Rubutacciyar Fassarar Huɗubar Idin Ƙaramar Sallah (Eid Kabir) Daga Masallaci mai Alfarma

0
34

Aminu Bashir

Mai Huɗuba: Sheikh Dr Abdurrahman bn Abdur’aziz Sudais

Mai Fassara: Dr Abdulkareem Tahir Abdullahi

Transcribe: Aminu Bashir

Shugaban Shashi: Dr Abdurrahman Muhammad Sani Yakubu

Huɗuba ta farko:

Dukkan yabo ya tabbata ga Allah, muna gode Maka – ya Ubangijina – kuma muna neman taimakonKa da gafararKa, muna tuba gare Ka, kuma muna yaba Maka da dukkan alheri.

Allahu Akbar, Allahu Akbar, Allahu Akbar, Allahu Akbar, Allahu Akbar, Allahu Akbar, Allahu Akbar, Allahu Akbar Kabiran, walhamdu lillahi kasiran, wa subhanallahi bukratan wa asilan.

Allah Shi ne Mafi girma, kuma dukkan yabo mai daɗin furtawa da kyawu naSa ne, Allah Shi ne Mafi girmam muddin zukatan masu kaɗaitawa za su ambace Shi kuma su Masa tasbihi mai tsawo.

Ina shaidawa lallai babu abin bauta bisa cancanta sai Allah, Shi kaɗai ba Shi da abokin tarayya, Ya shar’anta mana lokuta masu daraja da bukukuwan idi, don tabbatar da amfani ga bayi a duniya da lahira, kuma ina shaidawa lallai Annabinmu Muhammadu bawan Allah ne kuma ManzonSa, mafi alherin bayi kuma mafi darajan masu bauta, Allah Ya masa salati, shi da Alayensa, da Sahabbansa, da Tabi’ai, da waɗanda suka bi bayansu da kyautatawa, kuma Ya masa sallama mai yawa har zuwa ranar sakamako.

Bayan haka:

Ku kiyaye dokokin Allah – ya ku bayin Allah – in kun kasance masu biɗan maƙurar ɗaukaka, da ƙololuwar rahamar shiriya, ((Kuma duk wanda ya bi Allah da ManzonSa kuma yake tsoron Allah kuma yake kiyaye dokokinSa, to, waɗannan su ne masu rabauta)).

Duk wanda ya kiyaye dokokin Allah, to, zai sanya tsananinsa ya koma sauƙi, kuma Allah Zai girmama ladansa saboda taƙawa.

Ya ku taron Musulmi na gabashin duniya da yammacinta: Shin kun san wane yini ne wannan? Shin kun san wane lokaci ne wannan? Lallai wannan lokaci ne na bikin idin ƙaramar Salla mai albarka, ina taya ku murnar idi mai albarka, kuma ina roƙon Allah Ya karɓa mana kyawawan ayyukan mu tare da ku, Ya kuma maimaita mana da shugabanninmu da ƙasashenmu da al’ummar Musulunci da alheri da yalwa da albarka.

Ga shi Allah Ya muku ni’ima da riskar wannan yini mai daɗi, don haka ku yi farin ciki da idinku kuma ku yi murna, domin farin ciki da idi sunnar Musulmi ne, kuma alama ne daga cikin alamomin Addini, an shar’anta bayyana farin ciki da murna a bikin idi, ba bayyana baƙin ciki da damuwa ba, don haka ku yaɗa farin ciki, kuma ku bayyana murmushi, ku yaɗa jindaɗi da murna, ku kwantar da hankali, kuma ku kiyaye ƙaunar juna, don tutocin farin ciki su kaɗa a gidaje da unguwanni, da kasuwanni da hanyoyi, kuma ku kawar da dundumin baƙin ciki, ku hutar da jikkuna.

