo a kai (scalp) daidai saman goshi, ko tsakiyar kai, ko keya. Amma wani lokacin saiƙo yakan kama wasu sassan jiki daban kamar gira (eye brows), da gashin ido (eye lashes), da gashin gemu (beard), da gashin baki (moustache), da gashin hammata (armpit hair), da gashin mara (public hair). Idan mutum ya ga sassan jikinsa da na lissafa ba su yin gashi, to, akwai yiwuwar cewa saiƙo ne ya kama su.

RABE-RABEN SAIƘO (CLASSIFICATION OF BALDNESS)

Saiƙo ya rabu gida uku kamar haka:

1. Saiƙon da yake aukuwa ga maza (androgenetic alopecia): wannan shi ne saiƙon da aka fi sani. Alamarsa ita ce rashin gashi mai yawa ko kuma rashin gashi kwata-kwata a kai ko wani ɓangaren kai.

2. Saiƙo ga mata (androgenetic alopecia): sunansa ɗaya da na maza a likitance. Bambancinsa da na maza shi ne gaba ɗaya gashin yake zubewa, ba tare da farawa daga goshi ba (without receding hairline).

3. Saiƙo wanda yake sanya gashin kai ya yi cibiri-cibiri (alopecia areata): a wannan saiƙon, gashin kai zai yi dabbare-dabbare. Ma’ana, wani wurin akwai wani wurin babu. Matsalolin garkuwar jiki ne suke haddasa shi (autoimmune disorders).

MUTANEN DA SAIƘO YAKE KAMAWA (PERSONS AFFECTED BY BALDNESS)

Saiƙo yana aukuwa ga kowane irin mutum, mace ko namiji, yaro ko babba. Amma an fi ganinsa a jikin mutanen da suka kai shekarun balaga ko shekarun tsufa.

KARIYA DAGA SAIƘO (BALDNESS PREVENTION)

Mawuyaci ne mutum ya iya ɗaukar wani matakin da zai hana shi samun saiƙo, domin alaƙarsa da gado da kuma sinadaran jiki. Amma ana kyautata zaton cin abinci mai gina jiki tare da kaucewa yawan yin amfani da chemicals a gashin kai za su taimaka wajen rage hatsarin samun saiƙo.

MAGANI (TREATMENT)

Idan mutum ya samu saiƙo, to, sai ya tafi asibiti domin ganin likitan fata. Likitan zai binciki mutumin domin gane abinda ya haddasa samun saiƙon. Daga nan zai ɗora shi a kan magani bisa la’akari da abinda ya samar da saiƙon.

Magungunan da akan yi amfani da su wajen magance saiƙo sun haɗa da minoxidil da finasteride. Sa’annan akan yi amfani da hasken na’urar computer (lazer treatment), ko dashen gashi (hair transplant). Idan kuwa ba a yi nasara ba, to, sai mutum ya riƙa yin amfani da hular gashin roba (wig) domin ɓoye saiƙonsa.

Domin karanta Cututtukan Haƙori danna nan
Edita:@rumasau-kallamu

labarin da ya wuceMatasa
Labarin na GabaCikin Molo (Molar Pregnancy)