khairatu.shehu
Ahmad Tijjani Gandu
‘Yar Maye ‘yar maye,
‘Yar maye ya kamata ki bar shaye-shaye, Shaye-shaye, Ya kamata ki bar shaye-shaye.
Amshi
‘Yar uwa ki lazumci karamci kada ki sa ni na zub da hawaye,
Ta zamo, mai kayan maye mujiya a cikinsu ƙawaye.
Namiji
Ni kalar ki tana burge ni,
Kina da kyau a cikin mataye,
Nai zaton ki kina da mutunci,
Sai na gan ki kina shaye-shaye,
Ga shi ƙauna ta kuma kullu,
Ƙafa jikinmu zuwa hannaye,
Da ina murna na dace,
Ga shi yanzu ina ta hawaye.
Mace
Dakata ka ji labarina,
Na kasance ‘yar shaye-shaye.
Kuma iyayena sun nunan,
Tarbiyyarsu da kyan halaye.
Yau da gobe a kwana a tashi,
Saurayi ya kira ni kiranye.
Shi ya ce na raka shi wurin party,
Can na tadda dukan ‘yan maye.
Namiji
Na ji zancan yai mini muni,
Duk da dai na so ki a ɓoye.
Yanzu ne na fito in gaya maki,
‘Yar’uwa buɗe kunnaye.
Shi halin da kike kai yanzu,
Bai da kyau a cikin sunaye.
Shawara ce yau zan ba ki,
Ya kamata ki bar shaye-shaye.
Mace
Ni fa zancena a taƙaice,
Ba na so ka gaya wa ƙawaye.
In kana so mu yi soyayya,
Za mu yi amma fa a ɓoye.
Ga waya ta sai ka buga mini,
Za ka ganni ina nanaye,
Kar ka damu ka bi ni masoyi,
Kar ka ce in bar Shaye-shaye
Amshi
‘Yar Maye ‘yar maye,
‘Yar maye ya kamata ki bar shaye-shaye, Shaye-shaye, Ya kamata ki bar shaye-shaye.
Namiji
Hafsa ke na riƙa zan aura,
Taimake ni ki bar shaye-shaye.
Kuma ki tuba zuwa Allahu,
Yai maza shi yai mataye,
Hailala da Salati sannan,
Tarbiyya ki yowa iyaye.
Kuma ki kamu da istigifari,
Ba ƙawa da dukan ‘yan maye.
Mace
So da ƙauna ta kama ni,
Ɗan uwa mai kyan halaye.
Tarbiyyarka tana burge ni,
Kai daban da zubin wawaye.
Ko ina na yi sai a gaya min,
An gan ka kana ta hawaye.
Mai kake so in maka sahibi,
Ba ni son ka da zubda hawaye.
Na bi na ɗauka kuma ɗan uwa,
Karɓi wannan share hawaye.
Ga jikina har ya canja,
Nai daban a cikin mataye.
Da ana ta kira na Hafsat,
Yanzu na koma ‘yar maye.
Na shiga uku wayyo Allah,
Dan’uwa saitan halaye.
Namiji
Hafsa ɗan natsu kadda ki damu,
Rabbi zai yafe halaye,
Tun da dai kin daina babu ji,
Yau ido ya daina hawaye,
Godiya gun Sarkin Allah,
Shi ya gyara dukan halaye,
Mu yi zaman aure da mutunci,
Mun shigo hanyar angwaye.
Danna nan don karanta Illolin Shaye-Shaye
Wannan bayani an ciro shi ne daga littafin Mata Da Shaye-shayen Kayan Maye: Ina Mafita? Wanda Ado Ahmad Gidan Dabino MON ya wallafa.
Edita@rumasau-kallamu