Kuma duk wanda ya hango jindaɗi na haƙiƙa da fata da albishir da farin ciki na har abada a furuci da magana da kyakkyawar hangensa, to, wani mashaya da ya fi ruwan girgije garɗi kuma haskenshi ya fi tataccen zuma ƙyalli zai bayyana gare shi, kuma wannan mashaya ba komai ba ne face wasu gwalagwalai masu ƙyalli, daga tarihin mai kyakkyawar ɗabi’u da siffofi, mai tarin albarka, mafi alherin halittu, Annabinmu Muhammadu tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, mafi darajan salati da mafi tsarkakar jinjina su tabbata a gare shi, wanda ya zo mana da shiriya mai haske da ƙyalli.

Ya zo a Bukhari da Muslim, daga Uwar Muminai A’isha Allah Ya ƙara mata yarda cewa, lallai Abubakar ya shiga wajenta, alhali a tare da ita akwai kuyangu guda biyu suna rera waƙa kuma suna buga ganga, a wannan lokacin Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana lulluɓe cikin tufafinsa, sai Abubakar ya musu tsawa, sai Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya yaye fuskarsa, sai ya ce: (Ka ƙyale su ya Abubakar, saboda waɗannan kwanakin idi ne).

Kuma an rawaito daga Uwar Muminai A’isha Allah Ya ƙara mata yarda ta ce: (Wallahi haƙiƙa na ga Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana tsayuwa a kan ƙofar ɗakina, alhali Habashawa suna wasa da masunsu a Masallacin Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yana suturce ni da tufafinsa don na kalli wasansu, sannan sai ya tsaya don ni har sai na kai lokacin da ni da kaina zan tafi).

Ya ku Muminai!

A wannan yini na farinciki mai albarka, ku yalwata wa kawunanku da ‘ya’yanku, kuma ku shigar da farin ciki ga iyalanku da maƙoftanku da makusantanku, haƙiƙa Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: (Yana daga mafi falalar aiki, shigar da farin ciki ga Mumini). Baihaƙi ne ya rawaito shi.

Ku tsarkake zukatanku daga ƙeta da ƙullata da hassada da ƙiyayya da tsana da gaba, kuma ku karɓi uzuri, ku gyara kuskure, kuma kada ku juya wa juna baya, kada ku yi gaba, kada ku yi hassada, ku zama bayin Allah ‘yan’uwan juna.

Idinmu mu Musulmi, idin murna da farin ciki da sada zumunci ne, ba idin yanke zumunci da ƙullata ba, ku sada zumuntanku, ku ziyarci juna, kuma ku kira wanda yake nesa da ku ta hanyar kafafen sada zumunta na zamani, wannan rana ce ta zumunci da ziyara da tausayi da sasanta juna da kau da kai, ku yafe wa wanda ya yi tuntuɓe ko kuskure, ku yi afuwa ga wanda ya yi zalunci kuma ya munana muku.

Wannan rana ce ta ‘yan’uwantaka da haɗin kai, da curewa da dunƙulewa da tausayi, kuma waɗannan su ne alamomi da Musulunci ya ba wa muhimmanci matuƙar gaske sai ya ƙarfafa su, ya tabbatar da su kuma ya kafa su, ashe ba su ne ginshiƙan ƙarfi da tabbatawu ba bayan tauhidi da saboda shi ne aka aiko Manzanni kuma aka saukar da littaffafai, Allah Maɗaukaki ya ce: ((Ban halicci aljani da mutum ba sai don su bauta mini)).

Kuma Maɗaukakin Sarki ya ce: ((Ku yi riƙo da igiyar Allah gabaɗaya, kada kuma ku rarrab. Kuma ku tuna ni’imar Allah da Ya yi muku yayin da kuka zamo abokan gaban juna sai Ya haɗa tsakanin zukatanku, sai kuka zamo ‘yan’uwan juna a sakamakon ni’imarsa)). Haka kuma ya kasance ne saboda abin da yake samuwa ta dalilin haɗin kai na so da ƙauna, da tunɓuke ƙeta da ƙullata.

Allahu Akbar, Allahu Akbar, la’laha illallah, wallahu akbar, Allahu Akbar, wa lillahilhamd.

