Physiology da Hausa Kashi na Biyar: Temperature and Metabolic Rate (Ɗumi Ko Yanayi Na Jiki)

0
115

Ɗumin cikin jiki shi ake kira da core body temperature wato ɗumin tsakiyar jiki, ya yi daidai da 37 degree bisa ma’aunin Celsius (salshiyos). 

Ɗumin jikin fata na sauyawa ne saboda zafin dake waje ko sanyin dake waje. 

Kitse dake ƙarƙashin fatarmu na aiki a matsayin insulator wato abinda ke rage fitar zafi daga jiki. 

Yana adana core temperature, wato ɗumin cikin jiki kuma ya kare jiki daga sauyin yanayin wajen duniya, wato idan ana zafi ko sanyi. 

Idan ɗumin jiki ya ƙaru, jijiyoyi masu ɗauke da jini waɗanda suke ƙarƙashin fata na bubbuɗewa, hakan yana sa zafi ya fita ta hanyar gumi. 

Yana dakyau ka/ki karanta Physiology da Hausa kashi na hudu: Autonomous nervous system (Sashin Bada Umarni Da Amsa Saƙo)

Abubuwan dake sauya ɗumin jiki. 

Sassaita ɗumin jiki na ɗaya daga cikin aikin homeostasis wato masaitin jiki. Idan ɗumin jiki ya gaza saituwa abubuwa da dama kan rikice kamar:

  • Aikin enzymes wato sinadaran dake ragargaje wasu sinadaran idan aikinsu ya ƙare.
  • Metabolic reaction, wato duk wata kimiyya dake faruwa a cikin jiki.
  • Nervous system wato sashen kai da komo na saƙo mai nauyin lantarki daga ƙwaƙwalwa zuwa jiki.
  • Sashen zuciya da jijiyoyi.
  • Sashen numfashi.
Temperature Regulatory Center

Cibiyar sassaita ɗumin jiki na ƙwaƙwalwa: Akwai wani ɓangare a cikin ƙwaƙwalwa wanda ake kira da Hypothalamus a cikinsa ne ake da sashen sassaita zafi na jiki, wato idan ana buƙatar jiki ya ɗau ɗumi ko ya sanyaya wannan ɓangare shi ke so ma wannan aikin. 

Taya jikinmu ke rasa ɗumi? 
  1. Conduction idan jiki ya haɗu da wani jikin, ma’ana jikin da ya fi zafi zai ba wa jikin da bai kai shi zafi ba, har sai sun daidaita.
  2. Convection.
  3. Evaporation wato fitar gumi.
Taya jikinmu ke kara ɗumi? 
  1. Metabolism wato kimiyyar sarrafa abin da muka ci. 
  2. Motsi. 
  3. Cin abinci. 
  4. Yanayi na haɗuwa da wani jikin zafin gari ko zafin abinda ke kusa. 
Amshin da jiki ke yi a yanayin zafi
  1. Gumi
  2. Bubbuɗewar hanyoyin jini
  3. Daɗin numfashi
Amshin da jiki a yanayin sanyi
  1. Rashin gumi
  2. Tsukewar hanyoyin jini.
  3. Raguwar numfashi.
Bambancin ɗumin jiki a mutane daban-daban. 

Shekaru:

  • Jarirai sun fi yara.
  • Yara sun fi manya

A jarirai ya fi yawa, sabo da gaɓoɓi sun fara girma, sabo da haka aikin cikin jiki na ƙaruwa. 

Jinsi:

  • Maza sun fi mata, sabo da mata na da kitse kuma kitse insulator ne.
  • A lokacin da mace keda ciki, sinadarin progesterone na ƙara ɗumin jiki.
  • Da kuma ƙarin buƙatar sarrafa abincin da uwa ta samu, ɗa ya samu, na sa ɗumin jiki ya ƙaru
  • Shayarwa na sa ɗumin jiki ya ƙaru, Sabo da motsin sashen cikin mama domin haɗa ruwan mama da fitowarsa

Domin karanta Physiology da Hausa kashi na biyu: Body Fluids (Ruwan Jiki) Ruwan dake jikin ɗan Adam Danna nan

Circadian fluctuation

Wato sauyin yanayi daga safiya zuwa yamma. Da rana jiki ɗumi akan safiya, saboda zafin gari ko yanayin aiki, saboda ayyuka na motsi sun yi yawa da rana.

labarin da ya wucePhysiology da Hausa Kashi na Hudu: Autonomous nervous system (Sashin Bada Umarni Da Amsa Saƙo)
Labarin na GabaPhysiology da Hausa Kashi na Shida: Hematology (Jini da Abun da ya Ƙunsa)
Dr. Yasir Aminu Ado
Ni dalibin likitanci ne nayi karatun likitanci a Kasar Sudan, Ina koyar da daliban jami'a masu tasowa ilimin karutun likitaci a saukake cikin harshen Hausa