Nazarin Yabo Daga Cikin Waƙoƙin Ala

0
36

Jigon yabo baduniyen jigo ne da ke yaba mashahuran mutane irin su; sarakuna da shugabanni da attajirai da ma’aikata da manyan malamai da masu ilimi ko ba na addini ba ne.

Irin waɗannan waƙoƙi sun fara samun tagomashi bayan zuwan Turawan Mulki, kuma sun haɓaka daga wajen 1950 zuwa yau. Waƙoƙin yabo suna taimakawa wajen ƙara wa waɗanda aka yi wa yabo gwuiwa don sun ƙara hoɓɓasa kan irin gudunmawar da suke bayarwa, domin yaba musu kamar ƙaimi ne wato ke nan an ga fa’ida da muhimmancin abin da suke yi.

Waƙoƙin kuma sukan zama kamar matashiya ga wasu daban domin; sukan sa wasu mutanen su ma su tashi tsaye su yi hoɓɓasan da su ma; wasu mawaƙan za su gani su ma su yi musu irin waɗannan waƙoƙin yabo don yaba musu (Abdulƙadir, 2014: xx).

Makaɗan baka na zamani sun yi waƙoƙin yabo da zuga daban-daban ga malaman Hausa musamman waɗanda suke jami’o’in ƙasar nan, inda waƙoƙin nasu suka fi karkata ga farfesoshi.

A wannan gaɓa, za a bayyana wasu muhallai da aka yi irin wannan yabo ga wasu manyan malaman Hausa; sannan a yi ƙoƙarin yin sharhin wannan yabo a taƙaice.

1. Salon Yabo ga Farfesa Ɗandatti Abdulƙadir

Farfesa Ɗandatti Abdulƙadir yana cikin jerin malamai, masana kuma manazarta harshen Hausa ‘yan Ƙasa na farko, masanin harshe da adabi da al’adun Hausa ne. Gudumawarsa ba ɓoyayyiya ba ce; musamman a fagen waƙa.

Makaɗi (Dr) Aminuddeen Ladan Abubakar (Alan Waƙa), ya yi wa Farfesa Ɗandatti waƙa, inda a cikin waƙar ya yabe shi a wasu baituka. Ga yabon da ya masa:

G/Waƙa : Ɗandatti Dattijo Abdulƙadir Furofesa,
Ka ji masu umarni da hani bisa sha’anin Allah,

Misali na I

Jagora : Ka ji masu umarni da hani bisa sha’anin Allah,
Ɗandatti Dattijo Abdulƙadir Furofesa,
Yau gida na malanta na taho za na yi wa ƙasida,
Yau jinin sarakai zan waƙe in rubuta nashida,
Bahari na taso in wa yabo masani na al’ada,
Bahari na fannonin adabi na gama da al’ada,
Ɗan Abdulƙadir Abdulƙadir ku min shaida,
Baitukan na yo wa ne atafa ko in ce farar tsada,
In zubo ɗiyan waƙa wane dirhami fagen tsada,
In yabon Furofesa Abdulƙadir a ƙasida,
Datti masu umarni da hani bisa sha’anin Allah.

Idan aka dubi matashiyar wannan waƙa, za a ga Makaɗin ya buɗe waƙarsa da wannan ɗiya; wanda hakan ɗaya ne daga cikin salon da Alan Waƙa ke bi yayin buɗe waƙoƙinsa musamman waɗanda suka shafi yabo. A wannan ɗiya, ya yi yabo ga Farfesa Ɗandatti ta amfani da kalmomi da dama. Misali, ya ambace shi da “masu umarni da hani”, a nan sai ya yabe shi da wata kyakkyawar sifa ta koyarwa. Sannan ya ambace shi da “masanin al’ada”, da “bahari a fannoni”, ma’ana mutum ne wanda yake da ilimi a ɓangarori da dama, inda har ma ya keɓanci wasu ɓangarori, wato masanin adabi da kuma al’ada.

