Rahamar Ubangiji Ga Bayinsa

0
17

Yayin da Allah ubangiji ya halicci mutum ya yi nufin alheri da rabautar duniya da ni’imar lahira da aljanna gareshi amma wannan duk ba ya samuwa sai idan mutum ya yi amfani da hankalinsa da kuma abin da ya dace da ruhinsa da jikinsa, wannan kuwa yana buƙatar abin da zai ɗauke waɗannan buƙatu waɗanda ba wanda zai iya samar da dukkan wannan sai mahaliccin mutum ɗin da ya san shi, kuma ya san buƙatunsa.

Tun da Allah yana son rabauta ne ga mutum shi ya sa ya halicce shi, don haka ne sai ya samar masa da hanya kamila da zai bi domin samun rabauta ta hanyar wasu amintattun bayi nasa da suke ma’asumai daga dukkan kuskure da mantuwa kuma tsarkaka daga dukkan aibobi da zunubai waɗannan su ne annabawa da manzanni.

Don haka ne: Annabi shi mutum ne da Allah ya yi masa wahayi ya zaɓe shi a cikin mutane kuma sun kasu gida biyu: Annabi ɗan saƙo shi ne wanda aka aiko domin ya tseratar da mutane daga duhu zuwa haske daga ɓarna zuwa gaskiya daga camfi zuwa gaskiya daga jahilci zuwa ilmi. Annabi ba ɗan saƙo ba: shi ne wanda aka yi masa wahayi zuwa ga kansa kuma ba a umarce shi ya isar da saƙon ga mutane ba.

Yahudawa suna bin Annabi Musa (a.s) kiristoci kuma Annabi Isa (a.s) musulmi kuma Annabi Muhammad (s.a.w) da sauran annabawa duka. Sai dai musulunci ya shafe sauran addinai da suka rigaya, bai halatta ba ma’abotansu su wanzu a kansu, dole ne a kan kowa ne mutum ya bi koyarwar musulunci. Ubangiji yana cewa: “wanda ya yi riƙo da wani addini ba musulunci ba to ba za a karɓa daga gareshi ba, kuma shi a lahira yana daga cikin masu hasara”.

Don haka yahudanci da kiristanci ɓarna ne da aka shafe su, amma musulunci mai wanzuwa ne har zuwa ranar kiyama. Annabi Muhammad (s.a.w) shi ne ƙarshen annabawa kuma addininsa shi ne musulunci mai shafe duk wani addini kuma shari’arsa za ta wanzu har zuwa ranar ƙiyama kuma ita kaɗai ce shari’ar da za ta azurta mutum da tabbatar masa da burinsa da amincinsa har zuwa ƙarshen rayuwa duniya da lahira.

Kamar yadda shi kaɗai ne mutum abin koyi ga dukkan duniya baki ɗaya, dukkan mutanen duniya idan suna son alheri ga kawukansu to dole ne su bi tafarkinsa su yi koyi da kyawawan halayensa (s.a.w) da kuma sanin sashen tarihinsa da ba makawa mu kawo wasu daga siffofinsa (s.a.w): Shi ne Muhammad ɗan Abdullah (s.a.w) kuma mahaifiyarsa ita ce Aminatu ‘yar Wahab.

An haife shi a Makka ranar Litinin goma sha-biyu ga watan Rabi’ul awwal a shekarar giwa, a zamanin sarki mai adalci Kisra. (wato idan an kwatanta shi da ire-Irensa a cikin sarakunan wannan zamani). An aiko Annabi Muhammad (s.a.w) da saƙo yana ɗan shekara 40 yayin da Jibrilu (a.s) ya sauka gareshi daga wurin Allah (S.A.W) yana kogon Hira wanda yake dutse ne a Makka ya ce masa ka karanta kuma ya saukar masa da ayoyi biyar na surar Alaƙi.

