Physiology da Hausa Kashi na Shida: Hematology (Jini da Abun da ya Ƙunsa)

1
129

Jini wani nau’i ne na tissue wanda ake kira da connective tissue wato sashe mai sadarwa. Ma’ana yana haɗa gaɓoɓi daban-daban na jiki da juna.

Kamar ko wani irin sashe mai sadarwa, jini ma yana ɗauke da ƙwayoyin halittu da kuma wasu abubuwa a zagaye ko a tare da waɗannan ƙwayoyin halittu, wadda kowace ƙwayar halitta na da aikinta 

Kwayoyin halittun sun haɗa da:

Red blood cell: wato ƙwayar haliita mai launin ja, wadda ke ɗauke da jini mai sinadarin oksijin (oxygen) wato iska kan isar da su daga inda aka dauko su zuwa ga inda za a kai su haka a ɗauko ko iskar da ba a buƙata akai shi inda za a fitar da shi. 

White blood cells: Wato ƙwayar halitta ta jini mai launin fari wadda sun ƙunshi sojojin da suke yaƙi da ƙwayoyin cututtuka a cikin jikinmu. 

Platelets: Wato ƙwayoyin halluttun dake samar da jini a lokacin da aka samu zubar jini. 

Sauran abubuwan da jini ya ƙunsa su ake kira da Plasma, za ka iya cewa ruwan da jinin ya ƙunsa. Za a iya raba waɗannan ƙwayoyin halittun daga jikin plasma ta hanyar kaɗi wato centrifuge ta hanyar amfani da na’urar centrifuge machine wadda ke girgiza jinin da aka zuba a cikin kwalba domin rarraba waɗannan ƙwayoyin hallittu na jini da juna. 

Yana dakyau ka/ki karanta Physiology da Hausa kashi na hudu: Autonomous nervous system (Sashin Bada Umarni Da Amsa Saƙo)

Mene ne PCV ()
  • Shi ne kaso na ƙwayoyin halittun dake cikin jini.
  • Normal shi ne kashi 40 zuwa hamsin a maza,
  • Kaso 37 zuwa 45 a mata, ƙasa da haka shi ake kira da ANEMIYA (anaemia) wato ƙarancin jini a jiki, sama da haka kuma POLISAITEMIYA (Ploycythemia) wato jini yi yawa kenan.
  • Red blood cell ya fi yawa domin ya ƙunshi sama da kashi 90.
Shin mene ne amfanin Jini a Jikin Mutum
  1. Isar da iska da kuma sarrafaffen abinci zuwa inda ake buƙata.
  2. Daidaita zubar jini ta hanyar amfani da platelates wajen hana zubar jini.
  3. Hana daskarewar jini ta hanyar amfani da sinadaran tsinka jini wato.
  4. Garkuwar jiki ta hanyar amfani da WBC
  5. daidaita kaurin jini da hanyar amfani da ECF wato ruwan dake wajen ƙwayoyin halittu, ma’ana wanda ke cikin hanyoyin jini.
Ta yaya jini ke haɗuwa? 

Kafin haihuwa ana haɗa jini ne a Yolk Sac, a wata ukun farko wato wani abu kamar leda wanda ya zagaye jariri. 

Saifa da Hanta a wata ukun tsakiya, ɓargo wato  Bone marrow a watanni ukun ƙarshe. 

Abubuwa da ake buƙata domin sarrafa ko haɗa jini,  rashin waɗannan abubuwan yakan jawo matsala a haɗuwar jini, ma’ana za a ga matsala a inda ya kamata su yi aiki. 

  • Amino acid
  • Iron
  • Bitamin B12
  • Bitamin C
  • Bitamin E
  • Copper

Buƙatuwar waɗannan abubuwan na ƙaruwa a wasu yanayi wanda jiki ke buƙatar jini da yawa. Misali mace mai ciki ko mai shayarwa da kuma yaro a shekara ta farko a rayuwarsa. 

Misali VitB12 shi kesa girman ƙwayar halitta ta jini, ya zo a daidai, idan muka rasa shi, hakan zai sa girman ya ƙaru. 

Mene ne HEMOGLOBIN (Hg)

Wani abu ne wanda RBC ya ƙunsa, wanda shi kesa shi ya zama ja. Ya ƙunshi wasu ɗakuna wanda suke adana sinadaran iska, domin kai komo a cikin jini 

Akwai nau’ikansa iri-iri

  1. Akwai Hg F wanda shi ne na jarirai zuwa shekara A na manya kenan.
  2. Akwai HbA1C wato wanda ke ɗauke da sugar wanda, da shi ake amfani wajen gano illar da suga ya yi yawa jiki.
  3. Akwai Hb wanda suke da matsala wato na cuta kenan kamar Hg S wato na masu sikila kenan.

Ana ragargaje jini ne duk bayan kwana 120, sannan hakan na faruwa ne a cikin Saifa wato spleen

Idan an ragargaje shi, ana amfani da wani ɓirɓishin wajen haɗa wani jinin. Sauran ɓirɓishin kuma a haɗa BAYIL (wato) madaɗiya kenan, wadda ita ke taimakawa wajen narkar da kitsen da muka ci ta kuma ba wa bayimu ko fitsari nau’in ruwan ɗorawa. 

Domin karanta Physiology da Hausa kashi na biyu: Body Fluids (Ruwan Jiki) Ruwan dake jikin ɗan Adam Danna nan

labarin da ya wucePhysiology da Hausa Kashi na Biyar: Temperature and Metabolic Rate (Ɗumi Ko Yanayi Na Jiki)
Labarin na GabaPhysiology da Hausa Kashi na Bakwai: Respiratory System (Sashin Numfashi)
Dr. Yasir Aminu Ado
Ni dalibin likitanci ne nayi karatun likitanci a Kasar Sudan, Ina koyar da daliban jami'a masu tasowa ilimin karutun likitaci a saukake cikin harshen Hausa

SHARHI ƊAYA