Misali na II

Jagora : Gaisuwa gurin Allah arraziƙi mai azirtawa,
Mai aro na ilhama hikima kyauta gurin bawa,
Taimake ni min lamun na zo a gare ka don ƙwawa,
Zan yabon wurin jigon adabi mai hali na madalla.

A wannan ɗiya na farko, bayan ya yi gaisuwa ga Allah da roƙon lamuni. Sai ya bayyana zai yi yabo ga “jigon adabi”. Jigo a nan, na nufin ginshiƙi, wato ginshiƙin adabi. Shi kuwa adabi sanannen abu ne ga masu nazari da ɗalibai.

Misali na III

Jagora : In ana dara dangi ai fid da uwa ake gefe,
Yau uban iyaye ne na tashi yabo fa zan tsefe,
In ana batu na sani Abdulƙadir ku kai gefe,
Bahari fa kogi ne na masu iyo fa don Allah.

A wannan ɗiya na uku, ya yabe shi ta hanyar ambatarsa da ‘uban iyaye’ da ‘kogi’. Uban iyaye na nufin kakan jikoki amma a fuskar ilimi. Sannan ya ambace shi da kogi, wato iliminsa yalwatacce ne ta yadda ganin ƙarshensa akwai matuƙar wahala.

Misali na IV

Jagora : Rukunin dukkan daraja da ke ɗaga martabar bawa,
Ilimi da sarauta sai alatu halin bawa,
Ka haɗa mu’amilla yakana mai izo gurin bawa,
Babu wanda ɗan Audu bai taka ba ibadul Lah

A wannan ɗiya na huɗu kuwa, ya yabe shi ta hanyar amfani da rukunan da suke sanyawa a yabi mutum, wato ilimi ko sarauta ko dukiya ko kuma wata kyakkyawar mu’amala ga mutane. To a nan, sai yake ƙoƙarin nuna cewa duk waɗannan dalilai da suke sanyawa a yabi mutum, to fa Farfesa Ɗandatti ya haɗa su.

2. Yabo ga Farfesa Abdulƙadir Ɗangambo

Farfesa Abdulƙadir Ɗangambo yana cikin rukunin ‘yan Ƙasa rukuni na uku a fagen Hausa, fitaccen masani ne a ɓangaren adabi da al’adu, musamman yadda ya zama manazarci mai son ganin an haɗa hanyoyin nazarce-nazarce su tafi bai ɗaya. Farfesa ya taimaka wajen samar da hanyar fiɗar waƙa, sannan ya fassaro kalmomin nazari tare da ƙirƙiro wasu. (Gusau, 2008: 56).

(Dr.) Alan Waƙa ya gwangwaje Farfesa da waƙoƙi, cikin waƙoƙin an bibiyi guda ɗaya, sannan aka zaƙulo yabon da ya yi ga Farfesa.

G/Waƙa : Garkuwar Adabin Hausa sannu Farfesa,
Sannu Ɗangambo na taho in gaishe ka.

Misali na I

Jagora : Za ni hau sarari na yabo da baitukka,
: In yabanta gwani turmi ma-sha duka,
: Nemi Ɗangambo ka ji rairayar waƙa,
: Rariyar adabi ce matankaɗar waƙa

A wannan ɗiya, ya yabe shi da kalmar ‘gwani’, wato ƙwarrarre a kan abu, sannan kuma mai juriya. Har wa yau, ya yabe shi ta hanyar gwarzantawa wajen nuna cewa dukkanin abin da ya shafi adabi, to shi yake tantancewa.

Misali na II

Jagora : Maliyar malala dole sai fa an sha ka,
: Ko cikin birni ko a sha a ƙauyuka,
: Ga ni nai girshe ginshiƙi fa zan waƙa,
: Matsirar masana Hausa sai fa labbaika.

A wannan ɗiya, Makaɗin ya yi ƙoƙarin amfani da salon kambamawa ga Farfesa a yayin yabo, sannan sai ya ƙara bayyana cewa shi Farfesa Ɗangambo tushe ne na masana Hausa. A taƙaice a nan, ya yabe shi da kasancewarsa mai yalwar ilimin Hausa, sannan kuma tushe ga dukkanin wani masani ga Hausa.