Ya ku Musulmi! Wannan idin Allah Ya shar’anta mana shi ne bayan ibadar azumi don mu yi farin ciki da shi bayan cikar azumi da doguwar tsayuwar dare, kuma haƙiƙa kun ba da zakkar fidda kai kuna masu son haka a zukatanku, ita kuma tsarkaka ce ga mai azumi daga maganar wargi da batsa, kuma abinci ne ga miskinai, Allah Maɗaukaki Ya ce: ((Don ku cika adadin (kwanakin Ramadan), kuma domin ku girmama Allah bisa ga shiryar da ku da Ya yi, don ku yi godiya)).

Kuma daga cikin shiriyarsa tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi akwai cewa lallai yana sanya mafi kyawun tufafi da yake da shi ranar idi, kuma ya kasance tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana fita a idin ƙaramar Salla da na layya yana mai ɗaga sautinsa da hailala da kabbara, kuma Ibnu Umar Allah Ya ƙara masa yarda ya kasance idan ya wayi gari ranar idi yana bayyana kabbara har sai ya iso filin Salla kuma liman ya zo.

Allahu Akbar, Allahu Akbar, Allahu Akbar, la’laha illallah, Allahu akbar, Allahu Akbar, wa lillahilhamd.

Kuma an rawaito daga Ummu Aɗɗiya Allah Ya ƙara mata yarda ta ce: (Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya umurce mu da mu fitar da zawarawa da ‘yan mata, da masu haila ranar idin ƙaramar Salla da ranar Sallar layya, su halarci alheri da addu’ar Musulmi). Ahmad ne ya rawaito shi a Musnadinsa.

Allahu Akbar Kabiran!

Wannan shi ne Addininmu tsarkakakke, kuma wannan ita ce shari’armu mai haske, shari’ar sauƙi da rahama da tsakatsakiya da daidaito Allah Ya ce: ((Kuma kamar haka ne Muka sanya ku al’umma tsakatsaki)), lallai ita ce haske mai ƙyalli da haskakawa, Ubangijin talikai Ya yi gaskiya da ya ce: ((Ba mu aiko ka ba face don ka zama rahama ga talikai)).

Ya ku ‘yan’uwa Musulmi!

Taya juna murnar idi yana ƙara ƙauna, da ƙarfafa soyayya, kuma an shar’anta a riƙa cewa a lokacin taya murna na idi: (Taƙabbalallahu minna wa minkum). An rawaito daga Wasilatu ɗan Asƙa’ ya ce: Na haɗu da Manzon Allah tsirda da amincin Allah su tabbata a gare shi a wata rana ta idi, sai na ce: (Taƙabbalallahu minna wa minka), sai ya ce: (Na’am, Taƙabbalallahu minni wa minka). Baihaƙi ne ya rawaito shi.

Ya ku al’umma masu imani!

Musulunci Addini ne na yalwa da yafiya da sassauci da sauƙi, da fahimtar juna da rayuwa tare da tattaunawa da ɗan’adamtaka, saboda haka ne hujjarsa ta bayyana, matsayinsa ya haskaka a cikin talikai, saboda ya ƙunshi maƙuran sassauci da sauƙi, da nisantar wahalarwa da tsanantawa, don haka, ku bayyana hakan ta hanyar furuci da aiki- Allah Ya kiyaye ku -, ku zama masu kira na gaskiya ta hanyar kyakkyawan furuci ((Kuma ku faɗa wa mutane magana mai kyau)), da aiki nagari, ku yaɗa fata nagari da daddaɗar kalma don koyi da Manzonku mai girma.

Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance yana son kyakkyawan fata da daddaɗan zance, an rawaito daga Anas Allah Ya ƙara masa yarda ya ce: Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: (Alfa’alu yana birge ni), suka ce: Mene ne Fa’alu ya Manzon Allah? Ya ce: (Daddaɗar kalma). Bukhari da Muslim ne suka rawaito.