Sai ya zo ya tsaya a kan dutsen Safa a masallaci mai alfarma na Makka a lokcin akwai jama’a masu yawa a wurin da ake taruwa ya isar da saƙon Allah na shiryar da mutane zuwa ga imani da shi yana cewa da su: “Ku ce babu abin bauta da gaskiya sai Allah kwa rabauta”. A lokacin tunda mutanen Makka mushirikai ne, kuma suna ganin maslaharsu ita ce shirka kuma suna tsoron maslaharsu sai suka riƙa yi masa isgili suna yi masa dariya suna cutar da shi.

Kuma duk sa’adda ya dage wajen shiryar da su sai su dage wajen cutar da shi har ya ce: “Ba a cutar da wani Annabi ba kamar yadda aka cutar da ni”. Yayin da takurawar mushirikai ta yi yawa sai ya yi hijira zuwa Madina wannan kuwa ita ce hijirar farko a tarihin Musulmi, yayin da suka yi yawa sai ƙarfinsu ya daɗu kuma suka samu koyarwa daga Manzon Allah da shari’arsa mai sauƙi mai hikima, da kuma misali na kyawawan halaye da mutumtaka da wayewa da cigaba a Madina har suka fi dukkan duniya da addini na sama da waɗanda ba na sama ba.

Kuma an samu yaƙoƙi masu yawa a Madina kuma dukkaninsu sun zama domin kare kai ne daga maƙiya mushirikai da yahudawa da kiristoci da suke kai hari kan musulmi, kuma Annabi a kowane lokaci yana zaɓar ɓangaren sulhu da zaman lafiya ne da rangwame, don haka ne ma adadin waɗanda ake kashewa daga ɓangarorin biyu ba su da yawa a dukkan yaƙoƙinsa tamanin da wani abu, wato; waɗanda aka kashe na musulmi da kafirai duka ba su kai sama da dubu ɗaya da ɗari huɗu ba.

Tun lokacin da aka aiko Annabi da saƙo har ya tafi daga duniya wahayi yana sauka gareshi kuma Jibrilu (a.s) shi ne ake aiko masa daga wajen Ubangiji (S.A.W) a hankali a hankali har littafin Kur’ani ya cika a cikin shekaru ashirin da uku. Manzo (s.a.w) ya kasance yana tsara wa musulmi duniyarsu da addininsu, yana sanar da su littafi da hikima kuma yana yi musu bayanin dokokin ibada da biyayya da mu’amala da zamantakewa da siyasa da tattalin arziki da sauransu.

Sai Allah ya saukar da ayar: “A yau ne na kammala muku addininku, na cika ni’imata gareku kuma na yardar muku da musulunci shi ne addini”. A taƙaice, ya tattara dukkan wata ɗabi’a mai kyau da girma da ɗaukaka da kuma ilimi da adalci da taƙawa da kuma iya tafiyar da al’amuran duniya da na lahira, waɗanda babu wani mahaluki da yake da irinsu.

Wannan shi ne annabin musulmi kuma wannan shi ne addinin musulunci, kuma addininsa shi ne mafificin addinai, littafinsa shi ne mafifcin littattafai domin shi: “Barna ba ta iya zo masa ta gabansa da ta bayansa, abin saukarwa ne daga mai hikima abin yabo”. Muhimmancin samuwar wannan annabi mai daraja wanda ya kasance hanyar shiriya ga dukkan talikai da suke bayan kasa.

Don karanta Gudunmawar Iyaye Wajen Gina Al’umma danna nan

Edita@rumasau-kallamu

labarin da ya wuceGudunmawar Iyaye Wajen Gina Al’umma
Labarin na GabaFitowar Haƙora Ga Yara, Faɗuwarsu, Da Sake Fitowarsu
Faruq Adamu
Sunana Faruq Adamu. Mu'assasin Gidauniyar Less-Privileged and Almajiri Initiative. Gidauniya Mai Rajin Taimakawa Mabukata, Dakuma Inganta Tare da Zamanantar da Tsarin Ilimi Na Almajirci a Nijeriya.