Misali na III

Jagora : Na kira ka daƙu a fagen nazar naka,
: Hausa dai wannan sai in ce a kalle ka,
: Za a gan ta tafe a ƙasan ƙafafunka,
: Godiya Bakano ke ta yi da samun ka.

A nan kuwa, ya yabe shi ne ta hanyar kwatantawa, inda a layin farko na ɗa, sai ya ambace shi da ‘daƙu ‘. To a fagen ilimi ma ya ambace shi da ya san komai ko ya taɓa kowane ɓangare na ilimi.

Masali na IV

Jagora : Bishiyar rimi ko na nesa ya ganka,
: Mai firirita sai in ce ki yai kanka,
: Haka nan Jamus na ga ɗalibai naka,
: Da na je Oxford na ga ɗalibai naka.

A wannan ɗiya ma, sai ya sake yabonsa ta hanyar kwatantawa, inda ya kamanta shi da ‘Bishiyar Rimi’. Rimi wata ƙatuwar bishiya doguwa mai kamar kuka, tana da ‘ya’ya da ake samun audugar da ake katifa da matashin kai da ita (CNHN, 2006: 372).

Domin ya bayyana faɗaɗuwar ilimin Farfesa Ɗangambo da yadda ya kewaya ko’ina ta yadda kuma kowa na iya kwankwaɗa daga ciki, sai ya kwatanta shi da wannan bishiya. Abin nufi, duk yadda mutum yake son bincike a ɓangaren Hausa, a ko’ina yake, to fa sai ya ci karo da ilimin Ɗangambo a wannan fage. Domin ya tabbatar da abin da ya faɗa, sai ya bayyana cewa a Jihar Oxford ma ya ga ɗaliban da Farfesa Ɗangambo ya koyar.

Masali na V

Jagora : Malami tammi masani na fannoni,
: A adon harshe zai zame maka tsani,
: A fagen tarke ka biyo shi ladani,
: Ya faɗa ka faɗa ya sanar ka allonka.

Jagora : Yadda Jami’atu ke alam ya shaide ka,
: Ba ka satifiket wanda ke alamta ka,
: Haka nan Ala ke alam na shaidarka,
: In kiraye ka gwargwadon nagartarka.

Jagora : Ɗauraya ta fadon feɗiya a kan waƙa,
: Ka yi rabbe-rabben Adabi na Hausarka,
: Kai Kitsen Rogo ƙirƙira ta kwanyarka,
: Godiya wannan ya ci ai yi ma waƙa.

A waɗannan ɗiya uku da suka gabata, Makaɗin ya yi masa yabo ta hanyar tabbatar da ilimi da nagartarsa, ta yadda har Jami’a ta ba shi shaidar yabo ta satifiket, wanda samuwar wannan satifiket ne ya sanya shi kuma Makaɗin ya yabe shi gwargwadon wannan nagarta tasa. Sannan sai ya bayyana wasu ayyuka cikin muhimman rubuce-rubucensa da ya yi.

3. Salon Yabo ga Farfesa Ahmadu Bello Zaria

Farfesa Ahmadu Bello Zariya shi ma na cikin ‘yan Ƙasa rukuni na uku a Hausa, masani ne kuma manazarci a ɓangaren Harshe. Farfesa Ahmadu Bello ya yi rubuce-rubuce da dama a ɓangaren harshe; waɗanda suka fi karkata ga Nahawu da ƙa’idojin rubutun Hausa da Arulin Hausa da kuma kare-karen harsuna.

Makaɗi (Dr.) Alan Waƙa ya yabe shi musamman kasancewarsa ƙwararre a fagen Arulin Hausa. Ga wasu baituka da ya masa a wata waƙa.

G/Waƙa : Ahmadu Bello Farfesa kai ne mizanin Arulinmu,
A.B.Z Furofesa tartibi na awo a waƙenmu.