Kuma Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance idan zai aiki wani sashe daga cikin Sahabbansa tare wani al’amari yana musu wasici da faɗinsa: (Ku yi albishir kada ku kori mutane, kuma yi sassauci kada ku tsananta). Muslim ne ya rawaito.

Kuma an rawaito daga Ubayyu ɗan Ka’ab Allah Ya ƙara masa yarda ya ce: Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: (Ka yi albishir ga wannan al’umma da ɗaukaka da matsayi da nasara da tabbatuwa a bayan ƙasa). Imamu Ahmad ne ya rawaito shi a Musnadinsa da isnadi ingantacce.

Ya ku al’ummar Musulmi!

Kada ku guji ayyukan ɗa’a bayan watan Ramadana, ku riƙe karsashinku na Ramadana har zuwa bayansa, kuma ku raba kawunanku da kasala da rauni da nawa, ku yi riƙo da sabuban rabauta da tsira, na tawakkali da himma da ƙoƙari, saboda manyan burace-burace ba a samun su da nawa, to dama ta ya ya mai nauyin jiki ƙasƙantacce zai samu maɗaukakan darajoji!

Kuma lallai tabbatuwa a kan ayyukan ɗa’a da taƙawa yana daga alamomin karɓar aiki, Imamu Aliyu ɗan Abu Ɗalib Allah Ya ƙara masa yarda yana cewa: “Ku zama masu ba da muhimmanci ga karɓar aiki sama da ba da muhimmanci ga yin aiki”.

Kuma haƙiƙa Imamu Muslim ya rawaito a Sahihinsa cewa lallai Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: (Duk wanda ya azumci watan Ramadana, sannan ya bi bayanshi da azumin kwanaki shida na watan Shawwal, to, zai samu lada kamar wanda ya azumci shekara).

Domin karanta Yadda Ake Yin Umara Dalla-dalla danna nan

Don haka, ku kwaɗaitu wurin azumtarsu, kuma ku yi wasici wa juna da hakan, ku sadar da aikin ɗa’a da aikin ɗa’a, za ku kasance daga cikin karɓaɓɓu da izinin Allah.

Allahu Akbar, Allahu Akbar, Allahu Akbar, la’ilaha illahu, Allahu Akbar, Allahu Akbar, wa lillahil hamd.

Ya ku ‘yan’uwa mata masu daraja! Matsayinku a cikin addinin Musulunci kamar lu’ulu’u ne killatacce, ko kayan alatu mai daraja, kuma kun fi ma lu’ulu’u tsada, ku ɗabi’antu da kunya gwargwadon iyawarku, kuma ku yi riƙo da ɗabi’ar kamun kai da saka hijabi da rufe jiki, kuma ku kame ganinku, ku riƙa sadaka, ku yawaita istighfari, ku dena butulce wa ni’ima, ku kasance mafiya alherin mataimaka ga mazajenku a kan ayyukan ɗa’a, ku ƙara ƙaimi wurin tarbiyyantar da ‘ya’yanku ababen ƙaunarku, ku kange su daga fitintinu, domin su fuskanci kalubale da sauye-sauyen rayuwa da imani mai ƙarfi da azama tabbatatta.

Allahu Akbar, Allahu Akbar, Allahu Akbar, la ilaha illallah, Allahu Akbar, Allahu Akbar, Allahu Akbar, Wa lillahil’hamd, Allahu Akbar kabira, Wa-lhamdulillahi kathira, Wa subhanallahi bukratan wa asila.

Allah Ya albarkace mu da Alkur’ani da Sunna, Ya amfanar da mu da abin da ke cikinsu na ayoyi da hikima, ina faɗin wannan magana tawa, kuma ina neman gafarar Allah gare mu da dukkan Musulmi daga dukkan kuskure da saɓo, saboda haka, ku nemi gafararSa kuma ku tuba zuwa gare Shi, lallai Shi Mai yawan karɓar tuba ne.

