Ni’imar Da Allah Ya Yi Wa Mutane Ba Tare Da Sun Fahimta Ba

0
17

Akwai takaici ka ga mutum koyaushe abinda ya rasa shi ya fi damunsa, da shi yake ƙorafi a rayuwa. Ba nazari, babu tunani akan me Allah ya ba shi. Shin ko kun san yayin wankin ƙoɗa (hemodialysis) manya-manyan kawunan allura ne masu zafin gaske da sanya hawaye ƙwaya biyu ake turawa mutum a jijiyar jininsa, wani ma saboda rashin kyawun jijiyoyin sai dai a saita masa a jijiyar jinin wuyansa kai tsaye. 

Wannan wankin yana ɗaukar awoyi 4 ana yi mutum na kwance ba tare da ya motsa ba (immobilized) kafin a kammala, kuma mutum na buƙatar a maimaita hakan sau uku “3” dukkan satin duniya. Adadin sau goma sha biyu ’12’ a wata.

Ga wahala, ga shi duk yi ana buƙatar sai wani ya ba ka gudummawar jini, ga zaman jira, wasu tun safe amma saboda layi da sarƙaƙiyar kayan aikin sai biyun dare za su bar asibiti zuwa gida, kuma a haka jibi za su dawo. Ga yawan mantuwa da zazzaɓi, kasala, tashin zuciya, ciwon kai da sauran side effects saboda chemical ɗin tace jinin.

A ƙayyade dukkan wanki sai mutum ya biya kuɗin da suka kai dubu ashirin zuwa talatin N20,000 – N30,000. Wanda tunda sau uku ake a sati, wani ma sau huɗu za a yi, kuma huɗun shi ne ideal wanda jimilla zai kama dubu tamanin zuwa ɗari da ashirin duk satin duniya N80,000 – N120, 000.

A wata zai kama dubu ɗari uku da arba’in zuwa dubu ɗari hudu N340,000 – N400,000. Ko yaushe sai ka shafe awa 4 a kwance ba ka motsi har a gama, adadin awa 48 a wata ba tare da motsi ba, kuma zagaye ne ɗaya. 

AMMA ga kai wanda Allah ya yi masa baiwar lafiya, ya horewa ƙoda me lafiya kullum sai Allah ya wanke maka ita sau 36 free of charge, ba ka biya kowa ko sisi ba. Wanda in biya za ka yi dubu talatin sau 36 sai ka biya MILIYAN ƊAYA DA DUBU tamanin – N1,080,000 kullum na abinda Allah ke yi maka a wankin ƙoda kurum banda sauran ni’imomi.

Amma don ka tashi ka ji ka lafiya sharr kai ta wulaƙanci da rashin mutunci, kana jin kai wata tsiya ne, ko kuwa don ba ka da ko sisi kana ganin kamar Allah bai ƙaunarka… Kai bayin Allah yaushe za mu hankalta ne? 

Wannan tasa nake bamu shawarar yin check up, kana iya shekara 5 da ciwon ƙoda a hankali bai bayyana ba sai ta gama rikicewa baki ɗaya sannan ka fara jin alamomi, shi yasa ɗazu nace mu daure a je a yi awo ko da sau 1 ko 2 a shekara.

Wallahi duk gatanka ka kiyayi wannan ciwon domin sai an gaji da kai, masu ba ka jini ma in za ai wankin wataran sai an rasa, komi yawan danginka, balle a ce ba ka da kirki dama. Dama a duniya ba abu me ƙaranci irin jini, duk mutum 10 za ka samu 9 a ciki ba wai ya wadace su ba ne.

Kuma ba za a taɓa yi maka dashen ƙoda kai tsaye ba komai gatanka, dole sai ka biyo ta dialysis har ta jikinka ta ƙarasa lalacewa tukunna, domin inba haka ba ko an sa maka wata ba zama za tai ba. 

A rage son kuɗi a dinga check up. In ka yi wasa za ka ga wasa. Mu cigaba da godewa Allah a kodayaushe.

Danna nan don Karanta amfanin shan ruwa da safe kafin a ci komai

Edita; Rumasa’u Muhammad Kallamu

labarin da ya wuceLokacin Sanyi