Misali na I

Jagora : Ahmadu Bello Farfesa ABZ babban kadarkonmu,
Ahmadu Bello Farfesa gwadabe ɗoɗar na sani namu,
:Farfesa hanyar ilimi ne a waƙenmu,
:Farfesa alfijiri mai haska harkarmu,
ABZ Furofesa mudu na awon sha’irai namu,
:hanyar gane dukka lagonmu,
:hanyaar turke a ƙasidarmu,
:hanyar fiɗar abbiyat namu.

Makaɗi Alan Waƙa ya buɗe wannan waƙa tasa da waɗannan ɗiya, inda a cikin su ya yi amfani da wasu kalmomi domin yabo na sani da maƙura a ilimi ga Farfesa Ahmadu Bello. Kalmar ‘kadarko’ na da ma’anoni biyu, amma a nan mun kalli ma’anar wata ‘yar ƙaramar gada wadda yawanci ake yi da katako a kan hanya don kwararar ruwa (CNHN, 2006: 223). To a nan, an yi amfani da ita ga Farfesa Ahmadu Bello a matsayin babba duk da cewa ƙarama ce, mai makon ruwa da take kwarararwa, to a wurin Farfesa sa kuwa hanya ceta kwararar da ilimi.

Ambatarsa da gwadabe ‘godabe’ kuwa, an siffanta shi da babbar hanya ta sani ga ilimin waƙa. Sannan Makaɗin ya ƙara yabon shita hanyar siffanta shi da alfijir, wanda alfijir wani haske ne da ke fara fitowa domin yaye duhu. To haka shi ma hasken ilimi ne da yake yaye duhun jahilci. A wannan ɗiya dai, duk ya yabe shi da ilimi da sani a tsarin waƙa.

Misali na II

Jagora : Ya Jabbaru Ƙahharu mai ikon duka lammura namu,
: Ban hikima da tarbiyya za ni yaba wa gwaddabe namu,
: Za ni yabon Imaminmu Limamin da ya zamma gatanmu,
: Shehun Shehunai namu Ahmadu Bello qafar sani namu,
: Madalla da jagora mai fitilar haskawa dubanmu.

A wannan ɗiya kuwa, ya ambace shi da imam, wato ja-gaba. Sannan ya ba shi babban suna na malamin malamai, wanda idan aka ce ‘shehi’ babban malami ne, to shi kuma sai ya ambace shi da ‘shehun shehunai’.

Misali na III

Jagora : Amma na sani tunda na yi tawassil gunsa mai iko,
: Zai fisshe ni jin kunya inda na yo lam’a da mamako,
: Baiwa ta Jibulliya ba ta tsumayi ba ta yin dako,
: Allah ba ni ilhama lamunce Ka saka ni nai ƙarko,
: Za ni yabon madubinmu masanin waƙa har irin tamu.

A wannan baiti na huɗu, ya yabe shi da kalmar madubi masani. ‘Madubi’ na da ma’anoni da dama, amma a nan za mu ɗauki ma’anarsa ta ‘ƙarau da aka shafa wa wani abu mai ɗaukar ido da yake nuna surar duk abin daya bayyana a gabansa; mutane kan yi amfani dashi domin duba fuskokinsu’. To shi ma Farfesa a fagen ilimi, an siffanta shi da madubi ta yadda suke duba zuwa ga rumbun iliminsa a game da waƙa.

Misali na IV

Jagora : Na yi shiru na tsahirta na gyaɗa kai wayyo ni wayyo ni,
: Ya zan su fahimce ni na ga kamar malam suka riƙe ni,
: Mai nazari da mai waƙa ba ɗaya suke ba ko a mizani,
: Ba lalle ga mai waƙa yai nazari balle ya hau tsani,
: Ko bishiyar Galadanci sai Ahmadu AB madubinmu.