Huɗuba ta biyu:

Allahu Akbar, Allahu Akbar, Allahu Akbar, Allahu Akbar, Allahu Akbar, Allahu Akbar, Allahu Akbar, La ilaha illallah, wallahu Akbar, wa lillahil’hamd.

Dukkan yabo ya tabbata ga Allah, Ya kwararo mana ni’imomi masu yawa kuma masu girma, ina shaidawa lallai babu abin bauta bisa cancanta sai Allah, Shi kaɗai ba Shi da abokin tarayya, Ya tsarkaka da daraja da ɗaukaka, kuma ina shaidawa lallai Annabinmu Muhammadu Bawan Allah ne kuma ManzonSa, wanda aka zaɓe shi a cikin talikai da manzanci da matsayi.

Ya Allah Ka yi daɗin tsira ga Annabinmu kuma masoyinmu abin koyinmu Muhammadu ɗan Abdullahi, da Alayensa wanda suka kai maƙura wurin ƙaunarsa, da Sahabbansa masu bin sunnarsa suna masu lizimtar ta da riƙo da ita, da Tabi’ai da waɗanda suka bi su da kyautatawa matuƙar rana da wata na bibiyar juna kuma suna nan.

Bayan haka:

Ku ji tsoron Allah ya ku bayin Allah! Ku yi riƙo gaba ɗayanku da Littafin Ubangijinku, da Sunnar Annabinku Muhammadu tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, domin mafi alherin shiriya ita ce shiriyar Annabi Muhammadu tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, kuma mafi sharrin al’amura su ne ƙirƙirarrunsu.

Ya ku al’ummar Musulmi! Lallai daga cikin alamomin shiriya, akwai lazimtar tabbatattun abubuwa na shari’a, da kyawawan ɗabi’u, da riƙo da haɗinkai da kasancewa tare da jama’ar Musulmi, da abin da hakan ke lizimtawa na ji da biyayya ga shuwagabanni, an karɓo daga Ibnu Umar Allah Ya ƙara musu yarda ya ce: Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: (Al’ummata ba za ta taɓa haɗuwa a kan ɓata ba, saboda haka, ku lizimci jama’a, domin taimakon Allah yana tare ne da jama’a). Tirmizi da Ɗabarani ne suka rawaito shi da isnadi mai kyau.

Lallai jama’a igiyar Allah ne ga mai addini saboda haka, ku yi riƙo da igiyar mai ƙarfi.

Sau Nawa ne Allah Yake tunkuɗe bala’i ta dalilin shugaba.

A cikin lamuran addini da na duniya don rahama daga gare shi.

Ba don shugabanci ba da ba a amintar mana da hanyoyi ba.

Kuma da masu ƙarfinmu sun danne masu rauni daga cikinmu.

Da kasancewa tare da jama’a da biyayya ga shugaba ne aminci da zaman lafiya ke tabbata, kuma ababen guda biyu, ni’imomi ne da babu ni’imar da ta kai su girma, kuma kyauta ne da falala da babu abu mai daraja kamar su.

Kuma haƙiƙa Allah Maɗaukakin Sarki Ya fifita ƙasa mai tsarki da ni’imar aminci da zaman lafiya, sai Ya ce tsarki ya tabbata a gare shi: (Ashe ba su ga cewa lallai Mu mun sanya garin Makka mai alfarma ya zamto mai aminci ba, alhali ana fauce mutane a garuruwan da ke kewayensu).

Saboda haka, wanzuwar zaman lafiya a ƙasa mai tsarki aƙida ce tabbatatta, tushenta na kafe cikin ƙasa, rassanta kuma su na sama, kuma hakan ya tabbata kuma ya ƙarfafu tun lokacin kafuwar wannan ƙasa har zuwa zamanin shugaban da ya haɗa sassan ƙasar, nagartaccen Sarki – Allah Ya kyautata makomarsa – cikin inuwa mai faɗi na tutar haɗinkai da ɗinkewa, da nesantar sharrin rarrabuwa da saɓani.