Bishiyar Galadanci, ita ce bishiyar li’irabi ta jimla a Hausa. Wannan bishiya aba ce mai matuƙar muhimmanci a tsarin jimlar Hausa. Akan ɗauki jimla a yanka, a feɗe ta sannan a rataye ta a bishiyar. Farfesa M.K.M Galadanci ɗaya ne cikin malaman Farfesa Ahmadu Bello Zariya, wanda ya yi littafin kan wannan tsari na bishiya, duk da wahalar hawanta. To Farfesa Ahamdu ya naƙalci hawa wannan bishiya domin rataye jimla.

4. Salon Yabo ga Farfesa Sa’idu Muhammad Gusau

Farfesa Sa’idu Gusau na cikin ‘yan Ƙasa rukuni na huɗu, masani ne manazarci da ya yi rubuce-rubuce a kan abin da ya shafi adabi da al’adu, sai dai ya fi karkata zuwa waƙar baka. Farfesa Gusau ya bayar da gagarumar gudumawa a fagen waƙar baka, ya fito da hanyoyin nazarin waƙar baka, ba ya ga gata da ya mata na bincike da lalubo tushenta.

Aminuddeen Ladan Abubakar (Alan Waƙa) ya yi wa Farfesa Gusau waƙoƙin yabo da dama, amma a wannan takarda an bibiyi waƙa guda ɗaya sannan aka zaƙulo wurin da ya masa yabo, wato waƙar ‘Shehin adabi da al’ada’. Ga wasu ɗiya da ya yi yabo a cikin su:

G/Waƙa : Shehin adabi da al’ada,
: Sa’idu Gusau Furofesa mafakar mazaje

Misali na I

Jagora : Malam na Gusau kadarko ne,
‘Y/amshi : Ɗan maƙi garaji,
Jagora : Tsanin ilimi adibi ne,
‘Y/amshi : Namijin mazaje,
Jagora : Kambin adabi na ilmi ne,
‘Y/amshi : Ɗan maƙi garaje,
Jagora : A yau a fage karimi ne,
‘Y/amshi : Namijin mazaje,
Jagora : Ya zam fitilar adibbai ne,
‘Y/amshi : Ɗan maƙi garaje,
Jagora : Farfesa Gusau gadon bai ne,
: Mabiyar mazaje.

A wannan ɗa, Makaɗi Alan Waƙa ya yi wasu kalmomi ga Farfesa Sa’idu Muhammad Gusau, waɗanda kalmomi ne da suka bayyana yalwar ilimi da yadda shi Farfesa Gusau ya zama mai yi wa ilimi hidima a kowane ɓangare. Cikin kalmomin da ya yi amfani da su wajen wannan yabo akwai kalmar ‘kadarko’.

Kalmar ‘kadarko’ na da ma’anoni biyu, amma a nan mun kalli ma’anar wata ‘yar ƙaramar gada wadda yawanci ake yi da katako a kan hanya don kwararar ruwa (CNHN, 2006: 223). A nan, Alan Waƙa ya yi amfani da kalmar, maimakon ruwa da take kwarararwa, to a wurin Farfesa Gusau hanya ce ta kwararar da ilimi.

Har wa yau, ya sake yabon shi ta hanyar kambama iliminsa da cewa ‘Tsani ilimi’.

Tsani shi ne wani abu da za ka taka domin ya sada ka da wani abu; wanda ba za ka iya kai wa gare shi ba, dole sai ta wannan hanya. A nan, sai ya yabe shi ta hanyar kwatantawa, inda ya nuna Farfesa Gusau tsani ne ga wanda yake son ilimi, wato duk wanda ke son ilimi, to ga wanda zai haxa shi da ilimi, ma’ana zai karantar da shi ilimi.

Kambi na nufin hula ta zinare da sarakunan Turai kan sa. Ko kuma wata lamba ta girmamawa (CNHN, 2006: 229). A nan, sai ya kwatanta Farfesa da kambi, amma a fagen ilimi, domin a fagen ilimin, wani mutum ne da ake girmamawa.

A ci gaba da yabon, sai ya bayyana shi da ‘karimi’, wato mutum mai yawan kyauta.
Alan Waƙa, ya ci gaba da yabo, inda ya ambaci Farfesa Gusau da ‘Fitilar adibbai’. ‘Fitila’ na nufin abar da ake haskaka wuri ko ɗaki da ita (CNHN, 2006: 143). A nan, sai ya bayyana Farfesa Gusau da cewa fitilar adibbai ne, wato shi ne ke haskaka wa duk wani adibi domin ganin hasken ilimin adabi.

Domin ƙara fito da wani nauyi na ilimi da ke kan Farfesa Gusau, sai Makaɗin ya ambace shi da ‘Gadon bai’. A nan, kalmomi guda biyu ne aka mayar da su ta hanyar samar da harɗaɗɗen suna, wato ‘gado’ da ‘baya’. Amma a ginin kalmar, sai aka yi gutsirewa, wanda sanannen abu ne a tsarin nazarin kalma ko ilimin kalma, wato maimakon a ce ‘gadon baya’, sai a ce ‘gadon bai’, ko dai don shi mai waƙa ya sami kalmar ta shiga waƙarsa, ko kuma domin taƙaita kalmar. Gadon bai da ya ambace shi da shi, yana nufin shi sha-nauyi ne a fagen ilimi.

Misali na II

Jagora : Ruhin adabi da al’ada,
‘Y/amshi : Ɗan maƙi garaje,
Jagora : Ƙigon adabi da al’ada,
‘Y/amshi : Namijin mazaje,
Jagora : Jigon adabi na al’ada,
‘Y/amshi : Ɗan maƙi garaje,
Jagora : Domin ka a yau muke tsada.

Domin bayyana ƙarfin ilimin Farfesa Gusau a ɓangaren adabi da al’ada, sai ya yabe shi da ‘ruhin adabi da al’ada’, wato rai ne shi a adabi da al’ada, ta yadda idan babu shi; to babu waɗannan abubuwa biyu. Sai kuma ya yi masa kirari da irin kirarin da ake yi wa sarki ko ango, amma shi ya keɓanta shi da adabi da al’ada, wato ‘ƙigon adabi da al’ada’. Sannan kuma sai ya yabe shi ta hanyar ambaton sa da ‘jigon adabi na al’ada’. Imma dai jigo da ma’anar shugaba, ko kuma jigo da ma’anar itatuwan da ake kafawa su tallabi gugan ban ruwa (CNHN, 2006: 216). To amma shi a nan, shi ake kafawa domin a tallafi ilimi, ma’ana tsayuwarsa ce ke samar da wannan ilimi.

5. Salon Yabo ga Farfesa Salisu Ahmed Yakasai

Farfesa Salisu Ahmed Yakasai sanannen masani ne a ɓangaren harshe, ya yi rubuce-rubuce da dama waɗanda suka fi karkata ga kare-karen harshen Hausa, harsunan da ke maƙwabtaka da Hausa. Haka zalika ya yi rubutu a ɓangaren tatsuniya. Makaɗi (Dr.) Aminuddeen Ladan Abubakar ya yi wa Farfesa waƙoƙi, cikin waƙoƙin mun nazarci waƙa guda, inda muka ciro yabon da ya yi masa. Ga irin yabon nan biye:

G/Waƙa : Jagoran ilimi Salisu ɗan Amadu Furofesa,
: Darajar ilimi Salisu jigo na walwalar harshe.

Misali na I

Jagora : Ga ruhin ilimi Salisu in dai ana batun harshe,
: Ga rayin ilimi Salisu tsari na sautukan harshe,
: Ga gidan ilimi al’umma sauti na samuwar harshe,
: Ginshiƙin ilimi Salisu gado na sarrafar harshe,
: Falsafar ilimi Salisu na ɗaufare a kan harshe,
: Dakata ka jiya Salisu yau zan rawa rawar harshe,
: Ka yi min uziri Salisu rumbunka zan shige harshe,
: Zan yi ma tage Salisu jigo na walwalar harshe.