Kuma a wannan zamani na bunƙasawa da hangen nesa da kyakkyawan tsari na shugabanci da cigaba da ginawa da rayawa da haɓɓakawa da daɗin rayuwa da kyawunta, da cin ma manufofinta ta hannun matasanta maza da mata, da tabbatar da kishin ƙasrsu da jinginuwarsu gare ta, wannan ƙasa tamu maɗaukakiya tana da daraja ta ɓangaren abin da ya shafi haɗinkan mutanen cikinta, da sauƙin rayuwa da riƙo da al’adu da tafiya kafaɗa da kafaɗa da zamani da cigaba da bunƙasa, kuma dama – da falalar Allah – ita ce ƙasar da take da girman tasiri ga Musulmi da Larabawa da duniya, da mahimmancin wurin da take da girman tarihinsa, da matsayinta mai girma a idon duniya, ga Allah kaɗai godiya da falala suka tabbata, Allah Ya ƙara mata haɗinkai da dunƙulewa da wadata, kuma Ya ƙare mata aƙidarta da shugabancinta da amincinta lumanarta, lallai Shi Mai yawan kyauta ne Mai karamci.

Kuma bayan haka: Albishirinku ya ku waɗanda kuka yi azumi da tsayuwar dare, albishirinku ya ku waɗanda kuka yi Tahajjudi kuma kuka yi sadaka, haƙiƙa gajiya da wahala sun gushe, lada kuma ya tabbata in Allah Ya yarda, domin wannan rana ce ta kyaututtuka.

Kuma daga cikin falalar Allah ga ƙasarmu, akwai abin da Allah Ya ɗaukaka ta da shi na hidimar Masallatai biyu masu alfarma, da abin da Ya ni’imta wa masu Umra da maniyyata na samar musu da wani yanayi na imani mai girma, da manyan hidindimu masu ban-ƙaye, saboda haka, ga Allah kaɗai yabo da godiya suka tabbata, kuma Allah Ya saka wa Hadimin Masallatai biyu masu alfarma da magajinsa amintacce da mafi alherin sakamako kuma mafi cikarsa a kan ƙoƙari da suke yi na gabatar da ayyuka masu girma na hidima ga Masallatai biyu masu alfarma da maziyartarsu, da taimako cikin lamuran da suka shafi Musulunci da Musulmi, na gaba daga ciki, shi ne lamarin da ya shafi Falsɗinu da Masallacin ƙudus, da ƙoƙarin wajen samar da aminci da zaman lafiya a duniya.

Allah Ya karɓa mana kyawawan ayyuka, kuma Ya sa a kowace shekara ku cigaba da ni’imtuwa da alkhairai da jin daɗi, cikin aminci da lumana da natsuwa da kwanciyar hankali.

Wannan kena! Allah Ya muku rahama, Ku yi aiki da umarnin Ubangijinku da Yake sakanta muku da lada mai girma a kansa, da matsayi maɗaukaki, sai Allah Madaukaki Ya faɗi magana mai daraja: ((Lallai Allah da Mala’ikunSa suna salati ga Annabi, ya ku waɗanda kuka yi imani ku yi salati a gare shi da sallama mai yawa)).

Ya Allah Ka yi daɗin tsira ga Annabi Muhammadu, da Alayensa nagartattu tsarkaka, da Sahabbansa masu hasken fuska masu albarka, da Halifofinsa shirayayyu, Abubakar da Umar da Usman da Ali, da sauran Sahabbai baki ɗaya, da Tabi’ai da waɗanda suka bi su da kyautatawa har zuwa Ranar sakamako.

Ya Allah ya ma’abocin girma da ɗaukaka, Ka daidaiata tsakanin Musulmi, Ka azurta su da shiriya da tsoron Allah da kamewa da wadatar zuci, ya Allah Ka datar da su ga haɗin kai da ƙaunar juna, Ka nesanta su daga sharrori da laifuka don falalarKa, Ka shiryar da su hanyoyin tsira.