Kamar yadda ya gabata a bayanan sama, mafi yawa ire-iren waɗannan waƙoƙi Makaɗi Alan Waƙa kan buɗe su da wasu ɗiya, sannan daga baya gindin waƙa da amshi ya zo. A wannan matashiya, ya buɗe da yabon Farfesa Salisu Ahmed Yakasai inda ya bayyana shi da ‘ruhin ilimi’, da ‘rayin ilimi’ wanda dukkaninsu ma’ana ɗaya suke ɗauka. Sannan sai ya ambace shi da ‘gidan ilimi’ da ‘ginshiƙin ilimi’.

A waɗannan yabo da ya yi ta hanyar gwarzantawa, ya yi ƙoƙarin bayyana fagen da Farfesa Yakasai ya fi shahara, wato fagen ilimin harshe. Sannan a layi na ƙarshe, sai ya bayyana shi da ‘jigo na walwalar harshe’. Wannan sai ya ƙara fito da fagen da Farfesa Salisu Yakasai ya fi shahara.

Misali na II

Jagora : Jami’a na nufa aradu wanshekare batun harshe,
: Jami’ar ilimi zan je ga tushe maɓuɓɓugar harshe,
: Jami’ar su Kware autansu jika ga Shehu kau reshe,
: Ga Baba Gwani Salisu Amadu maigidan harshe,
: Walwala nika so Salisu za mu yi a kan batun harshe.

A wannan ɗiya kuwa, ya kira shi da ‘Baba’ da kuma ‘gwani’. Wato uba ne a ɓangarensa na harshe, sannan gwani ne ta yadda ya san wannan fage sosai da sosai.

Misali na III

Jagora : Sanadin su uba Salisu ɗan Amadu Furofesa,
: Daraja tasa ce ta hana Ala ya rinƙa Ingausa,
: Sababin ilimi wanda nake bibiya a rumbunsa,
: Daraja tasa ce ta hana Ala ya rinqƙa Arausa,
: Vurbushin ilimi ya ba ni dama ta walwalar harshe.

Domin ya ƙara nuna gogewar Farfesa Salisu Yakasai a wannan fage na harshe, sai ya bayyana wa duniya ta hanyar yabo cewa, shi kansa idan ba domin Farfesa Salisu ba, da ba zai rinƙa tafiyar da waƙarsa da tatacciyar Hausa ba, sai dai ya rinƙa haɗawa da Ingausa, wato ya rinƙa ɗaukar wasu kalmomi na Turanci yana kiran su da Hausa, ko kuma Larausa, shi ne Hausantar da kalmomin Larabci. To amma albarkar karatun da ya samu a rumbun Farfesa Salisu, sai ya san abubuwa da dama, kuma ya iya tantance kalmomi.

Misali na IV

Jagora : Zan yabon ka gwani ko da a kan bishiya a kan reshe,
: Zan yabanta gwani ba zan amai ba balle fa in lashe,
: Ko in na sarari ko ko ina a hukunce ga harshe,
: Za a ji ni da kai Salisu ƙaunarka na cikin tushe,
: A jinni take ma Salisu tun fil’azal cikin tushe.

Duk domin dai gwarzanta Farfesa Yakasai, sai ya ci gaba da yabonsa da kuma bayyana cewa ko a ina zai iya yabon sa, sannan ƙaunarsa daman can akwai ta tun a tsatso.

Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Masana A Bakin Makaɗa: Nazarin Yabon Masanan Hausa A Cikin Wasu Waƙoƙin Aminu Alan Waƙa wanda Ibrahim Baba (Nayaya) ya wallafa shi.

Domin karanta cikakken bayani akan Taƙaitaccen Tarihin Samuwar Waƙoƙin Baka a Ƙasar Hausa danna nan

Edita:@rumasau-kallamu

labarin da ya wuceShawara Ga Masu Ciwon Suga
Labarin na GabaRoƙo a Wasu Waƙoƙin Kamilu Almajirin Mawaƙa