Ya Allah Ka datar da shugabanmu Hadimin Masallatai biyu masu alfarma ga ayyuka na ƙwarai da tsoron Allah, da aikin da Ka yarda da shi, kuma Ka yalwata masa tufafin waraka da lafiya, Ka datar da shi da magajinsa ga abin da yake ɗaukaka ne ga Musulunci da Musulmi, Ka azurta su da mashawarta nagari, waɗanda za su riƙa nuna musu alheri su riƙa kwaɗaitar da su a kan shi, ya Allah Ka game su da baiwarwaki masu kyawu, Ka ƙawata su da siffofin karamci, Ka kasance Mai taimako da agazawa da ƙarfafawa da ba da nasara a gare su cikin ayyukan alheri, Ka sanya su su zamto masu taimako ga Musulunci da Musulmi.

Ya Allah Ka wanzar da aminci da zaman lafiya a garuruwanmu, Ka sanya su su rabuta da alheri da albarkoki, su kuɓuta daga sharrori da masifu.

Ya Allah Ka datar da shugabannin Musulmi ga hukunci da shari’arKa, da bin Sunnar AnnabinKa Muhammadu tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, Ka shiryar da su bisa tafarkin kyawawan ayyuka da tsira.

Ya Allah Ka taimaki ‘yan’uwanmu masu rauni a kowane wuri.

Ya Allah Ka ceto Masallacin ƙudus daga ta’addancin ‘yan ta’adda, da yahudawa ‘yan share wuri zauna, ya Allah Ka sanya shi ya zamto mai ɗaukaka da buwaya har zuwa Ranar sakamako.

Ya Allah Ka taimaki ‘yan’uwanmu a ƙasar Falasɗinu, ya Allah Ka darkake maƙiyansu, Ka tarwatsa taronsu, Ka sanya su su zamto abin lura ga masu lura.

Ya Allah Ka zartar wa wannan ƙasa wani al’amari na shiriya da za a ɗaukaka masu yi maka ɗa’a da shi, a shiyar da masu saɓa maka da shi, a yi umurni da kyakkyawan aiki da shi, a yi hani daga mummunan aiki da shi, ya Ma ji roƙo.

Ya Allah Ka datar da jami’an tsaronmu, da masu dako a fagage da iyakokinmu.

((Ya Ubangijinmu Ka ba mu kyakkyawa a duniya, Ka ba mu kyakkyawa a lahira, kuma tsare mu daga azabar wuta)).

Ya Allah Ka sanya Idinmu ya zamto mai daɗi, rayuwarmu ta zamto mai yalwa, aikinmu ya zamto daidaitacce, kuma Ka maimaita mana shi cikin shekaru masu yawa, da zamuna masu tsawo, muna cikin alheri da lafiya da rayuwa mai daɗi, ya Allah Ka maimaita mana shi tare da shugabanninmu da ƙasarmu da Musulmi cikin alheri da jin daɗi da albarka, ya Mafi alherin Wanda ake roƙo, kuma Mafi ɗaukakar Wanda ake fata.

Ya Ubangijinmu Ka karɓa mana lallai Kai Mai ji ne kuma Masani.

Ka karɓi tubarmu, lallai Kai Mai yawan karɓar tuba ne kuma Mai jinƙai.

Ka gafarta mana da iyayenmu da dukkan Musulmi, rayayyu daga cikinsu da matattu, don tausayinKa ya Mafi tausayin masu tausayi.

Allahu Akbar, Allahu Akbar, Allahu Akbar, la ilaha illallah, Allahu Akbar, Allahu Akbar, Allahu Akbar, Wa lillahil’hamd.

Tsarki ya tabbata ga Ubangijinka, Ubangijin buwaya daga abin da suke siffantawa).

Aminci ya tabbata ga Manzanni. Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai.

Danna nan don karanta Addu’ar Fita Daga Masallaci

Edita@rumasau-kallamu

 

 

 

 

labarin da ya wuceLailatul Ƙadri
Labarin na GabaAddu’ar Buɗe Sallah 2